1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Arewa » Tsohon kwarto na kokarin kwace ’ya’yan mijin tsohuwar farkarsa

Tsohon kwarto na kokarin kwace ’ya’yan mijin tsohuwar farkarsa

By Abdul Mk
Add Comment
Saturday, 26 September 2015
Wani magidanci mai suna Malam Muhammad Sani Najume da ke zaune a Federal Low Cost da ke yankin Usubu a garin Kwantagora ta Jihar Neja ya kai karar wani ma’aikacin asibiti mai suna Mista Kayode Adeyemi Stephen kan zarginsa da lalata da matarsa mai suna Suwaiba Aliyu Aski a lokuta da dama tare da kokarin kwace masa ’ya’yansa tagwaye biyu, bayan ya samu nasarar raba ta da shi.
Malam Muhammad Sani Najume wanda ma’aikacin gwamnatin Neja ne mai shekara 42, ya kai karar Adeyemi da surukinsa Alhaji Ibrahim danjuma Sarkin Aski bisa zarginsa da assasa badakalar da ta sa Mista Adeyemi ya yi ta lalata da matarsa a Kotun Shari’ar Musulunci da ke Unguwar Usubu a Kwantagora ne tun a ranar 22 ga watan Janairun bara, bayan da Mista Adeyemi ya yi ikirarin cewa ’yan biyun da matar ta haifar wa Najume masu suna Hassan da Husaini ’ya’yansa ne.
Najume ya shaida wa wakilinmu cewa, Malam Ada na Unguwar Yamma mijin mahaifiyarsa Hajiya A’i ne ya sanar da shi cewa Alhaji Gambara ya sanar da shi cewa “Matata Suwaiba Aliyu Aski da Mista Kayode Adeyemi Stephen sun samu Alhaji Adamu Mai Fatar Kada a gida sun bayyana masa cewa sun share shekara uku suna zina har ma ya yi ikirarin cewa cikin da matata ke dauke da shi ba nawa ba ne, nasa ne,” inji Najume.
Ya ce Mista Kayode, ya yi ikirarin kashe makudan kudi a kan matarsa inda duk wata yakan yi wa iyayenta hidima da suka hada da ba surukinsa Naira dubu 30 da buhun shinkafa da doya. Bayan haka, shi yake biyan kudin makarantar kanenta da wasu abubuwan da ba za a rasa ba.
Ya ce Alhaji danjuma ya tabbatar wa Alhaji Mai Fatar Kada cewa muddin Mista Kayode zai musulunta, shi kuma zai ba shi auren ’yarsa Suwaiba duk da cewa a lokacin suna da aure.
Sani Najume ya ce, “Bayan da na ji wannan jawabin, sai na kira surukina Alhaji danjuma Aski zuwa gidana da ke Federal Low-Cost domin ya tabbatar mini da gaskiyar maganar. Sai na je tare da dan uwanta Tijjani Sa’idu da daha da ’yar uwar mahaifiyarta Mama Larai Rafin Gora. Da muka hadu ne surukina ya sanar da ni cewa ba abin da ya samu aurena da matata, kuma cikin da take dauke da shi nawa ne. Idan ina son karin bayani in tambayi kowane malamin Musulunci da na sani.”
Ya ce bayan zaman ne ya samu Alhaji Adamu Mai Fatar Kada kan abin da ya faru, sai ya ka da baki ya ce masa ba abin da zai ce sai ya je da Alhaji danjuma da Alhaji Gambara da daha. 
Ya ce Mista Kayode ya yi hayar wani lauya mai suna Barista M.B. Shehu wanda ya je kotu domin a kashe aurensa da matarsa, bayan yana da masaniyar cewa na shigar da shi da matata da surukina kara domin bi masa hakkinsa. 
Mista Kayode Adeyemi mai shekara 43 da ke aiki a Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Neja kuma aka tura shi garin Bangi a jawabin da ya yi wa ’yan sanda ya ce yana da mata mai suna Suwaiba Aliyu da ’ya’ya biyu masu suna Hassan da Hussaini kuma ya tabbatar da auren matarsa a ranar 9 ga watan Maris na bana, wanda hakan ya halalta masa ’ya’yan da yake ikirarin nasa ne.
Mista Kayode Adeyemi ya ce a shekarar 2012 ne bayan ya taso daga aiki a Babban Asibitin Kwantagora yana hanyar zuwa gida, ya hangi Suwaiba inda ya tsaya a mota domin rage mata hanya amma ta ki, sai ta tsayar da dan acaba, ya biya mata kudin da za a kai ta gida, kafin su rabu a wurin sun yi musayar lambobin waya.
Ya ce, “Bayan wata uku sai muka hadu a Babban Asibitin Kwantagora tare da wata. A nan na tambaye ta ina mahaifinta? Sai ta kwashe labarin abin da ya faru tsakaninta da mijinta inda ta nuna ya yi watsi da ita kuma ba ya kwanan aure da ita tun farkon shekarar 2012.”
Mista Kayode Adeyemi ya ce a shekarar 2013 ne shi da Suwaiba suka je wurin Baba Mai Fatar Kada a Unguwar Tudun Wada inda ta sanar da shi cewa babu aure tsakaninta da mijinta Sani Najume, saboda ya yi mata saki fiye da sau uku. Da ta gama yi masa bayani, bai ce komai ba, ya ce sai bayan ta haihu.
Ya ce a shekarar 2014 Sani Najume ya shigar da kara Kotun Majistare ta Kwantagora yana zarginsa da jan  hankalin matarsa, sai  dai lauyoyin Mista Kayode da na Sani sun nuna wa kotun za a sasanta lamarin cikin ruwan sanyi inda aka nemi ya biya Naira dubu 350 shi kuma ya kasa biyan kudin daga baya.
Kayode ya ce a ranar 9 ga Maris na bana aka daura musu aure da Suwaiba bayan da ya Musulunta. Kuma a wannan ranar Malam Sani Najume ya shigar da kara kotu bisa dalilin kin biyan kudin da suka nema a wurinsa. Sai dai ya ce kafin ya aure ta sai da ya tabbatar ta gabatar masa da takardar sakin da Najume ya yi mata, a Kotun Shari’ar Musulunci. 
Ita kuwa Suwaiba Aliyu Aski ta shaida wa ’yan sanda cewa suna da ’ya’ya uku ne da tsohon mijinta Najume da suka hada da Sulaiman da Rahinatu da kuma Muhammad Sani. Ta ce a watan Janairun shekarar 2009 ne ya ba ta takardar sakin da ba ta tuna inda ta ajiye ta ba. Sannan ya yi wani sakin a watan Disamban shekarar 2013, inda ta ce tana da shaidun da suka hada da Alhaji Na-Jummai da Maryam da Hajiya A’i game da lamarin.
Suwaiba Aliyu Aski ta ce, “Lokacin da ya yi sakin a shekarar 2013 ya ki ba ni takarda. Da na nemi haka,sai ya ce ba shi ba ne zai rubuta mini da hannunsa ba. Jin haka ne ya sa na je Kotun Shari’ar Musulunci domin ta kawo karshen aure tsakanina da tsohon mijina Muhammad Sani.”
Ta ce sun taba zuwa wurin Mai Fata domin shaida masa cewa Mista Kayode ya yi mata ciki wanda ya yi sanadiyyar haihuwar ’yan biyun da suka hada da Hassan da Hussaini, kuma ba ta san dalilin da ya sa yake gudun cikin ba. Dalili kuwa daga shekarar 2012 suka fara soyayyya da Kayode da har ya kai suke lalata a tsakanisu a duk lokacin da ta je gidansa. 
Suwaiba ta ce, “Mista Kayode ya Musulunta a watan Fabrairun bana, kuma ranar 9 ga Maris, bayan na biya Muhammad Sani sadakinsa Naira 172 da sauran kudin da ya nema. Shaidana shi ne Tijjani Sarkin Aski. Kafin a kai ga wannan matakin sai da na tabbatar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kwantagora ta raba aurenmu da tsohon mijina.”
Alhaji danjuma Aski mai shekara 55 ya shaida wa ’yan sanda cewa a ranar 16 ga watan Maris na bana da misalin karfe 2:40, surukinsa ya kai shi kara kotun da ta ba ’yan sanda umurnin gudanar da bincike game da lamarin inda ya zarge shi da hannu wurin ba wani ’yarsa (matar mai kara) ana lalata da ita alhalin tana da aure. “Ba yadda za a yi in aikata irin wannan danyen aikin da addini bai yarda da shi ba ko kadan,” inji shi.  
Surukin ya ce ya sha sasanta tsakanin surkinsa da ’yarsa daga bisani Suwaiba ta shaida masa cewa Sani ya sha furta mata kalaman saki, kuma daga bisani ta shigar da kara a Kotun Shari’ar Musulunci ranar 10 ga watan Satumban bara. 
Muhamma Sani Najume da yake kukan ana kokarin kwace masa ‘ya’ya



Wakilinmu wanda ya ziyarci Kwantagora ya samu takardar da Kotun Shari’ar Musulunci ta tabbatar da kawo karshen aure a tsakanin Muhammad Sani da Suwaiba Aliyu Aski ranar 10 ga watan Satumban bara. Wannan ne ya ba Suwaiba damar fara iddar daga ranar da ta amsa ta kammala sannan ta auri Mista Kayode.
Ganin Mista Kayode Adeyemi wanda yanzu ya musulunta kuma yake amsa sunan Kasim yana ikirarin cewa shi ya yi wa Suwaiba cikin da ta haifi ’yan biyu masu sunan Hassan da Hussaini ne ya sa Muhammad Sani ya garzaya Kotun Musulunci domin ta kwato masa ’ya’yan da ya yi ikirarin cewa nasa domin tsohuwar matarsa ta haife su a gidansa, kuma da suka cika mako daya ya yi musu zanen suna tare da yanka musu hakika yadda addinin Musulunci ya bukata.
Muhammad Sani ya ce zai bi duk hanyoyin da shari’a ta tanada domin karbo ’ya’yansa, inda ya ce ya tanadi shaidun da zai gabatar a gaban Kotun domin kawar da shakkun cewa shi ne mahaifinsu.
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 10:21
In Arewa
Tsohon kwarto na kokarin kwace ’ya’yan mijin tsohuwar farkarsa Title : Tsohon kwarto na kokarin kwace ’ya’yan mijin tsohuwar farkarsa
Description : Wani magidanci mai suna Malam Muhammad Sani Najume da ke zaune a Federal Low Cost da ke yankin Usubu a garin Kwantagora ta Jihar Neja ya ka...
Rating : 5
Related Posts: Arewa

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Tsohon kwarto na kokarin kwace ’ya’yan mijin tsohuwar farkarsa"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ▼  September (198)
      • Ashe Kaine Mijina Part 12
      • Rijiyoyin Azabar Jahannama
      • Ba mu fitar da rai kan Kofin Turai ba — Wenger
      • Yan Boko Haram na zuba guba a ruwa
      • Buhari ya aika sunayen ministoci majalisa
      • Google ya fitar da samfurin mota mara matuki da za...
      • Jiragen saman Isra'ila sun kai hare-hare a Gaza
      • HANYOYI 10 DA ZAKA RAGEWA ANDROID PHONE JAN CAJI D...
      • [Video] Download Highlight Arsenal 2 Olympiacos 3
      • [Video] Download Highlight Porto 2 Chelsea 1
      • [Video] Download Highlight Barcelona 2 Bayern leve...
      • Buhari Ya Hadu Da Cameron
      • Yadda zaka Gyara layinka idan ya daina tura sakon ...
      • Alhazai fiye da 1000 ne suka rasu a Mina
      • Kawancen Boko Haram da IS ba alheri ba ne'
      • Tsokaci AKan Sallar Bana
      • Yanda Zaka dawo da Android zuwa modern
      • [Photos] Buhari Ya Gana Da Sarkin Jordan
      • Fareesah Part 1
      • Abincin Zuciya
      • Makaho Mai Ayukan Irin Na masu Ido
      • Idan Matarka Ta Bata Maka Rai
      • Kungiyar Yarrabawa Ta Gargadi Buhari Akan Saraki
      • Isra'ila na ci gaba da zaluntar Falasdinawa a Bait...
      • Gareth Bale Ya Dawo Baya Jinya
      • Boko Haram ta kai hari a yankin Askira Uba
      • [Photos] Behind The Scene Photos of ANA WATA GA WA...
      • NNPC: Za a gurfanar da masu almubazzaranci-Buhari
      • Nijar ta ware kwanakin juyayin mutuwar Alhazai
      • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Tara A Borno
      • Ranar Laraba Buhari Zai Mikawa Majalisar Dattawa S...
      • Kasar Faransa Ta Kai Hari Kan Sansanin ‘yan Ta’ada...
      • An tabbatar da rasuwar alhazan Nigeria 54
      • [Photos] Buhari Ya Gana Da Shugaban Kasan Korea
      • sakamakon wasannin mako na gida nigeria da aka yi:
      • Ashe Kaine Mijina Part 10
      • Ashe Kaine Mijina Part 9
      • Ronaldo ya yi takaici da bai ci kwallo ba
      • [Video] Download Kannywood Film Zee Zee
      • Alhazai 16 na jihohi uku sun jikkata
      • MESSi ya samu Mummunar Rauni
      • [Video] Download Highlight Tottenham 4 Manchester ...
      • [Video] Download Highlight Leicester City 2-5 Arsenal
      • [Video] Download Highlight Manchester United 3 Sun...
      • [Video] Download Highlight Barcelona 2 La Pasma 1
      • [Video] Download Highlight Real Madrid 0 Malaga 0
      • [Video] Download Highlight Newcastle 2 Chelsea 2
      • An kai hari a ofishin SSS a Lokoja
      • Sarkin Kano Ya Auri Yar Lamido Adamawa Aboye
      • Ashe Kaine Mijina Part 8
      • LEWANDOWSKI ya sake kafa tarihi
      • Manchester United ta doke Sunderland 3-0
      • Newcastle da Chelsea sun tashi wasa 2-2
      • Tottenham ta ci Manchester City 4-1
      • An Rabawa Iyalan Rabilu Musa Ibro Gado
      • An kama Yarima Saudiyya Da Niyan Yin Fyade A Amurka
      • [Photos] Shin Zaka Iya Siyan Wanna Suwaita Akan Ku...
      • Sarkin Zang Na Taraba Ya Rasu Makka
      • Makaho mai koyar da masu ido karatu
      • [Fasaha] Yanda Zaka haɗa Wayan Android Da kwamfuta...
      • Girgizar kasa ta afku a Indonesiya
      • Kukan Kurciya Jawabi ne
      • [Photos/Nishadi] Abinda Ya Dace Da Kwarto Kenan
      • [Download Tafsir] Hukuncin Sallan idi da Layya da ...
      • WASANNI: An Zura Kwallaye 644 A Gasar Firimiyar Ni...
      • BUHARI Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Suka Rasa Rayuk...
      • Ingila za ta rasa gurbi daya a gasar zakarun Turai
      • Neymar ya tattauna' da Manchester United
      • Tsohon kwarto na kokarin kwace ’ya’yan mijin tsohu...
      • [Photos]Buhari Ya Gana Da Manya Shugabanin Duniya
      • Ashe Kaine Miji Na Part 7
      • Iska Mai Fita Ta Gaban Mace
      • Za a cire Nigeria cikin jerin kasashe masu Polio
      • Mourinho Ya Yiwa Wenger Hannunka Mai Sanda
      • Fifa: An soma bincike kan Blatter
      • A Daina Dora Alhaki A Kan Mahajjata - Sarkin Kano
      • 'Yan Boko Haram 200 sun mika wuya
      • Gwamnatin Saudiyya ta kare kanta
      • [Photos] Bukola Saraki A Sinima
      • [Fasaha] Yanda Zaka Dakatar Da Wani Daga Kira ka
      • Duniya Za Ruguje
      • Sojojin Nigeria sun kwato garin Banki
      • 'Da akwai 'yan Nigeria da Niger cikin wadanda suka...
      • [Photos Evidence] Mummunar Tafiya Jami'an Tsaron K...
      • Saudiyya : Sarki Salman Ya Bukaci A Gaggauta Binci...
      • Labarin Wani Sarki Da Bafadensa
      • Yana Mafarkin Wata Mata
      • Ashe Kaine Miji Na Part 6
      • Layya Tana Da Sharadan Ingaci Gudu Biyar
      • Yayin da Musulmai ke bikin babbar Sallah an kai ha...
      • 'Kwanan Boko Haram ya kusa karewa'
      • An jefi Bukola Saraki a filin Idi
      • Sama Da Mutane 300 sun rasu a aikin Hajji Yau
      • Hukunce Hukuncen Layya
      • Shin Ya Halartar Mata Su Tafi Wajen Sallar Eidi
      • Shugaban Najeriya zai halarci taron MDD a Amurka
      • An saki ‘mai tsaron lаfiуаr’ Oѕаmа Bin Lаdеn
      • Yau Take Sallah
      • Hukunci Alhajin Da Ya Sadu Da Matarsa Kafin Arfa
      • Michel Kafando Ya Koma Kan Mulki A Burkina Faso
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger