1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Labari » Yadda Giwan Ruwa Kecin Kwari Miliyan 40 A Rana

Yadda Giwan Ruwa Kecin Kwari Miliyan 40 A Rana

By Unknown
Add Comment
Friday, 13 October 2017

Tsananin son cin abinci da matsananciyar yunwa da galabaita. Daukacinmu akwai ranakun da mukan yi fama da yunwa, amma ko yunwarka ta kai ga bukatar cin ton hudu na halittar ruwa?

Batu na gaskiya, shudin hamshakin kifi (the blue whale) giwar ruwa ita ce babbar dabbar da ta fi kowace girma a duniya, inda ta sha gaban komai a zakuwar son cin abinci.

A kullum wannan kasurgumar dabba tana lakume kananan kwari miliyan 40, wadanda ake yi wa lakabi da kananan kifaye

Sai dai akwai sauran dabbobi da ke cin abinci ba na wasa ba, ta yadda wasunsu za su ba ka mamaki.

Tamkar hamshakin shudin kifi, wannan katafariyar dabbar doron kasa tana cin abinci daidai da dundumemen jikinta.

A cewar kwararrun masana kan giwar Afirka, Norman Owen-Smith na Jami'ar Witwatersrand da ke Johannesburg a Afirka ta Kudu, inda namijinta ke lakume kaso guda cikin 100 na nauyinta a kan busasshen tundurkin kasa a ko wacce rana, yayin da ta-macen da ke shayarwa ke cin kashi 1.5 cikin 100 don su ci gaba da rayuwa.

Panda na cin abincin da nauyinsa ya kai kilo 12.5 na kwangwala ko wacce rana.

Namijin yana da nauyin ton 6, don haka abin da yake ci nauyinsa ya kai kilo 60 na busasshen abinci ba tare da an hada da yawan ruwan da ta kwankwada ba, al'amarin da ka iya nunkawa da rubi hudu.

Hamshakan dabbobi masu shayarwa kan shafe tsawon rana wajen kai-kawon cin korayen tsirran da ke ba su kuzarin rayuwa. Sukan iya shafe sa'o'i 18 suna cin abinci a rana, gwargwadon abin da ya samu.

Haka kuma hamshakiyar yanyawar Sin (Panda) kan shafe sa'o'i 14 tana gwagwiyar kwangwala.

Masu bincike sun yi nuni da cewa wanan abincin bai cika kosar da dabbobin ba, wadanda tsarrin sarrafa abincinsu na iya sarrafa ko wanne irin nau'in abinci, wanda da sarrafa dimbin tsirrai ba.

Wannan ke nuni da dalilin da ya sanya yanyawar Panda ke cin dimbin abincin da nauyinsa ya kai kilo 12.5 na kwangwala a ko wacce rana don samun isasshen abincin da suke bukata, kuma shi ne hujja da ke nuni da kimar kashinsu.

Daukacin maciyan tsirrai kan shafe tsawon lokaci suna bibiyar dimbin gayayyaki da itatuwa don samun isasshen abincin da zai ba su kuzari, yayin maciyan nama kan mayar da hankali kan kayan makwalashe (abincin da ake dafawa cikin gaugawa).

Brock Fenton na Jami'ar Western da ke Canada ya ce adadin an "zuzuta shi," sakamakon  biyu mabapaka gudanar kan nau'ukan jemage a shekarun 1950.

Nau'ukan jemagen Japan kan shirya shirin cin abinci na gaba kafin ma ya lakume wanda ke gabansa.

Fenton ya ce daya daga binciken da aka gudanar ya yi nazari ne kana bin da ke cikin jemage mai launuka uku bayan ya gama cin abinci, yayin da dayan kuwa ya bi kadin nau'ukan jemage kananan masu launin kasa-kasa a dakin binciken kan yadda yake kama sauraye da kudajen da ke zarya kan 'ya'yan itace.

Babu daya daga cikin binciken da ya bayar da adadin na gaskiya kan yawan kwarin da karamin jemage mai launin kasa-kasa ke lakumewa a daji.

Kuma karamin jemage mai launin kasa-kasa na cin dimbinci ba wai sauraye kadai ba: sun ma fi son abubuwan masu girma, kamar tsutsotsi, a duk lokacin da suka samu damar kama su.

Wani bincike da aka gudanar kan jemagu a kasar Canada ya yi nuni da cewa sauraye wani yanki ne kadan daga abincinsu.

Don haka ta yiwu fadadawa aka yi cewa suna iya lakume sauro a ko wacce dakika 3.6.

Sai dai akwai hujjar da ke nuni da cewa ire-iren jemagu sukan kara kaimin farautar abincinsu doin samun gwargwadon abin da ya wadata da suke ci.

A shekarar 2016 bincike ya nuna cewa Jemagun Japan kan shirya cin abinci na gaba kafin ma su lakume wand ake gabansu.

Sabanin yadda ake ganin tashinsu, jemagun kan tsara shawaginsu bisa la'akari da irin abin da za su iya sura a hanya.

Akwai sauran kananan kasa-kasan dabbobi masu shayarwa wadanda ke cin abinci babu kakkautawa: nau'ukan jabar daji (the shrews).

A kalla ko wacce tsiryar Amurka hummingbird na lakume sukarin da ya kai rabin nauyinta a ko wacce rana.

Jabar dawan da aka sani dole ta ci abin da ya yi daidai nauyinta da kashi 80 zuwa 90 cikin 100 a tsakanin sa'o'i 2 zuwa 3.

Karamar jabar dawa, wadda ta kai rabin girman 'yar uwarta tana cin kashi 125 cikin 100 na abincin da ya kai nauyin jikinta a kowace rana.

Irin wadannan dabbobi masu shayarwa suna da saurin sarrafa abinci, al'amarin da ke nuni da cewa nan take zai narke ya ba su kuzari cikin hanzari.

Don haka sai sun ci abinci akai-akai dibge da abinci mai kara lafiya na protein da dabbobi masu kasha ke ci ko yunwa ta halaka su.

Duk wata tattaunawa kan sarrafa abinci to za ta bi kadin tsiryar Amuyrka (hummingbirds).


Wadannan halittu masu tashin ban mamaki sun fi shan zakin sukari don samun kuzarin tashi. Sukan bubbuka fuka-fuklinsu sau 50 a kowace dakika, irin wadannan tsuntsaye sun fi saurin sarrafa abinci a jerin dabbobi masu kashi.

Ta yiwu ka ji labarin cewa akalla tysiryar Amurka na lakume zakin sukari da ya kai kimar rabin nauyin jikinta a kowace rana, inda take cin abinci bayar kowane minti 15 a furannin kallo.

Akan sarrafa dimbin sinadarin kuzari da ke tare don bunkasa karamin dan tayi zuwa tsutsar siliki.

"Yawan zakin furen kallo da tsiryar Amurka ke lakumewa na iya bambanta," a cewar Adam Hadley, ja-gaban masu binciken tsiryar Amurka (hummingbird) a Jami'ar Jihar Oregon.

"Musamman tunda suna da mabambanta girman jiki, wanda ya kama daga giram 2.5 na kudan tsiryar Amurka (bee hummingbird) zuwa babbar tsiryar (giant hummingbird)."

Yayin da manya ke kwankwadar dimbin zakin furanni, suna sarayar da makamashin kuzarinsu ne a hankali fiye da kananan tsuntsaye. Wannan na nuni da cewa, in an kwatanta, kananan halittu sun yi fama da matsananciyar yunwa.

Hadley ya ce tsuntsaye na adana makamashi har zuwa lokacin da suka bukaci amfani da shi. "Abin sha'awar shi ne yadda suke adana abin da ya kai kashi 17 cikin 100 na nauyin jikinsu na maiko, ta yadda za ta kasance kowace tsiryar amurka za ta yi amfani da 30lb a rana guda."

Sauran nau'ukan halittu na nuni da cin abincin ban mamaki a wani yanayin lokaci na rayuwarsu. Alal misali, akwai bukatar dimbin makamashin kuzari don bunkasar dan-tayi zuwa tsutsar siliki.

Kwaron tsutsar siliki (The Polyphemus moth) an yi masa lakabi ne da sunan gwarazan Girkawa da Homer ya bijiro da su a labaran ban mamaki, saboda a kowane fufffike yana da alamar kwayar ido.

Sai dai daukacin halitta mai cin mutum da tsutsa mai lakume tsirrai abu guda ne wajen zakuwar son cin abinci da yawa.

Don mu kamo tsutsa, sai mun rika cin abincin da nauyinsa ya kai laba 50 zuwa 200 na latas a kowace rana.

Kamar yadda Kundin shahararrun al'amuran duniya Guinness ya tattara cewa, kwaron tsutsa irin "caterpillar" na cin abincin da nauyinsa ya rubanya na jikinta sau 86,000 a kwanaki 56.

Amma Andrei Soirakov jagoran masu tattara bayanai a gidan kayan tarihin albarkatun kasa na Florida cewa ya yi, akwai tababa kan adadi.

Wanan kawai tamkar ka auna abin da mutum ke ci ne tsawon rayuwar yarintarsa, sannan ka kwatanta shi da nauyinsu a lokacin da suke kamar jariri sabuwar haihuwa.

Sourakov ya ce aikin da aka gudanar kwanan nan a Jami'ar Florida ya gano cewa kwaron luna, wanda yake kwatankwacin girin irin wadannan halittu, kawai suna cin abin da ya kai rabi ko biyu bisa uku na nauyin jikinsu a ko wacce rana.

"Har yanzu dai lamarin da kayatarwa," inji Sourakov. "doin su yi daidai da kwaron tsitsar 'caterpillar' to sai mun ci laba 50 zuwa 200 na latas kowace rana."

Karara yake, a cewar Eric Carle yunwar kwaron tsutsar caterpillar ta shahara ba kai makurar da ake nuni da ita ba.

Dabba ta karshe da muke bin kadin tsananin yunwarta a duniya ba lallai su kasance mashahuran abubuwan da ake nuni da su a littattafan labarai na yara.

Ko da yake yanayin cina bincinsu na musamman an tattaro shi ne don ceton rayuwar mutane, inda aka siffanta su da dodanni masu ban tsoro.

Source:BBC Hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Unknown at 09:42
In Labari
Yadda Giwan Ruwa Kecin Kwari Miliyan 40 A Rana Title : Yadda Giwan Ruwa Kecin Kwari Miliyan 40 A Rana
Description : Tsananin son cin abinci da matsananciyar yunwa da galabaita. Daukacinmu akwai ranakun da mukan yi fama da yunwa, amma ko yunwarka ta kai ga ...
Rating : 5
Related Posts: Labari

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Yadda Giwan Ruwa Kecin Kwari Miliyan 40 A Rana"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2026 (2)
    • ►  June (1)
    • ►  January (1)
  • ►  2025 (5)
    • ►  December (5)
  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ▼  October (258)
      • Zaa Fadada Rijiyar Zam Zam A Masallacin Makkah
      • Buhari Ya Kori Babachir
      • Allah Yayi Rasuwa Wa Matar Danjuma Goje
      • Kenyatta Ya Sake Lashe Zaben Kenya
      • Lukaku Shafaffe Da Mai Ne-Mourinho
      • Yadda Na Sauya Rayuwar Abokina Dan Shaye Shaye
      • Sanata Wamakko Ya Tsallake Rijiya Da Baya
      • An Killace Mutum 60 Masu Kyandar Biri A Kano
      • Anyi Walkiya Sau 176,000 A Dare Daya A Australia
      • Masu Sukata Sunji Kunya-Wenger
      • Matsalar Da Mata Ke Shiga Sanadiyan Zubewan Ciki
      • Yan Kunan Bakin Wake Sunkai Hari Maiduguri
      • Burina Nataka Leda A Kasashen Turai
      • Madrid Tasha Kashi A Hanun Girona
      • Aure Kan Iya Hana Samun Cutar Mantuwa-Bincike
      • Rabin Gwamnatin Buhari 'Yan PDP Ne-Hameed Ali
      • Ansake Kai Harin Bam Mogadishu
      • Buhari Na Nuna Wariya Wajen Yakan Cin Hanci-Farfes...
      • Ana Bincike Ko Kyandar Biri Taje Kano
      • Muna Kama Macizai Ne Don Ceton Rayukan Jama'a
      • Mutane Na Mutuwa Sabida Yunwa A Congo
      • Matata Da 'Ya'yana 5 Na Hanun Boko Haram
      • Buhari Ya Nemi Afuwar Yan Malisa Kan Hanasu Ganinshi
      • Meyasa Ba'a Biyan Yan Wasa Mata Kamar Yadda Ake Bi...
      • Burundi Ta Fice Da Kotun ICC
      • Yan Majalisa Sun Mayar Da Cin Hancin $8,000
      • Yankin Catalonia Ta Balle Daga Spain
      • Harry Kane Bazai Buga Karawarsu Da Man Utd Ba
      • IS Tadauki Alhakin Harin Da Aka Kai Yobe
      • Don Me Buhari Ke Gum In Makusantansa Sunyi Laifi?
      • Matsalar Tabin Hankali Nasa Asarar Naira Triliyan 47
      • Andaure Mutumin Dayasa Wa Mata 30 Cutar Kanjamau
      • Jita Jitane Kisan Da Ake Yadawa Wai Anyi A Zamfara...
      • Jami'an Tsaro Sun Hana Saraki Da Dogara Shiga Fada...
      • Bawani Aibu A Auren Wuri
      • Anyi Dauki Ba Dadi Tsakanin Jam'iyu Biyu A Kenya
      • Za'a Kona Gawar Sarkin Thailand Bayan Shekara Daya...
      • Buhari Ya Kammala Kasafin Kudi Na 2018
      • Meyasa Ake Aurin Wuri A Amurka?
      • Bazamu Kori Malami A Jihar Sokoto Ba,Zamu Horas Da...
      • Shekara Uku Kenan Baasami Bullowar Cutar Polio A J...
      • Zaben Shugaban Kasar Kenya
      • Tsofaffin Mayakan Ivory Cost Na Neman Hakkinsu
      • Yadda Wani Nau'in Abinci Ya Janyo Mummunar Cuta A ...
      • Matar Dake Aikin Fasa Dutse Don Ciyar Da Kanta A A...
      • Fursunoni Zasuyi Zabe 2019
      • Sojin Nijeriya Sunkashe Matan Shekau A Wani Lugude...
      • Fifa Ta Wanke Juventus Kan Batun Pogba
      • Rahma Sadau Tanemi Gafaran Ganduje Da Sarki Sunusi...
      • Yan Shi'a Na Gudanar Da Zanga Zangan Sako Zakzaky
      • Video: This Is The Way Official Trailer Starring A...
      • Majalisa Zata Binciki Batun Abdulrasheed Maina
      • United Takai Mataki Na Gaba A Wasan League Cup
      • Sabuwar Rigakafin Cutar Typhoid
      • Twitter Ta Fidda Sabbin Kaidojin Talla
      • Ziyara Gidan Abdulrasheed Maina
      • Ko Meyasa Kasar Zimbabwe Tanada Ministan WhatsApp?
      • Zaben Kenya Na Cike Da Takaddama
      • Dalilin Dayasa Nakeso Jonathan Ya Halarci Kotu-Metuh
      • Gwamnatin Tarayya Sun Bar Jihohi Su Kula Da Manyan...
      • Phil Neville Nason Karban Kocin Everton
      • Ba Bambanci Tsakanin Gwamnatin Buhari Dana Jonatha...
      • Amurka Zata Taimakawa Kotunan Nigeria
      • Buhari Ya Tauna Tsakuwa
      • Haryanzu Giwayen Afirka Na Fuskantar Barazana
      • Sojin Amurka Bazasu Fice Daga Nijar Ba
      • Ban Manta Sunan Sojan Amurka Ba-Trump
      • Ana Zaton Wani Yakamu Da Cutar Money Pox A Nasarawa
      • Rundunar Sojin Sama Sunyi Wa Maboyan Boko Haram Ru...
      • Bani Kewar Yin Fina Finan Kannywood-Mansura Isa
      • Everton Ta Kori Kocinta
      • Wanene Abdulrasheed Maina?
      • Ronaldo Ne Gwarzon Kwallon Kafa Na 2017
      • Labarai 25 Da Aka Tantance Na Gasar Hikayata Na 2017
      • 'Yan Shia Ne Suka Hana Kwace Iraqi Daga Syria-Iran
      • Bam Bai Sunkashe Mutane 14 A Maiduguri
      • Jami'ar Katsina Zata Dauki Masu Kama Macizai Aiki
      • Ana Taron Hana Auren Wuri A Afrika
      • 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Far Wa Maiduguri
      • Hukumar WHO Tasoke Mukamin Da Akabawa Mugabe
      • Tottenham Ta Lallasa Liverpool
      • Waye Zai Lashe Gwarzon Dan Kwallon Bana A Cikin Ne...
      • Mai Zai Faru Idan Tashin Duniya Yazo?
      • An Fallasa Sunayen Berayen Harda Na Gida-Shehu Sani
      • Yawan Wadanda Aka Kashe A Harin Mogadishu Ya Kai 358
      • An Hallaka Sojojin Nijar 13 A Kan Iyakarta Da Mali
      • Meyasa Malamai Da Dalibai Ke Faduwa Jarabawa A Nij...
      • Wasikun Soyayya Da Obama Ya Rubuta Wa Budurwansa
      • Masu Shayi Sun Koka Kan Tsadan Burodi A Kaduna
      • Messi Ne Gwarzon Dan Wasa-Valverde
      • Buhari Yana Son Hadinkan Nigeria-Atiku
      • Ankashe 'Yan Shia 60 A Masallaci A Afghanistan
      • Ana Mamakin Sabon Mukamin Da Aka Bawa Mugabe
      • Dalibi Ya Bindige 'Yan Ajinsu Guda Biyu
      • Kullun Sai Nayi Jana'izar Wanda Maciji Ya Sara-Liman
      • An kashe Yan Sandan Masar 53 A Wani Kwanton Bauna
      • Atiku Ya Jinjina Wa Shugaba Buhari
      • Music: Lee Weed ft BOC - Kuna Ina
      • APC Nada Tsarin Yadda Zata Fidda Dan Takaran Shuga...
      • Wani Shiri INEC Tayi Don Zaben 2019
      • Yadda Hadiman Jonathan Suka Taya Patience Satan Bi...
      • Tari Yakashe Yara 11 A Jihar Kano
      • Ankashe Mana Yara 6,Ansace Mana Shanu Sama Da 200 ...
      • Wayafi Morar Wani Tsakanin Nigeria Da China
      • Yadda Wani Yaci Zarafina A Motar Bas
      • Kamfanin Nivea Na Tsaka Mai Wuya
      • Antura Jiragen Yaki Jihar Filato
      • Kotu Tasaki Dan Atiku
      • Ansace Turawa 'Yan Mishan A Nigeria
      • Gwamnatin Saudiyya Ta Hana Yada Hadisan Karya
      • Messi Yaci Kwallo Dari A Wasan Nahiyar Turai
      • Macizai Nasaran Sama Da Mutum Miliyan Biyar A Shek...
      • An Gargadi 'Yan Nijeriya Kan Zuwa Asibitocin Turai
      • Ba Ruwana Da Kowani Jam'iyya-Obasanjo
      • Kotu Tabada Daman Akawo Mata Nnamdi Kanu
      • Ana Zargin Marcelo Da Kin Biyan Haraji
      • Kome Buhari Yajeyi A Turkiyya?
      • Anfara Taro Kan Harkar Noma A Landan
      • Liverpool Tayi Wa Maribo Ruwan Kwallaye
      • Shin Anayin Lalata Da 'Yan Matan Kannywood?
      • Dokar Trump Kan Musulmi Tagamu Da Cikas
      • Rashin Biyan Ma'aikata Albashi Yanaban Takaici-Buhari
      • Babban Jami'ar Hukumar Zaben Kenya Tagudu Amurka
      • Yadda Ake Rawa Da Gawarwaki A Madagaska
      • Kachikwu Babban Makaryaci Ne-Ofishin Osinbajo
      • Zaa Saki 'Abu Hassan'
      • Abubuwa Uku Dake Burgeni Da Wadda Ke Tadamin Hanka...
      • Saraki Ya Roki Duniya Tayi Wa Taaddaci Taron Dangi
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • MAGANIN KARYA SIHIRI DA IZININ ALLAH
    TAMBAYA TA 1606 ********************* Assalamu alaikum, Malam barka da aiki ya hidima da mutane Allah ya saka muku da mafificin alkairi. ...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...
  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Rikicin Rarara da Naziru Sarkin Waka Ya Ƙare? Naziru Ya Taya Rarara Murn...
  • Kannywood Director Iliya Tantiri involve in a car Accident
    the accident happen on his way to Kaduna. the car was burnt but the Director was fine
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Zanga-zanga A Bauchi-Gwamnatin Ta Saka Dokar Hana Fita Da Zirga-Zirga Ac...
  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger