Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana kudurinsa na halartar taron bude ofishin jakadancin Amurka a kasar Isra’ila wanda za'a tashe shi daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus.
Bayan ganawa da sukayi a kasar Amurka da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya gana da shugaba Donald Trump bayan haka shugaban ya yi magana da ‘yan jarida, ya bayyana cewa Kudus ce helkwatar Isra’ila ya kuma ce ofishin jakadancin Amurka zai tashi daga Tal Aviv ya koma kudus
.Trump ya bayyana cewa in dai kudirin su ya tabbata na mai da ofishin zuwa kudus to zai kokarin halartar bikin bude shi.
Ya yi shirin zaman lafiya a gabas ta tsakiya, in da bayyana janye maganar matsalar kudus a teburin sulhu. Wanda hakan ya rage matsalolin da kasar ke fuskanta na samun zaman lafiya.
Source :naij hausa
Title :
Trump Na Neman Sake Jefa Duniya Cikin Rikici
Description : Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana kudurinsa na halartar taron bude ofishin jakadancin Amurka a kasar Isra’ila wanda za'a ta...
Rating :
5