Mun samu labari cewa wani Jigo a Kudancin Najeriya na Jam'iyyar APC Nyerere Anyim ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019.
Nyenyere Anyim wanda shi ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Abia a zaben 2015 yayi kira ga Shugaban kasa Buhari ya zarce kurum domin karasa ladan sa lokacin da yayi hira da gidan Jaridar Daily Post a gidan sa.
Babban 'Dan APC ya roki Shugaban kasar ya ji kukan mafi yawan 'Yan Najeriya da ke neman sa ya kara fitowa zabe. Nyerere yace duk Najeriya babu 'Dan siyasar da zai iya doke Shugaban kasa Buhari a zabe a Najeriya.
Wannan Babban 'Dan siyasar kasar nan wanda yana cikin manya a Gwamnatin Buhari ya ce Shugaban kasar na bakin kokari kuma Jam'iyyar APC tayi daidai na kara wa'adin Shugaban ta John Oyegun yace yanzu 2019 ake hari.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Ya Sami Karfin Gwiwar Yin Tazarce A 2019
Description : Mun samu labari cewa wani Jigo a Kudancin Najeriya na Jam'iyyar APC Nyerere Anyim ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takar...
Rating :
5