A ranar Talatar da ta gabata ne, gwamnatin jihar Buachi ta bayar da rahoton salwantar rayukan mutane uku, bayan da bincike ya tabbatar da mutane 25 masu dauke da cutar Lassa a kananan hukumomi bakwai na jihar.
Shugaban asibitocin duba gari na jihar, Alhaji Ibrahim Gamawa, shine ya bayar da wannan sanarwa a yayin bude taron fadakarwa tare da wayar da kawunan malaman asibiti a kan wannan cuta ta Lassa.
A cewar sa, jihar ta samu mutane 25 masu dauke da kwayoyin cutar tare da salwantar rayuka 3 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Maris.
Shugaban makiwatan lafiya na jihar ya bayar da jerin sunayen kananan hukumomin da annobar ta afkawa kamar haka; Alkaleri, Bauchi, Bogoro, Dass, Tafawa Balewa, Toro da kuma Warji.Gamawa ya kuma fadakar da ma'aikatan na Lafiya akan wannan cuta da ka'idoji tunkarar ta kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Jaridar NAIJ ta kuma ruwaito cewa, a yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin zagayowar ranar 'yancin kai na kasar Ghana tare da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Source :naij hausa
Title :
Zazzabin Lassa Yayi Barna A Jihar Bauchi
Description : A ranar Talatar da ta gabata ne, gwamnatin jihar Buachi ta bayar da rahoton salwantar rayukan mutane uku, bayan da bincike ya tabbatar da mu...
Rating :
5