1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Al'ajabi » Arewa » Makaho mai koyar da masu ido karatu

Makaho mai koyar da masu ido karatu

By Abdul Mk
Add Comment
Saturday, 26 September 2015
Malam Yusha'u Ibrahim

Malam Yusha’u Ibrahim kofar Waika, malami ne da ke koyar da masu ido a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi a Kano, duk da cewa yana da damuwar rashin gani amma hakan bai hana shi neman ilimi ba, inda har ya kai ga samun digiri na biyu, don haka yake ganin babu wani abu da zai gagari mai bukata ta musmaman matukar mutum yana numfashi. A  tattaunawarsa da Aminiya ya yi kira da a samar da dokar da za ta ware wani kaso ga masu bukata ta musamamn a dukkanin ma’aikatun gwamnati da sauran abubuwa. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so jin takaitaccen tarihin rayuwarka?
Yusha’u: An haife ni a unguwar Chediyar ‘yan, gurasa cikin Birnin Kano. Na fara yin karatuna na firamare a makarantar Firamare ta Malam Aminu Kano da ke Sudawa. Wata rana da aka yi hutu a shekarar 1979 sai na yi rashin lafiya inda na yi kyanda bayan na warke sai na rasa gani. Hakan ya sa bayan mun koma hutu sai wasu malamaina suka shawarci mahaifina da ya kai ni makarantar masu bukata ta musamman da ke Tudun Maliki. Jin cewa makarantar ta kwana ce sai mahaifina ya ki amincewa, sai dai bai bayyana musu dalilinsa na hakika ba, inda ya ce musu mahaifiyata ce ba ta amince ba.
 Ana cikin haka sai Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa. To daga baya sai mahaifiyata ta sa aka sanya ni makarantar Tudun Maliki inda na fara daga firamre aji daya. Bayan na gama firamare da karamar sakandire sai na shiga makarantar babbar sakandare ta Wudil. Muna wannan makaranta sai gwamnatin Jihar ta rushe makarantar. Daga nan aka mayar da ni Makarantar Horon Malamai ta Kano. Ina wannan makaranta saboda yanayin da nake ciki sai ya zama ina makara wajen zuwa makarantar, don haka na nemi canji aka mayar da ni makarantar Horon malamai ta Minjibir wacce ta kasance ta kwana ce. Anan na kammala sakandare dina a shekarar 1993.
Bayan na kammala sai na fara neman aiki, a shekarar sai na nemi aiki na fara koyarwa a karkashin  ma’aikatar ilimi ta karamar Hukumar Dala. Daga baya sai na ga ya kamata na koma makaranta sai na sayi fom din Kwalejin Ilimi ta gwamnatin Tarayya da ke Kano. Amma sai suka ce su ba su taba koyar da dalibai marasa gani ba, to da yake mu biyu ne muka nema sai suka dauki wancan bisa sharadin za su gwada idan ya yi kokari to ni ma za su dauke ni. Allah cikin ikonsa wanan dalibin ya gama cikin nasara, don haka suka dauke ni, inda na kammala karatuna a 2003.
Bayan na koma na ci gaba da aiki, a shekarar 2005 sai na koma makaranta, inda na yi digiri a bangaren Special Education,  inda na kammala a shekarar 2008. A shekarar 2009 sai na ga akwai bukatar in karo karatu, inda na yi digiri na biyu a bangaren Special Education.
Ina nan ina koyarwa a makarantar firamare sai na ji ina son in ci gaba da aikin koyarwa amma a manyan makarantu, don haka sai na nemi aiki a Kwalejin ilimi ta Tarayya (FCE) Kano, sai dai ban samu ba. Lokacin da gwamnatin Jihar Kano ta tashi daukar malami a manyan makarantun jihar sai na nama, nan ma dai ban samu ba. Da za a sake dauka sai na ce ba zan nema ba, amma sai wani abokina da muka yi karatu da shi ya karfafe ni da in nema, don haka na sake nema, inda kuma Allah Ya sa na dace  aka dauke ni a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi a shekarar 2014.
Aminiya: Kasancewar duk da damuwar rashin ganida kake da ita, amma ga shi har ka yi digiri na biyu kana kuma koyarwa a  daya daga cikin makarantun Jihar Knao, mene ne sirrin hakan?
Yusha’u: Ba wani siriri ba ne da ya wuce yarda da kai. Har kullum ina ganin cewa zan iya yin duk wani abu da mai ido zai yi, matukar ba nuna shi za a yi ba. A ganina nakasa ba a ta hana mutum kai wa ga cikar burinsa na rayuwa ba.
Muna da rubutu iri biyu. Na farko shi ne wanda muke zanawa da hannu, wanda ake kira brai,l sai wanda ya iya shi ne zai iya karantawa. A lokacin da nake karatu na fi yin amfani da brail wajen rubuta lacca, amma idan zan bai wa dalibai na kan buga da kwanfuta.
Babu shakka a lokacin da nake karatu na yi karo da matsaloli da dama, amma kuma hakan bai hana na ci gaba da neman ilimi ba har Allah Ya sa na samu cikar burina. Abin da ya sa ba na damuwa shi ne gani na yi masu idon ma haka suke fama da matsaloli ballantana marasa shi.
Tun farko ni mutum ne mai sha’awar aikin koyarwa, hakan ya sa duk karatun da na yi a bangaren koyarwa na yi shi, tun daga sakandire har digiri na biyu.
A ganina nakasa ba zai zama hujja ga mutum ya ki neman abin da yake so a rayuwa ba. Mutane na mamakin yadda nake koyarwa. Ina ganin in har zan iya koyarwa a matakin firamare wanda yake bukatar sai malami  ya zaga aji don tabbatarwa.  Ina ganin babu dangantaka tsakanin bara da nakasa.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati wajen ganin ta inganta rayuwar musu bukata ta musamman?
 Yusha’u: Ina kira ga gwamtani da ta samar da makarantu don masu bukata ta musamamn, kasancewar har yanzu makaranta guda daya ce rak a Kano, wato ta Tudun Malili. Idan kin duba wannan makaranta an yi ta ne a shekarar 1979 , amma tun daga wannan lokaci ba a sake yin wata ba.
Haka kuma akwai bukatar a samar da kayan aiki ga makarantun, domin har yanzu babu kwamfutoci na musamman a makarantar Tudun Malikin ma.
Bincike ya nuna cewa masu bukata ta musamman suna daukar kashi 40 na al’ummar jihar, amma idan ka duba babu wani abu da ake musu na a-zo-a-gani. A Najeriya damar da ke ga masu bukata ta musamman takaitattu ne, saboda ba a ba su ilimi ba ballantana a dauke su aiki. Idan ka bai wa mutum ilimi ka ba shi kashi 90 na rayuwarsa.
Su ma ‘yan majalisa ina kira gare su da su samar da wata doka da za ta kula da muradun masu bukata ta musamman. Misali, ya zama cewa dukkaknin ma’aikatu da hukumomin gwanmati an ware wasu guraben aiki ga masu bukata ta musamman.
Ina tunatar da duk wani zababbe da ke kan wata kujera ya tuna cewa da kuri’ar masu bukata ta musanmman ya samu kai wa ga wannan matsayi, don haka sai ya yi tunanin me zai iya yi musu a matsayinsu na wadanda suka zabe shi.
Ba zan manta  da lokacin Gwamnan Kano Kanar Idris Garba ba, wanda ya tabbatar cewa a mai’aikatu da kamfanonin da ba na gwamnati ba dole sai an ware wani kaso ga masu bukata ta musamman kamar yadda aka yi tanadi a majalisar dinmin Duniya. To Idan har wanda ba ka zaba ba zai yi maka irin wanann tagomashin, to ina ga wanda ka zaba. Don haka na kalubalanci duk wani zabababen shugaba tun daga sama har kasa, su zauna su yi tunani mai suka yi wa masu bukata ta musamman. Ina kira da a samar da daidaito tsakanin masu bukata ta musamman da sauran jama’a ta kowace fuska.
Haka kuma ina kira ga sauran jama’a masu hannu da shuni da su shigo wajen karfafa gwiwar masu bukata ta musamman, musamman ta fuskar ilimi. Ba zan mance yadda wani attajiri lokacin muna karatu a Jami’ar Bayero ya bayar da makudan kudi don rabawa ga dalibai masu bukata ta musamman ba.
Haka kuma duk da cewa bara ba abu ne mai kyau ba, amma bai kamata a hana ta ba, bayan ba a samar wa mutum wani abu da zai rika yi don sama wa kansa abin kai wa bakin salati ba. Ita kanta barar ai tana nuna gazawar gwamnati ce a fili. A kasar nan babu kabilar da a  cikinta babu masu bukata ta musamman, amma bahaushe ne kawai ke yin bara, saboda gwamnatinsa ba ta ba shi kulawar da ta dace.
Ina ganin sai mutum ya samu ilimi sannan cikin hikima zai fahimci me ya kamata ya yi a rayuwarsa, don haka masu bukata ta musamamn suna bukatar ilimi. Haka kuma wadand suke manya a samar musu wurin horarwa ta sana’a ta yadda za su dogara da kansu.
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 17:30
In Al'ajabi, Arewa
Makaho mai koyar da masu ido karatu Title : Makaho mai koyar da masu ido karatu
Description : Malam Yusha'u Ibrahim Malam Yusha’u Ibrahim kofar Waika, malami ne da ke koyar da masu ido a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi a K...
Rating : 5
Related Posts: Al'ajabi, Arewa

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Makaho mai koyar da masu ido karatu"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ▼  September (198)
      • Ashe Kaine Mijina Part 12
      • Rijiyoyin Azabar Jahannama
      • Ba mu fitar da rai kan Kofin Turai ba — Wenger
      • Yan Boko Haram na zuba guba a ruwa
      • Buhari ya aika sunayen ministoci majalisa
      • Google ya fitar da samfurin mota mara matuki da za...
      • Jiragen saman Isra'ila sun kai hare-hare a Gaza
      • HANYOYI 10 DA ZAKA RAGEWA ANDROID PHONE JAN CAJI D...
      • [Video] Download Highlight Arsenal 2 Olympiacos 3
      • [Video] Download Highlight Porto 2 Chelsea 1
      • [Video] Download Highlight Barcelona 2 Bayern leve...
      • Buhari Ya Hadu Da Cameron
      • Yadda zaka Gyara layinka idan ya daina tura sakon ...
      • Alhazai fiye da 1000 ne suka rasu a Mina
      • Kawancen Boko Haram da IS ba alheri ba ne'
      • Tsokaci AKan Sallar Bana
      • Yanda Zaka dawo da Android zuwa modern
      • [Photos] Buhari Ya Gana Da Sarkin Jordan
      • Fareesah Part 1
      • Abincin Zuciya
      • Makaho Mai Ayukan Irin Na masu Ido
      • Idan Matarka Ta Bata Maka Rai
      • Kungiyar Yarrabawa Ta Gargadi Buhari Akan Saraki
      • Isra'ila na ci gaba da zaluntar Falasdinawa a Bait...
      • Gareth Bale Ya Dawo Baya Jinya
      • Boko Haram ta kai hari a yankin Askira Uba
      • [Photos] Behind The Scene Photos of ANA WATA GA WA...
      • NNPC: Za a gurfanar da masu almubazzaranci-Buhari
      • Nijar ta ware kwanakin juyayin mutuwar Alhazai
      • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Tara A Borno
      • Ranar Laraba Buhari Zai Mikawa Majalisar Dattawa S...
      • Kasar Faransa Ta Kai Hari Kan Sansanin ‘yan Ta’ada...
      • An tabbatar da rasuwar alhazan Nigeria 54
      • [Photos] Buhari Ya Gana Da Shugaban Kasan Korea
      • sakamakon wasannin mako na gida nigeria da aka yi:
      • Ashe Kaine Mijina Part 10
      • Ashe Kaine Mijina Part 9
      • Ronaldo ya yi takaici da bai ci kwallo ba
      • [Video] Download Kannywood Film Zee Zee
      • Alhazai 16 na jihohi uku sun jikkata
      • MESSi ya samu Mummunar Rauni
      • [Video] Download Highlight Tottenham 4 Manchester ...
      • [Video] Download Highlight Leicester City 2-5 Arsenal
      • [Video] Download Highlight Manchester United 3 Sun...
      • [Video] Download Highlight Barcelona 2 La Pasma 1
      • [Video] Download Highlight Real Madrid 0 Malaga 0
      • [Video] Download Highlight Newcastle 2 Chelsea 2
      • An kai hari a ofishin SSS a Lokoja
      • Sarkin Kano Ya Auri Yar Lamido Adamawa Aboye
      • Ashe Kaine Mijina Part 8
      • LEWANDOWSKI ya sake kafa tarihi
      • Manchester United ta doke Sunderland 3-0
      • Newcastle da Chelsea sun tashi wasa 2-2
      • Tottenham ta ci Manchester City 4-1
      • An Rabawa Iyalan Rabilu Musa Ibro Gado
      • An kama Yarima Saudiyya Da Niyan Yin Fyade A Amurka
      • [Photos] Shin Zaka Iya Siyan Wanna Suwaita Akan Ku...
      • Sarkin Zang Na Taraba Ya Rasu Makka
      • Makaho mai koyar da masu ido karatu
      • [Fasaha] Yanda Zaka haɗa Wayan Android Da kwamfuta...
      • Girgizar kasa ta afku a Indonesiya
      • Kukan Kurciya Jawabi ne
      • [Photos/Nishadi] Abinda Ya Dace Da Kwarto Kenan
      • [Download Tafsir] Hukuncin Sallan idi da Layya da ...
      • WASANNI: An Zura Kwallaye 644 A Gasar Firimiyar Ni...
      • BUHARI Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Suka Rasa Rayuk...
      • Ingila za ta rasa gurbi daya a gasar zakarun Turai
      • Neymar ya tattauna' da Manchester United
      • Tsohon kwarto na kokarin kwace ’ya’yan mijin tsohu...
      • [Photos]Buhari Ya Gana Da Manya Shugabanin Duniya
      • Ashe Kaine Miji Na Part 7
      • Iska Mai Fita Ta Gaban Mace
      • Za a cire Nigeria cikin jerin kasashe masu Polio
      • Mourinho Ya Yiwa Wenger Hannunka Mai Sanda
      • Fifa: An soma bincike kan Blatter
      • A Daina Dora Alhaki A Kan Mahajjata - Sarkin Kano
      • 'Yan Boko Haram 200 sun mika wuya
      • Gwamnatin Saudiyya ta kare kanta
      • [Photos] Bukola Saraki A Sinima
      • [Fasaha] Yanda Zaka Dakatar Da Wani Daga Kira ka
      • Duniya Za Ruguje
      • Sojojin Nigeria sun kwato garin Banki
      • 'Da akwai 'yan Nigeria da Niger cikin wadanda suka...
      • [Photos Evidence] Mummunar Tafiya Jami'an Tsaron K...
      • Saudiyya : Sarki Salman Ya Bukaci A Gaggauta Binci...
      • Labarin Wani Sarki Da Bafadensa
      • Yana Mafarkin Wata Mata
      • Ashe Kaine Miji Na Part 6
      • Layya Tana Da Sharadan Ingaci Gudu Biyar
      • Yayin da Musulmai ke bikin babbar Sallah an kai ha...
      • 'Kwanan Boko Haram ya kusa karewa'
      • An jefi Bukola Saraki a filin Idi
      • Sama Da Mutane 300 sun rasu a aikin Hajji Yau
      • Hukunce Hukuncen Layya
      • Shin Ya Halartar Mata Su Tafi Wajen Sallar Eidi
      • Shugaban Najeriya zai halarci taron MDD a Amurka
      • An saki ‘mai tsaron lаfiуаr’ Oѕаmа Bin Lаdеn
      • Yau Take Sallah
      • Hukunci Alhajin Da Ya Sadu Da Matarsa Kafin Arfa
      • Michel Kafando Ya Koma Kan Mulki A Burkina Faso
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger