Ahmed Makarfi, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na rikon kwarya kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yi wata Doguwar hira da jaridar Daily Trust inda ya tattauna a kan batutuwan da su ka shafi jam'iyyar da kuma siyasar Najeriya.
Da yake amsa tambaya a kan yadda tun bayan kammala zaben sabbin shugabannin jam'iyyar 'ya'yanta ke cigaba da ficewa bisa zargin cewar jam'iyyar ta koma aljihun gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.A martanin sa, Makarfi ya bayyana cewar jam'iyyar na kokarin ganin sulhunta mambobinta domin zama tsintsiya madauri daya.
Makarfi ya ce ba ya jin dadin ficewar 'ya'yan jam'iyyar, saidai ya ce ba abin damuwa ba ne domin siyasa ta gaji haka kuma shugabancin jam'iyyar da gwamnonin jam'iyyar na yin iyakar kokarinsu domin dinke duk wata baraka da jam'iyyar ke fama da ita.
Da yake amsa tambaya a kan ficewar wasu iyayen jam'iyyar, Farfesa Jerry Gana da Farfesa Tunde Adeniran, zuwa jam'iyyar SDP, Makarfi ya ce, duk ba zai iya magana da yawun jam'iyyar PDP ba, amma ya san jam'iyyar ta amince da yin aiki da jam'iyyar SDP da wasu jam'iyyun Najeriya domin hada karfi wajen karbar mulki daga hannun jam'iyyar APC.
A dangane da rade-radin rabuwar kayuwa tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar Kaduna tsakanin bangarensa da na tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, Makarfi, ya ce babu rabuwar kayuwa kuma yana fatan 'yar tsamar dake tsakanin magoya bayansu za a dinke ta.
Makarfi ya ce zai bayyana matsayin takarar sa ta shugabancin kasa da zarar ya kammala tuntubar magoya bayansa.
Source :naij hausa
Title :
PDP Zata Ci Gaba Da Rasa Magoya Baya-Makarfi
Description : Ahmed Makarfi, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na rikon kwarya kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yi wata Doguwar hira da jaridar Daily T...
Rating :
5