Daya daga cikin fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa sannan kuma jigo a harkar ta shirin fim na Kannywood Ali Nuhu ya bayyana irin yadda a ko yaushe yake alfari da irin kyautar 'ya'ya da Allah yayi masa.
Jarumin wanda kuma fitaccen darakta ne sannan kuma mashiryin shirin fim ya wallafa wasu sabbin hotunan sa ne tare da yaran nasa Ahmad Ali Nuhu da kuma Fatima Ali Nuhu a shafin sa na dandalin sada zumunta.
Yaya Ali kamar dai yadda ake kiran sa a masana'antar ya kuma yi wani dan gajeren rubutu a kasan hotunan na sa inda ya rubuta sakon farin ciki bisa ni'imar da Allah yayi masa na samun ya'yan.
Labari yazo ya samemu cewa jarumin ya rubuta: "Daya daga cikin kyata mafi soyuwa a gare ni da Allah ya bani shine samun diya ta". Idan mutum ya zama uba to ya zamanto abun koyi ga dan shi".
Wannan dai kamar yadda muka samu yana zuwa ne a dai dai lokacin da alummar duniya a ko ina suke gudanar da bukukuwa don tunawa da ranar mata ta duniya.
Source :naij hausa
Title :
Ali Nuhu Yayi Tsokaci Game Da 'Ya'Yansa
Description : Daya daga cikin fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa sannan kuma jigo a harkar ta shirin fim na Kannywood Ali Nuhu ya...
Rating :
5