Kasar Pakistan ta haramta yin amfani da Ajinomoto ko gishirin china, wanda a turance ake ce ma Monosodium Glutamate saboda yana da illa ga kwakwalwar mutun.
Kasar ta yi hanin ne a jahohi 4 da garuruwa 3 masu zaman kansu, hakan ya fito ne daga babbar kotun kasar ta Pakistan.
Al’umma na amfani da gishirin don kara wa abinci dandano, ba ma kamar kashen gabashin Asiya. Kwarrarun likitoci sun bayyana cewar ya na da illa matuka ga jijiyoyin kwakwalwar mutum.
An sanya dokar ta hana amfani Ajinomoto cikin abincin jarirai da basu wuce wata 3 ba a kasar turai, da kuma rage yawan sanya shi a abinci a wasu kasashe 50 wanda suka hada da Amurka.
Source :naij hausa
Title :
Ajinomoto Babbar Annoba Ce Ga Lafiyar Dan Adam
Description : Kasar Pakistan ta haramta yin amfani da Ajinomoto ko gishirin china, wanda a turance ake ce ma Monosodium Glutamate saboda yana da illa ga k...
Rating :
5