1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Fasaha » Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Facebook

Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Facebook

By Abdul Mk
Add Comment
Wednesday, 24 June 2015

Wannan lamari na barin account da mutumin da ya rasu a social network yana baiwa mutane da dama haushi da takaici, musamman waɗanda suke kusa da wanda ya mutu. A wani lokaci za ka ga mutane suna jingina (tagging) hotunan banza ko na batsa ga shi wannan mamaci, haka za ka samu duk shekara mutane su yi ta mai murnar cika shekara (birthday) amma alhali shi yana lahira, wasu waɗanda suka saba wasa da shi, idan suka yi magana da shi bai amsa ba su yi fushi ko zagi da dai makamantan su.

Muna yawan samun ƙorafe-ƙorafe a wurin jama’a musamman waɗanda suka damu da makomar ‘yan uwansu waɗanda suke da account a Facebook ko Twitter ga shi kuma Allah Ya yi musu mutuwa dangane da ya za ayi su iya goge wannan account domin yadda hankalinsu yake tashi duk lokacin da suka ga hotonshi ko kuma wani abu makamanci haka.

Wannan dalilin ne ya sa muka yi bincike muka gano ashe tun tsawon wancan lokacin da muke ganin haka tuni kamfanin Facebook suka fito da wani fom wanda shi ne kawai abin da kake buƙata domin goge irin wannan account ɗin.

A GYARA HALI KAFIN A MUTU.

Yana da kyau duk wanda yake karanta wannan takarda ya sani wata rana shi ne wanda mutuwa zata riske shi, kuma bai san wani lokaci ba ne, kuma bai san a wani hali ba ne. Yana da kyau mu riƙa tsaftace abubuwan da muke sakawa  social networks domin duk abin da ka saka yana nan kuma wani ya killace shi. Kuma dani da ku duk mun san watan wata rana za a tambaye mu, kuma sai mun bayar da bahasi a kai.

Mutane da dama basa la’akari da cewar duk abin da na rubuta ko na saka a social network Allah zai tambaye ni, idan na saka wata magana ta karya wani ya yaɗa to zunubin yana kaina, haka idan na yaɗa abin da yake na alkairi ladan yana kaina. Mu guji yiwa mutane ƙazafi, saka hotunan da basu dace ba, da kuma yaɗa jita-jita da zarge-zarge domin waɗannan abubuwan suna da wahalar tuba kuma suna da wahalar kankarewa.

INA ZAN SAMI FOM DA ZAN CIKE

Shi wannan fom da za ka cike, yana da waɗansu ƙa’idodi da ya kamata mutum ya sani, kuma akwai abu mai muhimmanci da koya ya kamata ya kiyaye.

Kamfanin Facebook basa la’akari da garinka ko kuma addinin ka, suna la’akari da addininsu da kuma al’adunsu, saboda haka abin da suke buƙata wurin cike fom ɗin shi ne takardar shaidar cewar wannan mutumin ya mutu wacce kotu ko Asibiti suke bayarwa. Saboda haka kafin ka fara cike wannan fom sai ka je ka karɓi takardar shaidar cewar wane ya mutu, sannan kayi scanning sai ka fara cike fom ɗin.

Za a iya buɗe wannan fom ɗin ta bin wannan link kamar haka https://www.Facebook.com/help/contact/228813257197480

Fom ɗin wanda da Turanci aka rubuta shi yana buƙatar ka amsa tambayoyi guda takwas (8) kafin ka aika shi wanda su kamfanin Facebook za su duba su gani sannan daga baya su goge shi wannan account ɗin.

TAMBAYOYI DA AKA AMSA

Cikakken Suna: A wannan ɓangare ana son kai da za ka cike wannan fom ɗin ka saka sunanka cikakke misalin Salisu Hassan
Sunan wanda ya mutu: shi kuma rami na biyu sai ka rubuta cikakken sunan wanda kake son a goge account ɗinshi, namiji ne ko mace.
Imel ɗin mamaci: a na son ka saka imel ɗin da kake tunanin cewar da shi wannan mamacin ya buɗe account, kodayake wannan imel ba dole ne ka san shi ba, kuma idan ma baka cike wannan ramin ba saboda rashin sani babu matsala, amma saka imel ɗin zai baiwa kamfanin sauƙi zaƙulo account ɗin kuma su goge shi.
Link ɗin mamaci na Facebook: duk mutumin da ya buɗe Facebook, suna bashi wani link (hanya ko rariyar liƙau) da ita ce hanyar shiga shafin ka kai tsaye, kuma wannan hanya babu mai ita a Facebook sai kai. Misali nawa shine https://Facebook.com/salisuwebmaster duk mutumin da ya rubuta wannan link a jikin browser to zai kaishi shafi na na Facebook kai tsaye. To idan baka san na wanda ya mutu ba, abin da za ka yi shi ne ka nemo shi a cikin abokanenka, sai ka taɓa sunan shi, zai kai ka kai tsaye cikin shafin sa, sai kayi amfani da browser ka kwafe link ɗin da ka gani sai ka saka a wannan ramin.
Dangantar ka da mamaci: lallai Facebook suna buƙatar su san dangantakar da wannan mamaci kafin su cire wannan shafi a gidansu. Saboda haka za ka zaɓi dangantakar ka, a cikin kashi uku da suke da shi.
Iyalai mafi kusa: kai ɗan uwansa ne, ko baban sa, ko matar sa ko kuma yayan sa da dai makamanta su.
Dangantakar jini: kamar kaka, goggo, baffa, da kawu da dai makusanta na jini
Abokantaka: idan wanda ya rasu, abokinsa ne ko kuna aiki wuri guda ne ko kuma aji ɗaya kuka yi, ko kuma ma dai ka san cewar ya mutu ne, sai ka zaɓi nan.
Me kake son Facebook su yi da account ɗin: a nan Facebook suna son ka faɗa musu abin da kake son ayi maka da account ɗin domin ba goge shi kaɗai za su iya yi ba, a nan akwai abu guda hudu (4) da za ka iya basu dama su yi.
A faɗawa abokansa ya mutu: wannan zabi ne da za ka ba Facebook na su saka a cikin shafin sa cewar wane fa yanzu ba shi, ya mutu, kuma su saka alamar da kowa zai iya ganewa cewar yanzu da gaske babu shi.
A goge account ɗin sa: wannan shi ne ɓangaren da ya fi kyau ayi amfani da shi, domin zai ba Facebook dama su share dukkan abin da wannan mamacin ya saka a cikin Facebook, tun daga rubutunsa, likes da comments da sharing da hotuna da video da yasa a Facebook, yadda ba shi suna ba su.
Ina da buƙata ta musamman: idan kuwa akwai wani abu da kake buƙatar Facebook su yi maka ba sharewa ba to sai ka zaɓi wannan ɓangare.
Ina da tambaya: wannan kuma idan kana da tambaya da kake son kayi wa Facebook sai ka zaɓi wannan ɓangare.
Yaushe mamacin ya rasu?: a wannan ɓangare suna son ka zaɓi rana da wata da shekarar da ya mutu ka saka musu.
Takardar shaidai mutuwarsa: a wannan wurin shi ne za ka sakawa Facebook takardar shaida daga kotu ko asibitin da mutum ya mutu cewar wannan mutumin ya mutu, ko shaida da mutane gidansu cewar su suka baka izini cewar Facebook su cire shafinsa.
Da zarar ka gama cikewa sai ka aika musu da wannan fom domin su duba su gani sannan su yi abin da ka ce kana so.
Ba kamar yadda mutane suka tsammani ba, zai ɗan ɗauki lokaci kafin kamfanin Facebook su waiwayi takardar da, domin kamfanin da yake da mutane sama da biliyan daya da rabi yana buƙatar lokaci kafin ya aiwatar da wani abu. Kai dai tunda ka aiki sai ka jira.

Kuma babu laifi idan mutane mabanbanta suka aika, misali a sami mutane da yawa su aika domin hakan zai sa Facebook su gane cewar wannan bawan Allah da gaske ne cewar ya mutu.

Muna rokon Allah Ya jiƙan waɗanda suka riga mu mutuwa da imani, Ya kyautata ƙarshenmu ya yafe mana kurakuranmu, ya amintar da mu baki ɗaya. Amin

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 16:31
In Fasaha
Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Facebook Title : Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Facebook
Description : Wannan lamari na barin account da mutumin da ya rasu a social network yana baiwa mutane da dama haushi da takaici, musamman waɗanda suke kus...
Rating : 5
Related Posts: Fasaha

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Facebook"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ▼  June (216)
      • CBN extends deadline for BVN registration
      • Facebook ya bude ofishin farko a Africa
      • Sojoji sun yi wa mata fyade a Sudan
      • Zurfin Ciki 1----1
      • HUKUNCIN AZUMIN WANDA YAYI MAFARKIN SADUWA
      • I don't have a house outside Nigeria - Aliko Dangote
      • Chadi ta yi wa Boko Haram luguden wuta
      • HUKUNCIN JININ HAILA MAI RIKICI
      • Carlos Tevez ya koma Boca Juniors
      • Wikki Tourists ta doke IfeanyiUbah da ci 1-0
      • Hisba ta kama mutane ‘aljannu’
      • Yadda ’yan Boko Haram suka kashe mijina suka maida...
      • Yadda muka yi azumi a kasar Switzerland
      • Tsohon shugaban Nigeria Gowon ya goyi bayan an cir...
      • An kai harin bam a Maiduguri
      • Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 5 a Maidu...
      • RAHOTO Kan Sabuwar Kungiya Mai Kama Da Boko Haram ...
      • HUKUNCIN SAYAR DA KAYAN ADO
      • RASHIN GAMSAR DA MATARSA
      • LABARIN WANI BARAWO
      • TANA AZUMI AMMA BATTA SALLAH
      • SALATUT–TASBEEHI DAGA ZAUREN FIQHU
      • BAI HALATTA KA RIKE KUDIN WANI
      • Buhari ya rushe hukumar zartarwar NNPC
      • MATSALAR CHANZAWAR HALITTA
      • Obama ya gayyaci Buhari zuwa Amurka
      • An yanke wa mutane 9 hukuncin kisa a Kano
      • Musulman China da aka hana azumi sun fafata da 'ya...
      • YADDA ZAKA FITA DAGA DUK WANI TSARI DA MTN SUKE CI...
      • Budurwar da ta yi Tayin Mota da Gida Na Asibiti a ...
      • Yan Boko Haram sun Halaka Mutane 42 A Biu
      • Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Fa...
      • Liverpool ta saya Roberto Firmino
      • Cutar Kwalara ta barke a Sudan ta Kudu
      • Buhari ya gargadi gwamnoni Akan Cuwa-Cuwa
      • What should the fasting person do and what is obli...
      • Leaving Off Fasting During Ramadhaan Due To Exams ...
      • He had Sexual Relations With his Wife During the D...
      • If a Fasting Person Masturbates, Does This Break H...
      • Using an Inhaler During for the Fasting Person
      • Bleeding from the Mouth/Nose Whilst Fasting
      • She Fasted During Her Days of Menstration
      • Fast what is upon you from missed fasts first
      • Can I kiss my wife while fasting
      • [Music] Download Autar Mata by Nura M Inuwa ft Uma...
      • CIKIN DARE Part 1
      • DUK ABINDA KAKEYI DAKATA KA KARANTA TAMBAYOYIN NAN...
      • YA KAMATA KUJI LABARIN WANNAN MATAR
      • Mata 10 Wadanda Allah Ya Tsine Musu
      • Sabuwar Gwamnatin Najeriya Zata Inganta Rayuwar Na...
      • Arsenal na daf da daukar Petr Cech
      • An umurci soji su cire shingaye a Nigeria
      • Du'a Gamai Azumi Idan Zaiyi Buda Baki.
      • Yadda Zaka Sami Kyautar 1GB A Layinka Na Glo
      • Does Masturbation Break the Fast?
      • Birnin Tsafi [Part 1]
      • President Buhari to remove oil subsidy?
      • HUKUNCIN ORAL SEX
      • TSOKACI AKAN WA'AZI DA MASU YINSA
      • United na zawarcin Ramos da Schweinsteiger
      • Juventus ta dauki Mario Mandzukic
      • Zan yi wa Buhari biyayya — Atiku
      • Bam ya hallaka mutane 20 a Maiduguri
      • Mayakan IS Sun Yi Awan Gaba Da Wasu Limaman Massal...
      • [Pictures ] President Muhammadu Buhari In His Farm
      • President Buhari Moves Into Presidential Villa
      • CIN NAMAN MUTANE DA AZUMI
      • Messi ya jajantawa Neymar bisa jan kati
      • Limamai sun soki daina ciyarwa da azumi
      • Rahmatullah Part 7
      • MAGANIN CIWON MARA
      • Dan-Maraya Jos ya rasu
      • [Tafsir] DR SANI UMAR RIJIYALLEMU
      • [Tafsir]Download Ramadan Day 1 Tafsir By Sheikh Am...
      • [Mp3 Tafsir] Download Ramadan Day 1 Tafsir By Shei...
      • [Mp3 Tafsir] Download Ramadan Day 1 BySheik Kabir ...
      • Dan Marayan Jos Is Dead
      • Kakuta ya koma Sevilla
      • Gwamnatin Bauchi ta kwato motoci 28
      • FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU
      • Rahmatullah Part 6
      • SHIN AURENSU ZAI GYARU?
      • Bauchi Govt Seizes 22 Vehicles From Yuguda’s Wives
      • Rahmatullah Part 5
      • SIFFOFIN ALJANNAH
      • SHIN KOYA HALATTA MUSULMI YAYI AIKI A CHOCHI, DON ...
      • ADDU'A GAMAI AZUMI IDAN ZAIYI BUDA BAKI.
      • Sani Musa DanjaYayi Rabon Shinkafa A Kano
      • Kano Pillars ta doke Giwa FC da ci 4-1
      • [MUSIC] Download Kololuwar Fahimta By Naziru M Adam
      • A Touching Hadith About Dua During Iftar
      • Summary Of Things That Nullify A Person's Fast (sawm)
      • FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU
      • NAIMAKA RANA PART 10
      • HUKUNCIN CIN NAMAN SADAKAR ALJANU
      • IYAYENTA SUN HANA TA KOMAWA WAJEN MIJINTA
      • Wani dan bindiga ya kai hari a South Carolina
      • Dangote ya dade yana sha’awar Arsenal
      • Bam ya hallaka mutane 23 a Monguno
      • Ni ma ina kaunar Nafisa — Adam Zango
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger