1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kazamar Gida Part 17

Kazamar Gida Part 17

By Abdul Mk
Add Comment
Monday, 1 February 2016
Ya gama sace zuciyarta,a yau saita kara ganin ya kara kyau agareta. Da wannan farin cikin ta fada shagonsu.
******
Karfe takwas na dare sai gashi yayi kiranta. Lokacin tana cin abinci,har ya gama ringing bata dauka ba. Ana biyu ne ta amsa kiran
"Assalamu alaikum."
Ya amsa da sauri ya k'ara da cewa
"Ina kika shiga inata kira deeya? Ko aljanar ta hau kanki?"
Tayi dariyar maganarsa
"Hum,har yanzu kana yimin kallon aljana kenan?"
Shima dariyar ya danyi
"Ai kece kika kira kanki da aljana kinga kuwa bani da laifi ko? Ina fatan Deeya ta yafewa Yaya j dinta?"
"Sai batun yafiya kakeyi,alhalin ko kusa ni bansan lokacin da kayimin laifi ba yaya j. Laifina ne ba naka ba,ni yafi cancanta na baka hakuri ba kaine yafi dacewa ka bani ba."
Yayi murmushi ya kara gyara zamanshi a cikin motar Haris, wanda ke tuk'i yana sauraronsa.
"Kada ki damu Deeya,donta ni na yafemaki ban rikeki a zuciyata ba kinji?"
Wani sanyin dadi ya mamaye zuciyarta
"Naji yaya j,nagode."
"Yauwa ko kefa deeyata,yaushe zanzo muyi magana?"
Ladi ta ture kwanon tuwonta
"Duk sadda kazo ina maraba dakai."
Yayi murmushi lokacin daya dubi Haris wanda ya tsaya a kofar gidan iyayensa.
"Shikenan deeya,gobe in sha Allah zan shigo."
"Toh yaya j."
Daga haka sukayi sallama.
Haris ya dubeshi yana murmushi
"Menene matsalarka kai kuma?"
Jafar yayi furucin yana harararsa da murmushi dauke akan fuskarsa.
Hakan ya bawa Haris damar tuntsirewa da dariya
"Menene kuwa banda abun boye daya fito fili. Daman na jima ina zargin soyayya kukeyi da wannan kanwartaka. Dole Ibrahim yaji wannan maganar ma don ya tayani dariya. Wato yanzu har gidansu ma ka sani?"
Jafar ya tabe baki hadi da murmusawa
"Kana da aiki fa malam,toh idan ma soyayya mukeyi menene a ciki? Kai karewa ma aurenta nakeson nayi idan Allah Ya yarda."
Haris ya bude baki cikin mamaki
"Wai daman rannan dagaske kakeyi da kace mini kanason kara aure? Wacece wannan data ture gwamnatin Siyama?"
Jafar ya girgiza kansa
"Babu wanda ya isa ya ture gwamnatinta a zuciyana kaji ko? Yauwa,kabar zancen nan ma please. Itama nata bangaren ta samu wanda banyi zaton akwai shi ba a zuciyata."
Haris yayi murmushi
"Ince dai ka taba ganinta kada kaje kaga ba daidai ba."
"Na taba ganinta mana."
Jin Haris zai kara wata tambayar ne ya sanyashi saurin fitowa
"Malam mu shiga mu gaida Hajiya dare yana yi mana."
Haris ya fito yana dariya kafin su shiga.
Hajiya Ummuhani taji dadin zuwansu sosai,ta dubi Jafar
"Daman ana ganinka Jafaru? Ya wajen su Hajja?"
Jafar yana dariya ya amsa mata,yayi mata sannu da dawowa gami da tambayar lafiyar kafarta.
Sun jima har abinci sukaci,kafin tayi musu nasihohi a karshe suka nufi bangaren Alhaji Muniru nan dinma gaisuwa ce da tambayar iyali. Shima ya dora da nashi nasihohin akan tsoron Allah a karshe sukayi musu sallama....
A yanzu Jafar bai fiye takura kansa da damuwar kazantarta ba. Saidai yaja tsaki ya gyara,wataran kuwa Dauda ke taimakonsa.
Ana cikin haka har babbar sallah tazo,ya zauna a dakinsa yayi jugum yana tunani. Fargabarsa bai wuce ya siyo rago ba ya kawo,amma idan Siyama ta soya ya zamana yak'i ciyuwa. Can kuma sai dabara ta fado mishi ya zaro wayarsa ya dannawa Hajja kira. Kara daya biyu ta dauka.
Bayan sallama da gaishe gaishe ne,ya sanar da ita yanason ta turo masa Bahijja saboda aikin nama tunda yasan masu taimakawa Hajjah da sallah suna da yawa. Hajjah tace
"Ba nak'i ayi hakan ba,ni abune na kananun magana banaso. Kayi wa ita Siyamar magana idan ta amince sai a kawota."
Jafar cike da mamaki yace
"Hajiya,Siyama ce zata k'i zuwan Bahijja kuma?"
Hajjah ta danyi shiru,Jafar baisan cewa Siyama ta jima rabonta da cikin gidan nan. Kusan sau hudu tana zuwa gidansu saidai ta bada yaro a kawo mata. Ita kanta batasan abunda ya jawo wannan chanjin ba.
"Hello Hajjah kina jina?"
"Kaidai kayi yanda na gayamaka."
Daga haka ta kashe wayar,ya tsaya sororo yana bin wayar da kallo har Siyama ta shigo goye da Faruk dake bacci.
"Kai kuma lafiya kuwa?"
Ya danyi murmushi
"Hum,barni da Hajja mana,wai nace a turo Bahijja ta taimaka miki da aikace aikacen sallah tace na nemi izninki shine abun yake bani mamaki. Yaushe kuka fara 'yar haka da Bahijjar taki?"
"Kada ki kuskura ki kara barin yar iskar nan ta kara zuwar maki gida. Wani munafuncin ne nasu na daban."
Hudubar da hajiyar ta taba yi mata kenan,nan da nan ta daure fuska
"Menene kuma na neman iznina? Kawai dai Hajja batason turomin ita ne,nikam barshi ma mantawa nayi ban fadamaka ba Hajiya zata aikomin mutum biyu zasu taimakamin. Ba saita zo ba."
Jafar ya mike tsaye,yana zargin wannan chanji na Siyama domin a kwanakin nan rashin kunyarta kara yawaita yakeyi. Baice komai ba har ta fice daga dakin. Ya girgiza kanshi ya mike da niyyar ficewa kasuwa don daman ya kammala shirinsa tsaf.
******
Tun ana gobe sallah,hadiyya suka tafi hutun zuwa kasuwa. Abun yazo mata da dadi saboda anyi musu hutu.
Kwatsam da yamma suna zaune ita da Mama suna lissafin kayan cefane sukaji sallamar Basma. Wani ihun murna Hadiyya ta saki ta rukunkumeta suna dariyar farin cikin ganin juna.
Mama sai murmushi takeyi,ita kanta taji dadin ganin Basma domin tunda ta tafi Zaria, makaranta bata kara zuwa garin ba sai yanzu.
Basma ta saki Hadiyya tayi wajen mama,itama rungumeta tayi tana mai gaisheta. Mama ta rike hannunta tana murmushi mai bayyana hakora
"Yan makaranta,saukar yaushe?"
Basma tana dariya tace
"Dazu dazun nan na iso Mama. Mun sameku lafiya? Ya shirye shiryen sallah?"
"Lafiya kalau mungode Allah. Sallah kam,gatanan ta iskomu sai fatan Allah Yasa muyita lafiya."
Basma tana murmushi ta amsa da amin. Hadiyya ta dubeta
"Taso muje."
Mama ta dakatar da ita ta hanyar harara
"Ni zan fita cefanen? Rike kudin kuje "
Suna dariya suka fice daga gidan bayan Hadiyya ta zura hijabinta a jiki.
A hanya hira kamar suyi me? Hadiyya ta labarta mata yanda take soyewa da Jafar a yanzun,Basma dadi ya rufeta
"Kinga amfanin addu'a Hadiyya. Ga wanda zai gane,ya saki komai ya kama addu a don takobin mumini ce. Nima gashinan da karfin addua mahaifin Bash ya sauko amince da batun aurena dashi. Allah dai Yayi mana jagora."
Hadiyya ta amsa da amin. Sukayita hira har suka isa inda zasuje.
*****
Bayan Sallah da Kwanaki....
Sallamar Shukra da Fatima ta maido da hankalin Siyama daga kallon da takeyi. Ihu ta saki ta rukunkumesu cikin jin dadin ganinsu. Fatima ta tureta saboda nauyin cikin dake jikinta
"Ke taimaka ki matsa so kikeyi nayi haihuwar da ban shirya ba?"
Siyama ta harareta
"Yo idan kin haihu a gidana ai daidai kenan,ko kin mance rabonki da gidana tun bikina?"
Suka zauna Fatima tana yamutsa fuska yayin da take karewa falon kallo
"Siyama fruits kikasha amma baki gyara falon ba?"
Shukra taja tsaki
"Kedai wallahi dama Nazifa aka sanya maki. Haba,ko yaya kikaga datti sai kinyi magana? Siyama bani ruwa idan da abinci ki hado don ko abincin rana banci ba wannan matar ta azazzaleni da waya."
(Shukra da Fatima aminan juna ne kuma kawaye ga Siyama. Tare sukayi karatun firamare zuwa sakandire sun shaku da juna sosai duk da dai akwai bambancin halayya,Fatima duk ta fisu hakuri da sanin ya kamata)
Siyama tace
"Shareta aminiyata,ai Fatima sai a hankali. Wannan da kece uwata bansan ya zanyi ba. Kina fama da jikinki amma baki bar neman rigima ba."
"Atoh dai."
Fatima dai baki ta tab'e
"Ai daman halinku daya baku da bambanci,sai ku koyi hankali yanzu tunda sai an soma tara zuri'a."
Shukra tayi dariya,Siyama dake kicin tana tayata.
"Toh ai tunda muna kyautatawa a shimfida ai inajin magana ta kare ko?"
"Bata kare ba,tsafta da kwalliya da girki suma wani abu ne. Uwa uba ladabi da biyayya."
Siyama wacce ta ajiye faranti cike da nama dayan kuma lemo ne da ruwa tace
"Toh wannan ai mai sauki ne tunda ana kokartawa ko ya kikace aminiyata?😎"
Shukra wacce ta bararraje akan kafet ta gama kwankwadar ruwa tana shirin sanya nama a bakinta ta gyada kai
"Wallahi fa. Bar wannan Nazifar,ita na lura batasan wahalar dake cikin aikace aikace ba tunda su biyu ne wajen mijinta."
Daga haka ta jefa nama a bakinta tana tauna, Fatima tana kokarin shan ruwa,Shukra ta dakatar da ita sakamakon naman data furzo waje .
"Lafiyarki kuwa?"
Shukra tayi saurin bude lemo tasha,sannan ta dubi Siyama
"Allah Ya isa amma,kin kasheni da raina. Wannan wane irin nama ne mai wari haka? Dame kikayi suyarshi? Mts,wallahi Malama yunwa nakeji nikam idan da biredi bani na afa ko zan samu naji daidai."
Siyama ta harareta
"Yau kuma salon wulakancin naki kenan? Wane irin wari a abunda aka soyashi kwanan nan?"
Shukra ta turawa Fatima farantin
"Don Allah ci kiji saiki tabbatar ko sharri nayi gareta. Kema ki dauki kici."
Fatima tunda ta doshi bakinta dashi batayi marmarin kaiwa bakinta ba ta maidashi. Siyama ta tauna ta hau yamutsa fuska
"Oh ni Siyama,a wane roba aka sanyamin naman nan? Ni kaina sai yanzu naji warin. Kodai shiyasa Jafar bayaci?"
Cike da mamaki suka dubeta,Fatima tace
"Amma kin bani kunya,yau kuma mijin naki ne kike kira haka? Ina laifin kiransa da baban faruk? Ta yaya naman nan ma zai ciyu Siyama? Gaskiya baban faruk yana fama."
Haka sukayi mata ca,duk rabin fadan Fatima ke yi,Shukra kuwa biredi da lemo take dank'ara abinta. Idan Fatima ta hado da nata kalar kazantar sai ta hayayyaji tace batasan da wannan ba.
Haka dai a karshe sukayi sallama suka tafi,Siyama bakin cikin lalacewar naman yafi komai nukurkusarta. Ta ja tsaki yafi sau nawa hakanan ta tattara ta ajiye.
******
Watanni biyu da kulluwar soyayyar Jafar da Hadiyya,ya shirya sanarwa iyayensa batun aurensu..
Koya abin xe kasance..?
Nasa mutane xasuce se posting nakeyi..eh sonake inna gudu indena tunoku..!
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 15:30
In Hausa Novels
Title : Kazamar Gida Part 17
Description : Ya gama sace zuciyarta,a yau saita kara ganin ya kara kyau agareta. Da wannan farin cikin ta fada shagonsu. ****** Karfe takwas na dare ...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kazamar Gida Part 17"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ▼  February (149)
      • Yar Amana Part 6
      • Na Goyi Bayan A Samar Da Kasar Falasdinu .
      • Sojoji Sun Bude Manyan Hanyoyin Jihar Borno Bayan ...
      • Idan Ka Shirya Mu Hadu A Kotu, Sakon Fani Kayode G...
      • New Film : Nasibi Part 1&2
      • Yar Amana Part 5
      • Ban Yi Alqawarin Bada Naira 5,000 Ga Marasa Aikin ...
      • Buhari Ya Naso Yadawo Da Najeriya Kasar Musulunci ...
      • New Video : Manchester United 3 Arsenal 2
      • Manchester United Ta Doke Arsenal Da Ci 3-2
      • Graphic Photos: Hukumar Kastam Sun Kashe Wani Mutum
      • Jami'ar Jihar Kaduna Ta Samu Tallafin Motar Kashe ...
      • Photos: Sabin Hotuna Yan Kannywood A Amurka
      • Yar Amana Part 4
      • Kanwata Part 1
      • Gwamnatin Nasarawa Ta Kori Wata Dan Bayyana Ra'ay...
      • Sabon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya, Gia...
      • Graphic Photos: Sojojin Nijeriya Sun Sake Samun Na...
      • Yar'adua Da Jonathan Basu Gina Titi Ko Daya Ba A N...
      • Yar Amana Part 3
      • Munafukai Da Barayin Gwamnati Ne Ke Sukar Gwamnati...
      • Hukumar EFCC Na Shirin Gayyato Tsohon shugaban PDP...
      • MATSAYIN MAHAIFIYA A MUSULUNCI
      • Photos: Yau Aka Daura Auren Ishaq Sidi Ishaq
      • Samson Siasia Ne Sabon Kocin Najeriya
      • Ziyarar Buhari Dakin Ka'aba A Jiya Da Yau
      • Sunday Oliseh Ya Yi Murabus
      • Saraki, Dogara Da Sauransu Na Shirin Kafa Sabuwar ...
      • Messi Ya Baiwa Yaro Rigarsa
      • Jami'an 'Yan Sanda Sun Rasa Ransu A Yayin Tashin B...
      • Dan Sanda Ya Bindige Wani Dalibi Har Lahira A Gombe
      • Yan Shi'a Sun Kauracewa Zaman Kwamitin El-Rufa'i A...
      • Photos: An Jefar Da Wani Jariri A Shadda
      • Photos: Buhari Tare Da Sarkin Kano A Saudiyya
      • Daraja Naira Ta Fara Farfadowa
      • Buhari Ya Ki Yarda Da Bukatar Sarkin Saudiyya
      • Photos: Buhari A Massallaci Madina
      • New Video: Arsenal 0 Barcelona 2
      • Hajiya Aisha Dan Kano Ta Rasu
      • Photos: Buhari Ya Ziyarci Sarkin Saudiyya
      • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya -...
      • Buhari Ya Nada Makaho A Matsayin Babban Mai Taimak...
      • Yan Shi'a Sun Ki Halartar Zaman Kwamitin Binciken ...
      • EFCC Ta Cafke Tsohon Minista Abba Moro
      • Har Yanzu Akwai Tuhuma Rashawa Akan Shugaban PDP -...
      • An Yi Wa Wata Mata Da 'Ya'yanta Hudu Yankan Rago A...
      • Photos: Hotuna Daga Wajen Liyafan Aure Aminu Tambuwal
      • An Baiwa Mahajjata Damar Shiga Da Goro Kasar Saudiyya
      • Mata Na Rububin Sayar Da Gwalagwalansu Saboda Tash...
      • Yar Amana Part 2
      • Photos: ISIS Sunyi Wa Mutane Biyu Yanka Rago
      • Yau Buhari Zai Kai Ziyara Kasar Saudiyya
      • Dalilan Da Suka Sa Na Musulunta - Emmanuel Adebayo
      • Almajiranci Ba Musulunci Ba Ne, Talauci Ne Ke Hadd...
      • An Kama Mai Magana A Madadin Shekau
      • Kwamitin Bincike Kan Rikicin 'Yan Shi'a Da Soji, Z...
      • Rakumi Yayi Sujadah Agaban Sa
      • Sakamakoni Wasanni Premier League Na Najeriya Na W...
      • Yar Amana Part 1
      • 'Yan Shi'a Sun Sha Alwashin Tarwatsa Gwamnatin Tar...
      • Sojojin Nijeriya Sun Sake Yin Nasara Akan 'Yan Boj...
      • Yadda Direbobin Ma'aikatun Kananan Hukumomin Jihar...
      • Ba Baiwa Bace Part 3
      • Dalilin Da Ya Sa Na Bar PDP - Dalhatu Sarki Tafida
      • Yanda Zaka Saya Datar Airtel 3GB Akan N1000
      • Amfanin Lemum Tsami
      • Anyi Wa Yaro Dan Shekara Hudu Hukucin Rai Da Rai A...
      • Ana Zargin Mutane Biyu Da Kwakwalewa Wani Yaro Ida...
      • Photos: Nafisah Abdullahi Ta Sake Sabin Hotuna
      • Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Suke Shirin Yin Auren J...
      • Photos: Gobara A Kasuwar Katako Dake Zamfara
      • Photos: Yaro Dan Shekara Biyu Wanda Iyayen Sa Suke...
      • Yau Buhari Zai Je Taro Kasar Masar
      • Buhari Na Bukatar Addu'ar Mu
      • Al'ummar Garin Keffi Na Fama Da Rashin Ruwan Sha
      • Photos: Matar Dan Sani Abacha Ta Haihu
      • Photos: Gobara A Kasuwar Singa Dake Jihar Kano
      • EFCC Ta Cafke Mijin Tsohuwar Ministar Man Fetur, A...
      • Rarara Ya Sha Ruwan Duwatsu A Jamhuriyyar Nijar?
      • Wata Uwa Na Shirin Auren Danta A Kasar Zimbabuwe
      • Photos: Wata Mata Ta Haifi 'Ya'ya Biyar A Jihar Oyo
      • An Yi Garkuwa Da Kawun Jonathan
      • Buhari Zai Jagoranci Bude Sabuwar Kasuwar Kasa Da ...
      • Buhari Ya Rike Mukaminsa, Ba Na So, Inji Naja'atu ...
      • Buhari Ya Nada Abike Dabiri A Matsayin Mai Taimaka...
      • Buhari Ya Sallami Shugabannin Kafafun Yada Labarai...
      • Boko Haram Sun Kashe Mutane Talatin A Jihar Borno
      • Daga Bakin Rarara Kan Sabuwar Wakar Da Aka Ce Ya Y...
      • Buhari Ya Nuna Jimaminsa Kan Rasuwar Hajiya Fati Koko
      • Wani Tsohon Shugaban Hafsan Soja Ya Maido Da Naira...
      • An Gano Tabbataccen Wurin Da Aka Boye Daliban Chibok
      • Photos: 'Yan Fim Din Hausa A Amurka
      • EFCC Ta Gano Dala Milyan Uku A Ramin Masan Gidan T...
      • Photos: Dubun Wani Barawo Ta Cika A Jos
      • EFCC Ta Cafke Wani Hafsan Soja A Hanyarsa Ta Ketar...
      • An Soma Kama 'Yan Arewa Mazauna Jihar Lagos
      • Ko Wannan Sako Yan Isa Gareka
      • EFCC Ta Soma Binciken Shema
      • Naira 20 Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Wani Mutum A Jiha...
      • Photos: Peter Psquare Ya Ziyarci Yan Wasan Kwallon...
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Fantyz Guy ft Mr SPYZY - ALKALERI GARINA (Official Hausa HipHop Music Video...
        Bauchi Base Popular HipHop musician FANTYZ GUY release hit track ALKALERI GARIN Featuring Mr SPYZY 
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger