1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kazamar Gida Part 9

Kazamar Gida Part 9

By Abdul Mk
Add Comment
Sunday, 15 November 2015
Ranaku suna ta ja har Allah Ya kawo ranar da aka yaye su Ladi daga sakandire. Yan uwan mahaifinta sun zo tayata murna. Ranar tayi murna marar misaltuwa saidai tana jin kewar rabuwa da aminiyarta Basma wacce zata tafi can Zaria garin iyayenta acan zatayi jami'arta. Babu wani sirrin Ladi da Basma bata sani ba,daidai da wannan zancen na Jafar tasan da zamanshi. Koda ace Ladi tayi niyyar karaya,tayi niyyar sanarwa Jafar gaskiyar lamari,Basma takan hanata tana mai karfafa mata gwuiwa akan cewar wataran sune da nasara tunda da zuciya d'aya take sonshi.
Sati d'aya da yayesu daga sakandire,Basmatazo har nan gidansu Ladi tayi mata sallama,suna kuka suka rabu saboda tsananin shakuwar da sukayi bayan sun daukarwa juna alk'awarin yin waya don bincikar lafiyar junansu akowace rana..
Yan uwan baban ladi,Malam mukhtar,ko kusa basu takurawa yaransu akan lallai bayan kammala sakandire zasu aurar dasu. Wannan ne yasa sam ladi bata samu matsala ba wajen bayyana ra'ayinta na son cigaba da karatunta a fannin business admin. Sun bita da addu'ar fatan alheri. Mama itama tana da burin d'iyarta ta cigaba da karatunta acewarta ko nan gaba zatayi alfahari da Ladi,musamman ma saboda yan uwanta na Nijar fa sam basu so aurenta da Mukhtar ba a cewarsu bahaushe ne kuma d'an nijeriya basu fiye rik'on aure ba. Ganin ta nace dole sai shi d'in ne suka aura mata shi da sharad'in babu su babu ita. So ya rufe mata ido ta amince.
Bayan rasuwar Mukhtar ko kusa batayi gigin zuwa inda suke ba kamar yanda suma basu damu da ita ba. Ta dauki lamarin a matsayin don tana marainiya ne shiyasa kawunnanta sukayi mata haka. Wannan yasa koda wasa bata kara marmarin komawa gida nijar ba,hakanan ta dauki yan uwan Mukhtar tamkar nata babu mai nuna mata kyama...!
*********
Cikin ikon Mahalicci,shak'uwar Jafar da Hadiyya takai har shi da kansa yakai ga tambayarta garin da take da zama.
Gabanta ya fad'i,duk da cewar wani dadi ya mamaye zuciyarta,gab'ar da take zaman jiran zuwansa kenan. Tayi shiru kamar bazata ce komai ba.
"Baki jina ne?"
Ta muskuta sosai akan tabarmar da take zaune a tsakar gidansu
"Um na'am,ina jinka yaya j."
"Toh baki ban amsa ba."
"Ni 'yar kano ce."
Yace "Ashe gari d'aya muke,kayya meyasa baki sanarmin tun wuri ba na kawo ziyara dutsen dala?"
Sukayi dariya,ta tuna hirarsu ta rannan ashe fa aljana yake kiranta. Cikin wasa tace
"Ai kuwa kamar kasan muhullina kenan,kodai nazo yanzu ka ganni?"
Ya girgiza kansa tamkar tana ganinshi,cikin dariya yace
"No,ki rufamin asiri malama. A wace unguwa kike ne?"
Sanin da tayi bai tab'a sanin unguwarsu bane ya sanyata fad'a kai tsaye
"Ni 'yar Yakasai ce."
"Baki da nisa sosai da kasuwar da nake ma. Kinsan wani abu Hadiyya?"
"Saika fad'a yaya j." Ta amsa gabanta yana dukan tara tara, tana tsoron abunda zaice.
"Allah ne mai had'a bayinSa ba tare da sun san takamaiman dalilin had'uwar tasu ba. Haka kawai nake jinki a raina tamkar wata 'yar uwata ta jini Hadiyya. I want to know more about you,shiyasa nakeson kawo maki ziyara idan har kin amince."
Ai batasan menene tsoro da fargaba ba saida Jafar yayi wannan furucin,ita kam ai ta shiga uku. Ta yaya ma za'ace ta baiwa Jafar damar zuwa gareta tun yanzu alhalin bata gama tabbatar da cewa soyayyarta ta zauna a zuciyarsa ba? Gaskiya da sake,tana kunyar had'uwarsu a wannan lokacin.
"Shirun fa?"
Tayi wal da ido,ya taho da ruwan hawayenta. Ta shafesu tana mai kokarin saita muryarta
"Ka gani yanzu bana Kano,nazo hutu Zaria gidan kakannina amma ka bari da zarar na dawo zan maka kwatance har kofar gidanmu. Ni kaina ina jinka sosai a raina yaya j fiye ma da yanda kakejina. Banajin har na mutu zan bar jin abunda kemin yawo a zuciyata da jinin jikina game dakai."
Ta fad'a tana mai rufe idanuwanta,wutar kaunar Jafar na k'ara ruruwa a zuciyarta. Takanyi nadamar b'oye mishi gaskiyar ainahin wacece ita da tayi. Tana tsoron ranar da zai fahimta,lallai babu yanda za'ayi ya cigaba da mu'amala da marar galihu mai siyar da abinci a kasuwa irinta.
"Bari nayi sallah Hadiyya."
Ya kashe kiran,kawai saita fashe da kuka tana mai tausayawa kanta. K'arya bata da amfani ko kusa,yanzu gashi tana nadamar aikinta. Tana yaudarar kanta ne,saidai bazata tab'a samun namiji irin Jafar ba. Ya dace ace ta fuskanci rayuwarta,ya kamata ta fidda rai a kansa.
Ta janyo wayar ta kasheta gaba d'aya. Saida tayi kukan tausayawa kanta a karshe ta share hawayenta ta mike don d'ora alwalar sallar magrib. Mama batanan ta fita zuwa gidan gaisuwa.
**********
BAYAN WATANNI BIYAR
"Siyama zata koma gida har acan zata haihu. Banason ta haihu ba kusa dani ba,tunda ta shiga watanta zan tafi da ita can wajena."
Hajiyar Siyama ke wannan bayanin ga Jafar,wanda shigowarsa gidan kenan da yammacin ranar juma'a ya isketa zaune tare da Siyama a falo.
Abu d'aya ne baiji dad'insa ba,yanda ko kusa bata tashi sanar mishi ba sai a yau,a yau d'in ne kuma takeso su wuce. Amma bayan hakan ko kad'an bai damu ba,toh daman tunda cikinta ya tsufa ai ko mutuwa zaiyi yana naci,babu abunda take tsinana mishi. Duk yanda zai rok'eta da magiyar duniya amma ko kad'an Siyama burus takeyi mishi k'arshe ma ta juya mishi baya tayi kwanciyarta. Hakanan yake hak'ura ya kwanta don tuni ya ajiye dokarsa na kada ta k'ara shiga d'akinsa a gefe. Abunda ya riga ya sani yana sonta.
"Kana jina kayimin kunnen uwar shegu,ko kana son ka nunamin ban isa bane tunda ba ni na haifeka ba?"
Hajiya tayi maganar cikin bacin rai,da sauri Jafar yace
"Ba haka bane Hajiya,bakomai kuje. Allah Ya sauketa lafiya."
Bata ko amsa ba ta dubi Siyama
"Tashi muje ki had'o kayanki."
Jafar ya bisu da kallo sa'ilin da suka tura kansu k'uryar d'akin. Ya mik'e yayi nashi d'akin.
Acan kuwa,kayan Siyama gaba d'aya Hajiya ta rasa na kirkin da zata daukar mata. Sai banbamin fad'a takeyi tana tsaki.
"Kedai Allah Ya sauwake maki Siyama,ace kayanki babu kyawun duba kowanne babu wankakke? Shi Jafar bai iya bayar da wankin matarsa bane? Ko menene?"
Siyama ta hau kumbura fuska
"Yana bayarwa,an kwana biyu ne ba'a bayar ba."
Hajiya ta tabe baki
"Ke kika janyowa kanki. Tun farko babu irin kashedin da banyi maki ba akan ki gujewa auren wannan shegen yaron ke kuma kika nace mishi. Yanzu ai gashinan duk kin kod'e kamar ba kece 'yar gayun nan ba wacce samari da dattijai suka dunga rububinta. Ko haihuwa bakiyi ba duk kin koma wata tsohuwa. Yarinya ina hango maki jin dad'i a gidan Bash d'an gidan hakimi. Wannan yaron babu irin dukiyar da bai kashe akanki ba,duba abubuwan arzikin da ya dunga aikomana don ma Abbanki yakan hana a karb'a saidai nayi dabarar kira nace ya mik'a gidan yayarki rumaisa. Amma kika gujeshi,yanzu ai gashinan ya auri 'yar fillo suna Dubai. Ke kam talauci saidai...
"Ehem ehem."
Gyaran muryar Jafar tayi saurin katse maganarta,duk da ta tsorata ta hau basarwa
"Tafi,ga mayen yana kiranki. Dad'in abun dai gaskiyata nake fad'a. Atoh "
Siyama dai ta fice ta bar Hajiya da surutan borin kunya......!
Tuni ya juya ya koma d'akinsa,bai damu da sanin fad'an da Hajiya ke yi ba. Domin bazaiyi mamaki ba,tana da illolin da idan ya kama har duka sai a had'a mata dashi.
Ya juyo ya dubeta lokacin data shigo
"Kina bukatar wani abu ne?"
Sanin da tayi komai na bukatar jariri Jafar ya siya ya sanya ta girgiza kanta
"A'a."
Ya jinjina kanshi,ya zaro kud'i har dubu goma ya mik'a mata
"Ki rike wannan a hannunki koda wata bukatar zata tashi. Zan dunga kiranki muna gaisawa. Allah Ya raba lafiya."
Yana magana ne fuska a had'e,kasancewar sun kwana biyu yana fushi da ita. Jikinta a sanyaye ta karb'a ta had'o da hannunshi ta rike k'am,ya dubeta cikin mamakin hawayen daya gani suna zubo mata,ya daure yace
"Toh menene na kukan?"
Ta kwantar da kanta a kafad'arsa cikin sanyin murya tace
"Kayi hakuri don Allah ka yafemin my j. Banason na tafi na barka kana fushi dani."
Ta d'ago tana dubansa,shima duk jikinshi yayi sanyi
"Ko ka manta yanda haihuwa take?"
Ya shafi fuskarta
"Kada ki damu Siyama,idan nace zan iya fushi dake nayi k'arya,komai ya wuce tun ranar da akayi. Na chanja maki ne ko don gaba ki gane kurenki,haramunne juyawa miji baya a shimfid'a. Nima son zuciyata ta sanyani kasa yin adalci gareki,na manta cewa ke a yanzu abar lalla.."
"Yau naga sabon iskanci ni Maimuna! Ni zaku mayar yar iska? Bazaki fito bane daga d'akin nan muyi abunda zamuyi mu tafi?"
Jafar ya saketa
"Jeki kawai sai munyi waya."
Ta juya da sauri ta fita. Tana shiga falon Hajiya ta rankwasheta
"Kedai Allah Ya sauwake maki,ki cigaba da sakin jikinki har sai ya rainaki."
Siyama ta turo baki
"Kud'i fa ya bani."
"Har nawa?"
"Dubu goma."
Hajiya taja tsaki tayi cikin d'aki
"Matsiyaci kawai,mecece goma?"
Siyama cikin rashin jin dad'in furucin Hajiya ta bita d'akin. Saida suka kammala komai sannan Hajiya ta yiwa Abba waya ya turo mata direbansa bayan ta sanar mishi Jafar ne yace ta tafi da Siyama saboda haihuwa. Yayi na'am da zancen saidai yaso kwarai ace a wajen Hajjah zata zauna tunda dai duka d'aya ne amma bayason tashin hankalin Hajiya Maimuna sai ya bar zancen haka.
Bayan tafiyarsu Jafar ya fice daga gidan bai dawo ba sai goman dare. Gidan yayi masa fad'i,ya amince cewar ko yaya mutum yake toh tabbas rahma ne. Yanzu da babu Siyama duk sai yaji babu dad'i. Daidai lokacin ne ya kunna wayarsa daya mik'a wurin chaji d'azu bayan fitarsa. Sak'onnin Hadiyya har biyu ne suka shigo. D'aya gaisuwa ce da tambayar ko lafiya ta bugo taji wayarsa a kashe,dayan kuwa gaisuwar juma'a ce. Murmushi yayi,shima fa yayi kewar kanwar nan tasa. Babu wata wata ya danna mata kira.
Ladi dake kwance ta kasa bacci saboda damuwar rashin jin Jafar gashi yau juma'a basuje kasuwa ba bata sanyashi a ido ba. Wayarta ta soma vibrating, taga shi d'inne kuwa. Tayi mamakin ganin kiransa,ta dubi Mama dake bacci ta mike sad'af sad'af zuwa d'ayan d'akinsu dake a matsayin falo.
"Assalamu alaikum,ba dai kin soma bacci ba deeya?"
Tayi murmushi mai sauti
"Wa'alaikassalam yaya j,idanuna biyu ina tunanin meke faruwa dakai na kira bata shiga ba. Gashi yanzu kuma nasan ka koma cikin iyalinka ko?"
Ta k'arasa cikin sanyin murya,maganar ta shigeshi. Yasan hadiyya tana da zak'in murya,saidai jin na yanzun yake kamar yafi na koyaushe. A hankali ya lumshe idanuwansa
"Iyalina bata nan,kinsan ta shiga watan haihuwarta. Al'adar bahaushe yasa aka daukemin mata,har sai ta haihu tayi arba'in."
Ladi ta sanya dariya mai had'e da farin ciki,tace
"Ashe kuwa kwana biyu yaya j zakayi kewa. Na tausaya maka,sorry."
Yayi murmushi,
"Zanyi maganinki,gwarani. Keda ko samarin baki dasu?"
Ta lumshe ido ta bud'e
"Haba,gaka nan."
Ta fad'a a hankali,ya gyara zamanshi akan gado
"Banji ba?"
Tayi dariya
"Tunda ina da yaya j ai shikenan,idan lokacin auren yazo sai na bawa ko waye damar fitowa."
"Kina nufin bazakiyi auren soyayya ba?"
Cikin damuwa tace
"Da wuya na samu wanda nakeso. Yaya j nifa ba 'yar kowa bace, ba wani kyau ne dani ba. Shi kuma wannan da nakeso ya keremin ta ko'ina,baisan ma ina sonshi ba sannan yana da matarsa kana ganin zai aureni ne?"
Zuciyarsa ta soma zargin wani abu, shi kansa ya kasa tantance abunda yakeji akanta. Yasan bai wuce shak'uwarsu ba,amma meyasa yakejin wani abu a kanta ne? Ya daure yace
"Waye wannan deeya? Na tabbata ko waye yana sonki. Deeya halayenki suna dakyau,ko kadan a yanzu ba a fiye auren kyau ba. Domin babu abunda aka fi tsinta sai munanan d'abi'u masu farraka ma'auratan da matsaloli daban daban. Kada ki yarda duk runtsi kiyi auren da babu soyayya Deeya,matukar kikayi hakan,zaki iya yin dana sani marar misaltuwa."
Kwallah ta cika idonta
"Kana nufin kowaye bazai gujeni ba yaya j?"
"Kwarai kuwa."
"Koda ya kasance kaine wannan mutumin?"
Dam qirginshi yabuga da qarfi.!.........
Please like Us On   Facebook
Follow us on   Twitter


Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 14:15
In Hausa Novels
Kazamar Gida Part 9 Title : Kazamar Gida Part 9
Description : Ranaku suna ta ja har Allah Ya kawo ranar da aka yaye su Ladi daga sakandire. Yan uwan mahaifinta sun zo tayata murna. Ranar tayi murna ma...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kazamar Gida Part 9"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2026 (2)
    • ►  June (1)
    • ►  January (1)
  • ►  2025 (5)
    • ►  December (5)
  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ▼  November (308)
      • Kafin Kayi Barci
      • Yanda Ake Hada Lemon Juice
      • Yan Boko Haram Sun Sace Wasu Mata A Banburaitai
      • Photos: Buhari Ya Isaa Paris Dan Halartar Taron Sa...
      • Ana Ta Samun Nasarar Kwato Shanun Sata a Kano
      • Zargin Kinshiyoyin Ta Sun Mata Asiri
      • Al'ajabi Part 16
      • Hisbah Ta Kama Wani Dan Sanda Da Yi Wa Budurwa Ciki
      • An kaiwa 'yan Shi'a hari a Masallaci a Bangaladash
      • Video: Download Highlight Leicester City 1 Manches...
      • Video: Download Highlight Barcelona 4 Real Sociedad 0
      • Yanda Ake Hada Cake
      • Photos: Yusuf da Zahra Buhari Su Halarci Taron Yay...
      • Photos: Sabin Hotuna Shahida Sanusi Lamido Sunusi
      • Buhari Ya Nada Sabun Alkalai
      • Al'ajabi Paart 15
      • Yan Boko Haram Na Shirin Kaima Abuja Hari
      • Mummunar Shiga Mai Bayyana Tsaraici Da Yan Uwa Mat...
      • New Music: Inda Rai Darabo By Hussaini Danko
      • Graphic Photos :Adadin Mutanen Da Su Ka Rasu A Har...
      • Photos: Gwamna Jihar Bauchi Ya Ziyarci Atiku Abubakar
      • Graphic Photos:Yanayi Wanda Ya Kai Hari Yau A Jiha...
      • Tafsir: Rikicin Duniya Da Na Lahira By Sheikh Isa ...
      • Hanyoyin 25 Masu Sauki Domin Samun Lada Mai Yawa
      • New Music: Kana Raina By Hussaini Danko
      • Bom Ya Tashi Dan Yan Shi'a 15 A Kano
      • Photos: Buhari Ya Gana Da Sarauniyar Ingila A Malta
      • Tafsir: Tambayoyi Tara Bayan Mutuwa By Sheikh Isa ...
      • Graphic Photos: Wani Dalibi Poly Ya Kashe Kansa
      • Buhari Na Neman Jefa Kasar Nan Cikin Mummunan Hali...
      • Yadda Wani Attajiri Ya Yi Wa Kansa Yankan Rago A J...
      • New Film: Zurfin Ciki 2015 Part 2 Starring Ali Nuhu
      • Yan Najeriya Sun Nuna Bacin Ransu Da Buhari
      • Dan Marigayi Audu Abubakar Ne Zai Maye Gurbin Sa A...
      • Kotu Ta Hana Wata Ma'aikaciya Sanya Hijab A Faransa
      • Photos: Buhari Yabar Najeriya Zuwa Malta
      • Photos: An Kaddamar Da Sarkin Kano Mastayi Sabon C...
      • Photos: Gwamna Jihar Nasarawa Ya Kwanta Akan Katif...
      • Nafisah Abdullahi Tayi Allah Wadai Da Matan Da Ke ...
      • Photos: Happy Birthday Haleema Atete, Ga Sabin Hot...
      • New Film : Zurfin Ciki 2015 Part 1 Starring Ali Nu...
      • An Haramta Yi Wa Mata Kaciya A Gambia
      • Magajin Garin Kano Ya Rasu
      • Photos:Buhari,Osinbajo, Saraki, Tinubu Da Amaechi ...
      • Video: Manchester United 0 PSV 0
      • Video: Shakhtar Donesk 3 Real Madrid 4
      • Yanda Ake farfesun kifi
      • Yanda Ake Karya Sihiri Da Lalata Sharrin Aljanu
      • Photos: Buhari Ya Halarci Wajen Binne Matan Awolowo
      • Za A Fara Kama Masu Boye Fetur A Najeriya
      • Abu Ashirin Da Mata Ke So
      • Macen da Aljanna ta fi Karfin ta
      • New Music: Nayi Kira By Hussaini Danko
      • New Music : Kira Nake by Hussaini Danko
      • Yanda Ake Hada Kunu Aya
      • Al'ajabi Part 11
      • Paparoma zai je Kenya
      • An gano wata jigidar bama-bamai a Paris
      • Bangladesh ta haramta amfani da Facebook saboda Tsaro
      • Graphic Photos: Abunda Kishiyarta Ta Mata Ranar Am...
      • Hanyoyin 15 Da Zaka Bi Domin Gujewa Aikata Zinna
      • Al'ajabi Part 13
      • Al'ajabi Part 12
      • Video: Barcelona 6 Roma 1
      • Video: Arsenal 3 Dinamo Zagreb 0
      • Video: Maccabi Tel-Aviv 0-4 Chelsea
      • Photos: An Ba wa 2face Sarauta A Kaduna
      • Buhari Ya Bada Sakon Ta’aziyya Ga Iyalan Audu
      • APC Za Ta Tsayar Da Sabon Dan takara
      • New Music: Mafita By Hussaini Danko
      • New Music: Rabin Mutum By Hussaini Danko
      • Al'ajabi Part 14
      • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
      • Graphic Photos: Wata Yarinya Tana Bukatar Taimako ...
      • Hakurin Zama Da Mace Mara Biyayya
      • Photos: Aisha Buhari A Offishin FIRST LADY
      • Photos: Major AL Ayangbesan, Soja Najeriya Wanda B...
      • Boko Haram, ISIS, Al-Qaeda Na Shirin Kai Hari — Am...
      • Photos: Sabin Hotuna Iyalan Marigayi Sani Abacha
      • New Music: Shakuwa By Hussaini Danko
      • Photos: Buhari Ya Halarci Taron Kasashen Masu Arzi...
      • An rataye 'yan adawa biyu a kasar Bangladesh
      • Darussa Bakwai Game Da Rasuwar Dan Takarar Gwamna...
      • Photos: Isar Buhari Iran
      • Abunda Dokar Zabe Tace Akan Mutuwar Audu
      • An yi jana'izar Abubakar Audu
      • Mutane 8 sun mutu a harin Maiduguri
      • Film: Download Hausa Shargalle Part 2 Starring Sul...
      • Photos: Adama Indimi A Sabon Hotuna
      • New Music: Sirrina By Hussaini Danko
      • Photos: Ali Artwork Ya Ziyarci Rahma Sadau
      • Prince Abubakar Audu Dan Takara Gwamna Jihar kogi ...
      • An Kai Hari A Garin Kauye Mafe Dake Borno
      • Photos: Buhari Yabar Najeriya Zuwa Iran
      • Photo; Aisha Buhari, Ambode Da Bola Tinubu Wajen W...
      • Film: Download Hausa Film Shargalle Part 1
      • Al'ajabi Part 10
      • List: Makarantu Sakandare Da Suka Fi Kowani Makara...
      • Photo: Buhari Tare Da Tsohon Direban Sa Da Yar sa
      • Music: SO by Hussaini Danko
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Bola Tinubu
      • Video: Real Madrid 0 Barcelona 4
      • Boko Haram Sun Kai Hari A Jihar Port Harcourt
      • VIDEO: Chelsea 1-0 Norwich City
      • [Video] Watford 1 Manchester United 2
      • Al'ajabi Part 9
      • HUKUNCIN SHIMFIDAR DA AKAYI JIMA'I AKANTA
      • Yan Bindiga Sun Sace Shanu 1,500 a Borno
      • An kafa dokar ta baci ta kwanaki 10 a Mali
      • Saurayi ya yi wa tsohuwa ciki ba tare da aure ba
      • Magidanci ya yi wa ’ya’yansa 4 yankan rago a Kaduna
      • [Mu Sha Dariya] Wani Gaye Yaje Interview
      • [Graphic Photos] ISIS Sun Yi Wa Mutane Biyar Hukunci
      • [Photos] Goodluck Jonathan Ya Dawo Daga Amurka
      • Wani yaro ya kamu da Ebola a Liberia
      • Magoya Bayan Jonathan Ne Ke Zanga Zangar Biafra
      • Yanda Ake Hada Rice And Peac
      • [Tafsir] Download Mazinaciya Jakar Gayu - Sheik Ah...
      • Hukumar Soji Ta Tabbatar Da Bacewar Mutanen Ta
      • Wacece Mace Ta Gari
      • Gwamnonin Najeriya Baza su Iya Biyan Albashi 18000
      • An Kai Hari A Bamako
      • Al'ajabi 8
      • Yanda Ake Hada Danbun Shinkafa
      • [Photos] Wani Matashi Ya Kashe Kansa Dan Talauci A...
      • [Photos] Ya'yan Sani Abacha
      • Buhari Ya Sha Alwashin Murkushe 'Yan ta'adda
      • Bama-Bamai Biyu Sun Tashi A Kasuwar Waya A Kano
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...
  • MAGANIN KARYA SIHIRI DA IZININ ALLAH
    TAMBAYA TA 1606 ********************* Assalamu alaikum, Malam barka da aiki ya hidima da mutane Allah ya saka muku da mafificin alkairi. ...
  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Rikicin Rarara da Naziru Sarkin Waka Ya Ƙare? Naziru Ya Taya Rarara Murn...
  • Kannywood Director Iliya Tantiri involve in a car Accident
    the accident happen on his way to Kaduna. the car was burnt but the Director was fine
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Zanga-zanga A Bauchi-Gwamnatin Ta Saka Dokar Hana Fita Da Zirga-Zirga Ac...
  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger