Akalla ‘yansanda 53 dake aiki a fadar shugaban kasa na Aso Rock dake Abuja, suka gudanar da zanga-zanga akan rashin biyan alawuns din su, tun daga shekara 2015 da aka tura su aiki a Aso Rock.
Sun yi zanga-zangar ne a takarda korafi d suka aika wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
‘Yansandan sun ce tunda suka fara aiki a fadar shugaban kasa, suke fama da talauci dan ba a biyan su alawun su din su.
‘Yansandan sun ce shugaban rudunar Squadron da shugaban tawagar dake kula da motocin shugaban kasa, suke hana su samun kudaden su.
“Muna kira ga maigidan mu shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya taimaka ya sa baki a biya mu alawuns din mu saboda mufita daga wahalar da muke ciki,” inji su
Source :naij hausa
Title :
Yan Sandan Aso Rock Sunyi Zanga Zanga
Description : Akalla ‘yansanda 53 dake aiki a fadar shugaban kasa na Aso Rock dake Abuja, suka gudanar da zanga-zanga akan rashin biyan alawuns din su, tu...
Rating :
5