Shin shugaba Buhari zai kara neman gudumuwar kudi kamfen daga wajen 'yan Najeriya idan zai kara tsawa takara kuwa?
A lokacin yakin neman zaben 2015, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nemi al’ummar Najeriya su taimaka masa da gudummawar kudaden kamfen.
Ta haka aka fara sayar da katin kamfen din sa irin wanda aka saka wa wayar tarho ta hannu. Jama’a da dama musamman talakawa da matasa suka ta sayan wannan katin dan taimakawa Buhari.
A jikin kowane kati akwai hotunan Buhari kuma an rubuta, ‘Mu hada hannu mu ceto Najeriya’Wannan kati ya karade fadin kasar nan, lungu-lungu, sako-sako, tsoho da yaro, kowa ya tallafa wa wannan tafiya.
Shin kai da ka sayi ko an hada hannun da kai? An ceto Najeriya din kuwa? Ko za ka sake sayen kati idan an sake sayarwa don zaben 2019?
Source :naij hausa
Title :
Shin Buhari Zai Kara Neman Tallafi Inzai Nemi Takara?
Description : Shin shugaba Buhari zai kara neman gudumuwar kudi kamfen daga wajen 'yan Najeriya idan zai kara tsawa takara kuwa? A lokacin yakin nema...
Rating :
5