1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Labari » Mai Zai Faru Idan Tashin Duniya Yazo?

Mai Zai Faru Idan Tashin Duniya Yazo?

By Unknown
Add Comment
Sunday, 22 October 2017

Mummunar annoba ta yi wa al'umma dabaibayi.

Bazuwarta ya karade ko'ina a duniyarmu mai gagarumin ci gaban birane cike da al'umma da jiragen sama masu kai-kawo a sararin samaniya, sai dai mun gaza shawo kan al'amuran tsawon lokaci.

Bunkasar harkokin rayuwar al'umma ya tarwatse, idan dumbin mutane suka mutu sai ka ji kamar ka zautu, amma saboda wasu makarai na jiki sai ka shawo kan matsanancin zazzabi, ka farka a gida mai sanyi, babu wutar lantarki ba ruwan famfo ko gas din hura wutar dumama ruwa ko girki.

Tituna za su yi tsit babu kowa, babu jirgin sama da ke shawagi a sama.

Kai kadai ka tsira a wannan rikirkitaccen al'amari na karshe.

Wadannan su ne bayanan da aka yi ta hakaito mana daga cikin littattafai, wadanda suka hada da "Can ticle for Leibowitz ko The Road," har ma da wasan kwamfuta na baya-bayan nan irinsu "the Last of Us da fina-finai kamar Am Legend ko Mad Max.

Daukacin wadannan labaran suna nuni da fahimtar masu ra'ayin mutanen da ke sanya warki, su yi ta gararamba a daji.

Ko mene ne hakikanin gaskiyar wadannan al'amura?

Kirkirarren labari game da tashin duniya nuni ne ga fahimtar wadanda ba sa sanya tufafi illa warki.

Idan ka samu kanka a matsayin wanda ya tsira daga masifar da ta tarwatsa duniya ta share mafi yawan mutane daga doron kasa. Ko me za ka iya yi?

Irin wannan ne muhimmin ilimin da kake bukata don tsira, har ka kara ci gaba da bunkasa?

A nan ne gwanintakarka za ta kai makura.

Mutuwar yawa kaka! Tabbas za mu samu damar ci gaba ne ta hanyar bibiyar tarihi, inda muka gina duniya mai ci gaban zamani a matakin farko ta hanyar aikin hadin gwiwar zamantakewar halittu, tuni da ma al'umma ta ginu kan tsarin zamantakewa.

Duk da cewa za a samu yamutsi bayan wargajewa, mutane za kuma su sake zama cikin tsarin al'ummomi ba da dadewa ba.

Tambayar dai ita ce saura da me..?

Wadanne al'amura ya kamata ka ba fifiko, kuma mene ne ya kamata al'ummarka ta kara kaimi wajen ganin ta farfado da shi bayan shekaru?

Wannan shi ne daya daga cikin mai yiwuwa a jerin al'amura.

Kwanakin farko

Da zarar mutane sun daina sa ido da gyara tashoshin samar da makamashi, sadarwa za ta gaza cikin sauri.

Sai dai a koma laluben faifan zuko makamashin rana ko amfani da jannareto daga wani gini, ta yadda za ka samu wutar lantarki na wucin gadi.

Intanet za ta shafe nan da nan, da zarar rumbun sakonnin kwamfyutocinsu ya daina aika sakwanni, da zarar man fetur din da ke cikin jannareto ya kare, don haka kada ka dauka za ka ci gaba da dogara da Wikipedia wajen samun ilimi.

Sai dai wannan ba yana nufin wayarka ta alfarma za ta zama fanko ba ne.

Manuniyar hanyar cikinta na amfani da ma'aunin maganadisu, ta yadda za ka ci gaba da gefa ne hanyarka lokacin da kake tafiya, kuma a gaskiya taswirar da ke kan wayar za ta ci gaba da taimaka maka wajen gane inda ka dosa (GPS).

Manunin taswirar tauraron dan Adam zai ci gaba da aiki na wasu makonni bayan rushewar al'amura, amma bayan wata shida aikin da yake yi daidai zai wargaje ya daina amfani kwata-kwata.

Abubuwan da za ka fifita su ne ka tabbatar ka tara ruwa da abincin gwangwani da managartan suturun fita waje.

Makonnin farko

A makonnin farko ta yiwu ka hadu da wasu mutane kalilan da suka tsira.

Ka yi taka-tsantsan wajen hulda da baki har sai ka hadu da wadanda ka aminta da su, wadanda za ku yi taimakekeniyar ba wa juna kariya, kuma zai yi matukar taimakawa wajen hada karfi a fafutukar tara abincin da kuke bukata.

A yanzu yankin birnin da ka fara harkoki ya fara rashin dadi.

Warin gawawwakin da suka rube ya cika iska, ga karnukan da ke jin yunwa sun yi gungu.

Ko ta wane halin, birni na zamani ya cika da kirkirarrun abubuwa, wadanda suka dogara kan tsarin ci gaban rayuwar da ta samar da su.

Rashin lantarkin da ke motsa matakalar bene da haskaka hanya, tsaftataccen ruwa zai zamo gurbatacce, kasa na zirga-zirga, jirgi zai zama tundurki, don haka rayuwa za ta yi maka sauki a karkara.

Gidan gona na al'ada da murhun wuta, inda girki zai yiwu cikin dadi bayan rushewar kayan amfani na zamani.

Za ka iya bincike tarin sharar sassan birane don tara abinci ko kayan amfani, a daidai lokacin da kake kokarin sake koyon yadda za ka kirkiro abubuwa da kanka.

Watannin farko

Abin da zai fi damunka shi ne yadda za ka samu tsaftataccen ruwan sha, ka kuma kauce wa cututtukan da ke bazuwa a cikin ruwa, wadanda suka cutar da mutane dubban shekaru.

Tafasawa hanya ce ta kashe kwayoyin cuta a ruwa, amma tana bukatar dumbin makamashi daga burbushin abubuwa da suka rage, amma wata rana dole sai ka yi amfani da dabarun sarrafa sinadarai don tabbatar da cewa ruwan da kake kai wa bakinka bai halaka ka ba.

Za a iya tsaftace ruwa daga sinadaran kwayoyin cuta da ke kara-kaina a dakin girki ko kududdufan ninkaya da za ka zuba sinadarin Chlorine (Sodium hypochlorite and Calcium hypochlorite) sai a narkar da shi yadda zai kashe kwayoyin cuta, amma babu gubar da za ta cutar da kai.

A nan kana amfani da kimiyyar sinadarai wajen sarrafa chlorine, don inganta ruwan famfon da muke sha a yau, wanda zai zamo tarihi, tun da irin wannan ci gaban a fannin tsafta da kula da lafiyar al'umma ya taimaka mana wajen zama a biranen da ke kwasar dumbin mutane a cakude.

Har sai ka samu dabarar sarrafa chlorine ta kashin kanka, wata karamar fasahar tsaftace ruwa da ake amfani da makamashin rana.

Irin wannan dabarar Hukumar Lafiya ta Duniya na koyar da ita a kasashe masu tasowa, kuma kawai cika robar ruwa ake yi da ruwan ake ganin ya gurbata a bar shi cikin rana tsawon kwana daya ko biyu.

Makamashin hasken rana zai ratsa cikin robar ruwan ya kashe kwayoyin cutar.

Wanke hannayenka ma yana da matukar alfanu wajen hana yaduwar cuta.

Za a iya yin sabulu ta hanyar tatso kitsen dabba ko man tsirrai; ta hanyar tafasa sinadarin alkaline.

Alkaline na da matukar muhimmanci cikin jerin sinadarai a daukacin tarihi, kuma za a iya kwakwulo shi daga muhallinka.

Kanwa (Potassium Carbonate) za a iya ciro ta, ta hanyar zuba ruwa a cikin tokar itacen girki, sannnan tokar soda daga burbushin tsirran teku da aka kona ko gishirin tsirran da ke gabar ruwa irinsu samphire ko saltwart.

Tattara tsirran teku don samar da soda babbar harka ce a gabar Tekun Atlantic ta kasar Scotland da Ireland tsawon karnoni.

Gobe za mu wallafa muku ci gaban wannan makala mai taken: 'Yadda za a tunkari karshen duniya.'

Source: BBC Hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Unknown at 09:30
In Labari
Mai Zai Faru Idan Tashin Duniya Yazo? Title : Mai Zai Faru Idan Tashin Duniya Yazo?
Description : Mummunar annoba ta yi wa al'umma dabaibayi. Bazuwarta ya karade ko'ina a duniyarmu mai gagarumin ci gaban birane cike da al'umm...
Rating : 5
Related Posts: Labari

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Mai Zai Faru Idan Tashin Duniya Yazo?"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ▼  October (258)
      • Zaa Fadada Rijiyar Zam Zam A Masallacin Makkah
      • Buhari Ya Kori Babachir
      • Allah Yayi Rasuwa Wa Matar Danjuma Goje
      • Kenyatta Ya Sake Lashe Zaben Kenya
      • Lukaku Shafaffe Da Mai Ne-Mourinho
      • Yadda Na Sauya Rayuwar Abokina Dan Shaye Shaye
      • Sanata Wamakko Ya Tsallake Rijiya Da Baya
      • An Killace Mutum 60 Masu Kyandar Biri A Kano
      • Anyi Walkiya Sau 176,000 A Dare Daya A Australia
      • Masu Sukata Sunji Kunya-Wenger
      • Matsalar Da Mata Ke Shiga Sanadiyan Zubewan Ciki
      • Yan Kunan Bakin Wake Sunkai Hari Maiduguri
      • Burina Nataka Leda A Kasashen Turai
      • Madrid Tasha Kashi A Hanun Girona
      • Aure Kan Iya Hana Samun Cutar Mantuwa-Bincike
      • Rabin Gwamnatin Buhari 'Yan PDP Ne-Hameed Ali
      • Ansake Kai Harin Bam Mogadishu
      • Buhari Na Nuna Wariya Wajen Yakan Cin Hanci-Farfes...
      • Ana Bincike Ko Kyandar Biri Taje Kano
      • Muna Kama Macizai Ne Don Ceton Rayukan Jama'a
      • Mutane Na Mutuwa Sabida Yunwa A Congo
      • Matata Da 'Ya'yana 5 Na Hanun Boko Haram
      • Buhari Ya Nemi Afuwar Yan Malisa Kan Hanasu Ganinshi
      • Meyasa Ba'a Biyan Yan Wasa Mata Kamar Yadda Ake Bi...
      • Burundi Ta Fice Da Kotun ICC
      • Yan Majalisa Sun Mayar Da Cin Hancin $8,000
      • Yankin Catalonia Ta Balle Daga Spain
      • Harry Kane Bazai Buga Karawarsu Da Man Utd Ba
      • IS Tadauki Alhakin Harin Da Aka Kai Yobe
      • Don Me Buhari Ke Gum In Makusantansa Sunyi Laifi?
      • Matsalar Tabin Hankali Nasa Asarar Naira Triliyan 47
      • Andaure Mutumin Dayasa Wa Mata 30 Cutar Kanjamau
      • Jita Jitane Kisan Da Ake Yadawa Wai Anyi A Zamfara...
      • Jami'an Tsaro Sun Hana Saraki Da Dogara Shiga Fada...
      • Bawani Aibu A Auren Wuri
      • Anyi Dauki Ba Dadi Tsakanin Jam'iyu Biyu A Kenya
      • Za'a Kona Gawar Sarkin Thailand Bayan Shekara Daya...
      • Buhari Ya Kammala Kasafin Kudi Na 2018
      • Meyasa Ake Aurin Wuri A Amurka?
      • Bazamu Kori Malami A Jihar Sokoto Ba,Zamu Horas Da...
      • Shekara Uku Kenan Baasami Bullowar Cutar Polio A J...
      • Zaben Shugaban Kasar Kenya
      • Tsofaffin Mayakan Ivory Cost Na Neman Hakkinsu
      • Yadda Wani Nau'in Abinci Ya Janyo Mummunar Cuta A ...
      • Matar Dake Aikin Fasa Dutse Don Ciyar Da Kanta A A...
      • Fursunoni Zasuyi Zabe 2019
      • Sojin Nijeriya Sunkashe Matan Shekau A Wani Lugude...
      • Fifa Ta Wanke Juventus Kan Batun Pogba
      • Rahma Sadau Tanemi Gafaran Ganduje Da Sarki Sunusi...
      • Yan Shi'a Na Gudanar Da Zanga Zangan Sako Zakzaky
      • Video: This Is The Way Official Trailer Starring A...
      • Majalisa Zata Binciki Batun Abdulrasheed Maina
      • United Takai Mataki Na Gaba A Wasan League Cup
      • Sabuwar Rigakafin Cutar Typhoid
      • Twitter Ta Fidda Sabbin Kaidojin Talla
      • Ziyara Gidan Abdulrasheed Maina
      • Ko Meyasa Kasar Zimbabwe Tanada Ministan WhatsApp?
      • Zaben Kenya Na Cike Da Takaddama
      • Dalilin Dayasa Nakeso Jonathan Ya Halarci Kotu-Metuh
      • Gwamnatin Tarayya Sun Bar Jihohi Su Kula Da Manyan...
      • Phil Neville Nason Karban Kocin Everton
      • Ba Bambanci Tsakanin Gwamnatin Buhari Dana Jonatha...
      • Amurka Zata Taimakawa Kotunan Nigeria
      • Buhari Ya Tauna Tsakuwa
      • Haryanzu Giwayen Afirka Na Fuskantar Barazana
      • Sojin Amurka Bazasu Fice Daga Nijar Ba
      • Ban Manta Sunan Sojan Amurka Ba-Trump
      • Ana Zaton Wani Yakamu Da Cutar Money Pox A Nasarawa
      • Rundunar Sojin Sama Sunyi Wa Maboyan Boko Haram Ru...
      • Bani Kewar Yin Fina Finan Kannywood-Mansura Isa
      • Everton Ta Kori Kocinta
      • Wanene Abdulrasheed Maina?
      • Ronaldo Ne Gwarzon Kwallon Kafa Na 2017
      • Labarai 25 Da Aka Tantance Na Gasar Hikayata Na 2017
      • 'Yan Shia Ne Suka Hana Kwace Iraqi Daga Syria-Iran
      • Bam Bai Sunkashe Mutane 14 A Maiduguri
      • Jami'ar Katsina Zata Dauki Masu Kama Macizai Aiki
      • Ana Taron Hana Auren Wuri A Afrika
      • 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Far Wa Maiduguri
      • Hukumar WHO Tasoke Mukamin Da Akabawa Mugabe
      • Tottenham Ta Lallasa Liverpool
      • Waye Zai Lashe Gwarzon Dan Kwallon Bana A Cikin Ne...
      • Mai Zai Faru Idan Tashin Duniya Yazo?
      • An Fallasa Sunayen Berayen Harda Na Gida-Shehu Sani
      • Yawan Wadanda Aka Kashe A Harin Mogadishu Ya Kai 358
      • An Hallaka Sojojin Nijar 13 A Kan Iyakarta Da Mali
      • Meyasa Malamai Da Dalibai Ke Faduwa Jarabawa A Nij...
      • Wasikun Soyayya Da Obama Ya Rubuta Wa Budurwansa
      • Masu Shayi Sun Koka Kan Tsadan Burodi A Kaduna
      • Messi Ne Gwarzon Dan Wasa-Valverde
      • Buhari Yana Son Hadinkan Nigeria-Atiku
      • Ankashe 'Yan Shia 60 A Masallaci A Afghanistan
      • Ana Mamakin Sabon Mukamin Da Aka Bawa Mugabe
      • Dalibi Ya Bindige 'Yan Ajinsu Guda Biyu
      • Kullun Sai Nayi Jana'izar Wanda Maciji Ya Sara-Liman
      • An kashe Yan Sandan Masar 53 A Wani Kwanton Bauna
      • Atiku Ya Jinjina Wa Shugaba Buhari
      • Music: Lee Weed ft BOC - Kuna Ina
      • APC Nada Tsarin Yadda Zata Fidda Dan Takaran Shuga...
      • Wani Shiri INEC Tayi Don Zaben 2019
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger