1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Article » LABARIN KHATIMIN ANNABTA

LABARIN KHATIMIN ANNABTA

By Abdul Mk
Add Comment
Saturday, 4 July 2015

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI
Wannan hatimin Annabtar yana daga cikin alamomi guda 3 wadanda suka janyo musuluntar Salmanul Farisi (ra).
Shi Salmanul Farisi ainihinsa mutumin Qasar Farisa ne. Wato IRAN. Mahaifinsa mai wadata ne. kuma Babbane agarin. kuma yana mutukar son Salmanun (rta).
Ya taso agidansu da kuma garinsu ya tarar suna bauta ma WUTA ne. Sai watarana Babansa ya aikeshi zuwa wata gonarsa, akan hanya sai yaga wasu Kiristoci suna Ibada achochinsu.
Sai yaga abin ya burgeshi. Don haka ya tsaya ya saurara. Sannan ya koma gida yana bayar da Labari yana cewa: "YAU NAGA WASU MUTANE SUNA IBADA, AMMA FA IBADARSU TAFI TAMU"
Da Babansa ya samu labari sai yasa aka daureshi Aka kulleshi acikin wani Daki. Aka sa mai tsaronsa.
Ana cikin hakane sai ya samu dama ya Kubce
Ya gudu wajen wadannan kiristocin. Yace su kwatanta masa garin da zaije ya samu mutanen kirki masu bin irin wannan addinin nasu.
Sai suka ce masa ya tafi Sham (Syria). Achan ne ya samu wani babban Pada na Kirista (nasara) ya zauna ya zama almajirinsa yana yi masa hidima tsawon wasu shekaru har zuwa lokacin da Padan zai rasu, Sai Salman ya tambayeshi cewa:
"INA SO KAYI MIN WASIYYAR GARIN DA ZAN SAMU WANI MUTUMIN KIRKI WANDA YAKE KAN WANNAN ADDININ?"
Sai ya turashi Izuwa wani gari zuwa wajen wani Pada. Anan ma haka yayi ta masa hidima har sai da ya cika. Shima da zai rasu sai da Salman yayi masa irin waccan tambayar.
Hakanan dai ya rika yawo daga wajen wannan pada izuwa wancan, daga Sham zuwa Mausul zuwa 'Umuriyyah ta Rum.
Har dai na Karshen cikinsu yace masa:
"Yanzu babu sauran wani mutum wanda yake kan ainihin koyarwar wannan addinin. Amma yanzu haka ma Ka iso lokacin bayyanar ANNABIN QARSHE. zai q haifeshi a Haramin Makkah amma zai yi hijira zuwa wani gari mai Qasar gishiri da kuma yawan Dabinai Don haka ka tafi chan wajensa"
"Yana da wasu siffofi guda 3 wadanda ba zasu buya agareka ba.
1. BA YA CIN SADAQA.
2. AMMA YANQ CIN KYAUTA.
3. YANA DA KHATIMIN ANNABTA ATSAKANIN KAFADUNSA".
Saboda haka Salman yana nan acikin wannan halin, Rannan sai ga wasu yahudawa wadanda suke zaune kusa da Madeena sunzo garin da yake.
Yace musu idan sun yarda zasu tafi dashi zuwa Madina, zai basu dukkan dukiyar da ya mallaka.
Awannan lokacin kuwa Salamanul Farisi mutum ne mai tarin dukiya da yawa.
Ga kudi, ga shanu, ga Rakumma, ga Tumaki.. Ance ko shanun ma sunfi 100.
Amma haka duk ya tattara ya basu. Don kawai yana so su kawoshi garin da zai hadu da Manzon Allah (saww).
To amma saboda rashin adalci irin na Yahudawa, bayan sun taho dashi akan hanya sai suka sayar dashi amatsayin Bawa.
Sai suka Sayar dashi ga wani mutum, shi kuma ya sayar dashi a kusa da Madeena. wani daga Yahudawan Banu Qurayzah ne ya sayeshi.
Amma awannan lokacin, Manzon Allah (saww) yana Makkah. bai yi hijira zuwa Madeena ba.
Don haka anan Salmanul Farisi ya zauna amatsayin Bawa, shekara da shekaru.
Watarana Ubangidansa yasa shi ya hau bishiya ya yanko masa Dabino. Yana kan dabinon sai Shi Maigidan nasa yayi wani Bako yazo wajensa acikin bacin rai da tashin hankali.
Yana ce masa:
"KAICON LARABAWAN NAN !! WAI KAJISU SUN TAFI QUBA'A SUN TARU AWAJEN WANI MUTUM SUNA CEWA WAI SHI ANNABI NE"
Sai Salmanul Farisi yaji wata irin Hajijiya ta kamashi. kamar zai fado Qas. Jikinsa yana rawa!!
Ya sauko yace musu:
"DON ALLAH ME KUKE FA'DA? SHIN WANNAN ANNABIN YA BAYYANA NE?? A INA YAKE?"
Nan take sai Ubangidan nasa ya Tsinka masa Mari!!
Yace masa:
"KAI KANA BAWA, INA RUWANKA DA WANNAN ZANCEN?"
Shi dai Salmanul Farisi bai yi Qasa agwiwa ba, yaci gaba da tuntubar labarin Manzon Allah (saww).
Har dai ya samu labarin cewa Manzon Allah (saww) yana chan a Quba'. (Wani Qauye ne kusa da Madeenah).
Sai ya nemi 'dan Dabinonsa ya rike. Sannan ya tafi wajen Manzon Allah (saww).
Daga zuwa sai ya same shi atsakiyar Sahabbansa suna zaune. Sai ya mika masa dabinon nan yace masa:
"GA SADAQAH na kawo muku ne don naga kun chanchanta."
Sai Manzon Allah (saww) yace ma Sahabbai "KU CI"
Amma fa Shi (saww) bai ci ba.
Salmanul Farisi ya fada (azuciyar sa) yace "Naga 'daya daga siffofin nan"
Washe gari ma sai ya sake dawowa da wani dabinon. Ya miko ma Manzon Allah (saww). Yace : "GASHI WANNAN KYAUTA CE NA KAWO MAKA DON NAGA KAMAR BAKA CIN SADAQAH"
Sai Manzon Allah (saww) yq karba da hannunsa mai albarka. Ya bude dabinon ya fara ci sannan ya mika wa Sahabbansa (rta).
Da Salmanul Farisi (rta) yaga haka sai yace:
"NAGA NA BIYU"
Daga nan sai Salmanul Farisi ya sake dawowa. Adaidai lokacin nan Manzon Allah (saww) yana wajen Makabartar Baqee'a. ya tafi janazar wani daga cikin Sabbansa (rta).
Salmanu yace:
"Sai na kasance ina bin bayansa ina duddubawa ko zan ga cikon alama ta ukun nan wacce Malamina ya gaya min?"
Shi kuwa Manzon Allah (saww) yana sanye da wani Mayafi.
Da yaga ina binsa abaya-abaya sai kawai ya tube mayafin. Yace min:
"SALAMANU KO KANA SO KAGA WANNAN ABUN NE?"
Salamanu yace "Sai naga wannan KHATIMIN ANNABTAR ABAYAN KAFADARSA. KAMAR GIRMAN QWAN TATTABARA"
"SAI NA RUNGUMESHI INA KUKA, INA SUMBARTAR KHATIMIN ANNABTAR INA KUKA"
Sai Manzon Allah (saww) yace min:
"JUYO YA SALMANU KA BANI LABARI"
Nan take sai na bashi labarina tun daga farko har Qarshe.
ALLAHU AKBAR!!
Nan zqmu tsaya, Sai nan gaba zamu dora a kashi na uku IN SHA ALLAHU.
Don neman Qarin bayani akan wannan aduba tarjamar Sayyiduna Salman Alfarisy cikin wadannan litattafan:
★ SIYARU A'ALAMIN NUBALA
★ USUDUL GHAABAH.
★ TAREEKHUL KABEER.
★ ALBIDAYAH WAN NIHAYAH.
★ SIFATUS SAFWAH.
★ RIJALUN WA NISA'UN HAULAR RASUL (SAWW).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 07:40
In Hausa Article
Title : LABARIN KHATIMIN ANNABTA
Description : DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI Wannan hatimin Annabtar yana daga cikin alamomi guda 3 wadanda suka janyo musuluntar Salmanul Farisi ...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Article

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "LABARIN KHATIMIN ANNABTA "

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ▼  July (211)
      • Nasara: Chadi ta kashe 'yan Boko Haram guda 100
      • Shugaban kungiyar Haqqani Jalaluddin ya rasu
      • Ebola - Afrika: An samu kwarin gwiwa a yaki da Ebola
      • Boko Haram: Yan kunar bakin wake sun mutu a Maiduguri
      • Walcott da Cazorla sun sabunta kwantaraginsu
      • Sojoji sun ceto fararen hula 59 daga hannun Boko H...
      • Taliban ta nada sabon shugaba
      • A kwashe 'yan gudun hijira daga makarantu
      • Yadda ‘Yar’Adua Ya Soke Batun Sayar Da Matatun Mai...
      • ZIYARA: Buhari ya kammala ziyararsa a Kamaru
      • Boko Haram: Yan Boko Haram sun yi wa mutane yankan...
      • Kamaru: Za mu mutunta kasancewar tsibirin Bakassi ...
      • ZIYARA: Yan Majalisar dattawan Najeriya zasu ziyar...
      • Shugaban Taliban Mullah Omar ya rasu
      • Matatun mai na Fatakwal da Warri sun fara aiki
      • Kasar Israi'la ta aikata 'laifukan yaki' a Gaza
      • NFF ta nemi hadin kan Jamus
      • Amfanin Dabino a Muslunci
      • Oni na Ile-Ife ya mutu
      • Shugaba Buhari zai kai ziyara Kamaru
      • An hana mata sanya hijabi a Diffa
      • An yanke wa Saif al Islam Gaddafi hukuncin kisa
      • Rikicin majalisar dokokin Nigeria
      • Gwamnati ta soma tantance wakilan Boko Haram
      • An kashe wani gawurtaccen Zaki a Zimbabwe
      • Keshi ya bukaci a biya shi sama da Naira biliyan daya
      • BOMB: Bam ya fashe a Damaturu
      • Boko Haram: An hallaka akalla mutane 19 a Maroua
      • Sinadarin Chlorine ya halakka mutane 8 a Jos
      • Amurka da Kenya sun raba-hanya a kan auren jinsi daya
      • Labarin soyayya na Niu Lang da Zhi Nu
      • AL’AJABI: Karon Battar Zaki Da ‘Direbobi, Bajinta ...
      • An samu ci gaba a yaki da maleriya
      • ZIYARA: Shugaba Obama na kan hanyar zuwa Kenya
      • BOKO HARAM: Sabbin dabarun kai hare-haren Boko Haram
      • Turawa na shirin daina tallafa wa Burundi
      • Amirka da Turkiyya da zasu hada kai don yakar Daesh
      • Akalla mutane 30 aka kashe a Gombe
      • Amurka ta 'taimakawa' Boko Haram — Buhari
      • An kai harin bam a garin Marwa
      • Buhari ya yi watsi da auren jinsi daya
      • 'An gano Kur'ani mafi dadewa a duniya'
      • An gano maganin cutar mantuwa
      • Barcelona ta doke LA Galaxy a Amurka
      • Za mu iya tattaunawa da Boko Haram - Buhari
      • Nasiha Mai Ratsa Zukata
      • An damke dillalin makamai na Boko Haram
      • Rooney zai koma mai cin kwallo a United
      • Boko Haram:— Bankin duniya zai kashe biliyoyi
      • An gano shanu 2,000 a dajin Kamuku
      • Sterling ya ci wa Man City kwallo
      • Tarihin Najeriya tun shekaru aru-aru
      • Ba zan nada ministoci ba sai a Satumba — Buhari
      • Na gamsu da shugabancin Buhari — Obama
      • Bom Ya Tashi A Damaturu
      • Buhari Yagana Da Obama
      • Dalilin da ya sa SSS ta binciki Dasuki
      • An Tozarta Dasuki Ne Saboda Ya Ki Bin Buhari, Inji...
      • Abun lura 1 & 2....
      • Bai kamata jami'an SSS su shiga gidana ba —» Inji ...
      • Buhari zai gana da Obama
      • Dasuki na shirya wa Nigeria makarkashiya-SSS
      • Vidal na gab da koma wa Bayern Munich
      • Saudia ta cafke 'yan kungiyar I-S fiye da 400
      • Ashton Carter zai kai ziyara Isra'ila
      • Buhari zai kai ziyara Amurka
      • Bam ya halaka mutane 12 a filin Idi
      • Dss Sun kama Sambo Dasuki
      • Alqur'ani Yayi Gaskiya!!
      • An haramta sa nikabi a Kamaru da Gabon
      • Gwamnati ta gargadi Radio Biafra
      • An soke hawan Sallah a Zazzau
      • An kashe mutane da dama a Ngamdu da Damasak
      • A daina ci da gumin 'yan fim — Buhari
      • An nada Oliseh a matsayin kocin Super Eagles
      • Na yi murna da komai ya zo karshe — Sterling
      • Boko Haram: Mutane na tserewa daga Damasak
      • Kun san tarihin sabbin manyan jami'an tsaron Nigeria?
      • Zan yi taka tsantsan kan cire tallafin mai — Inji ...
      • YADDA AKE SAMA WAKA HOTO TA WAYAR JAVA !!
      • Amaechi, Bakare kila Su Kasance Cikin Wadanda Zasu...
      • ZAKKA: Mutane uku sun mutu wajen karbar zakka a Ka...
      • EBOLA: Yara dubu 5 sun zama marayu a Laberia
      • Chelsea ta dauki Asmir Begovic
      • Man United Su Sayi Schweinsteiger da Schneiderlin
      • An hallaka mutane 16 a Fotokol
      • Buhari ya kori manyan jami'an tsaro
      • An kama 'Yan Nigeria masu kutse a intanet
      • Buhari ya nada sabbobin jami'an tsaro
      • MAHAIFIYARSA TA MAKANCE
      • KWARO YA SHIGA TA MAKOGORONSA
      • Hukunci Masu Yin Hacking Din Data
      • SIFFAR RAWANIN MANZON ALLAH(SAWW)
      • MAI HAILA ZATA YI KARATUN ALQUR'ANI
      • Hukunci Yin Family Planning (Kayyade Iyali)
      • Sababbin manyan jami'an tsaron kasar da Buhari ya ...
      • Buhari ya kori manyan Jami'an tsaron Nigeria
      • An hallaka mutane kusan 16 a Port Harcourt
      • An kama 'Yan Nigeria masu kutse a shafin yanar-giz...
      • Sarkin Kano ya bukaci likitoci su janye yajin aiki
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Sadiya Gombe Ft Al'ameen Bauchi (Ra'ayin Ki Ne Nawa) Sabuwar Waka
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Fantyz Guy ft Mr SPYZY - ALKALERI GARINA (Official Hausa HipHop Music Video...
        Bauchi Base Popular HipHop musician FANTYZ GUY release hit track ALKALERI GARIN Featuring Mr SPYZY 

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger