Rundunar Sojojin Najeriya sun damke wani gagararren mai laifi wanda ya addabi Jama’a a Jihar Kogi bayan wani hari da Sojojin su ka kai a Garuruwan Irovovochinomi da Egee da ke cikin Jihar. Har yanzu haka dai ana kan aikin.
An damke wannan gawurtaccen mai garkuwa da mutane ne a cikin Karamar Hukumar Okene. Rundunar Sojin kasar sun yi ram da Mohammed Bashir wanda yana cikin wadanda su ka kashe wani kurtun Soja kwanakin baya.An samu wannan mai gaurkuwa da mutane dauke da makamai na bindigar AK 47 da harsashi rututu.
Wata runduna ta musamman ce dai aka tura domin kamo wannan fitinannen mai laifi a jiya Ranar Lahadi kamar yadda mu ka ji.
Darektan yada labarai na gidan Sojan kasar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana wannan a shafukan sadarwa na Sojojin kasar. Sojojin na neman duk wani karin bayani da zai taimaka wajen ganin kawo karshen miyagu a kasar.
Source :naij hausa
Title :
Sojoji Sun Kama Wani Babban Mai Laifin Da Ya Addabi Jama'a A Kasarnan
Description : Rundunar Sojojin Najeriya sun damke wani gagararren mai laifi wanda ya addabi Jama’a a Jihar Kogi bayan wani hari da Sojojin su ka kai a Gar...
Rating :
5