Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria, ta alwashin za ta sanya kafar wando daya da masu haddasa tashin hankali a wasu yankunan jihar musamman Kudanci.
Gwamnati ta yi wannan kalami ne makwanni biyu bayan hatsaniyar da ta tashi a Garin Magani a karamar hukumar Kajuru, inda aka kona gidajen mutane da hallaka wasu da dama.
Ba wannan ne karon farko da ake samun rikici mai nasaba da addini da kabilanci a jihar Kaduna ba, kuma gwamnati ta sha shan alwashin magance matsalar.
Amma har yanzu ba ta sauya zane ba. Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya zargi wasu 'yan siyasar yankin da rura wutar rikicin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Source :bbc hausa
Title :
Zan Hukunta Duk Wanda Ya Haddasa Rikici A Kaduna-El Rufa'i
Description : Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria, ta alwashin za ta sanya kafar wando daya da masu haddasa tashin hankali a wasu yankunan jihar...
Rating :
5