1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Labarin Sarkin Busa

Labarin Sarkin Busa

By Abdul Mk
Add Comment
Saturday, 13 June 2015

Abin da ya sa na ce haka, a wani gari can ketaren Bahar Maliya a cikin kasar Jamus, tun shekaru da yawa da suka wuce, Allah ya saukar musu da wani babbar bala’i. Aka saukar musu da beraye ko’ina cikin garin. Berayen nan suka yi ta karuwa, har mutane suka rasa abin da su ke ciki, duk inda mutum ya duba garin ba ya ganin kome sai beraye. Ko wajen barci mutum in ya zo sai ya tarad da kamar ashirin tuku- tuku suna kwance. In hula ka ajiye, ko riga, kafin da safe sai ka tarar aljihun cike da beraye. In takaice maka labari, yawansu ba su kidayuwa. In da za ka kidaya su, ka kidaya kudajen da ke garin, sai ka ga sun fi yawan kudanjen nan kamar sau dari. Gari dai ba wajen sa kafa, duk beraye ne. Abinci kuwa mutum ko ya fi Aula dabara, ba yadda zai yi ya ajiye shi. Kome za a dafa sai a yi daidai da yadda za a iya cinyewa, don ko cikin akwati ka sa abinci ka kulle, sa san yadda za su yi wa akwatin nan huda, su shiga su cinye. Duk wani abu da ka sani ana yi da fata sun cinye. Ba ka ganin mai takalmi, ko matashin kai, ko gafaka, ko buzu a garin. In ko sun kai ga abin da ba su ci, sai su yi masa hudoji, su bata shi. Ta ishe ka ma ko jariri suka tarar yana barci, sai su tasam masa da cizo za su cinye. Sai in ya yi kuka iyayen su kwace shi. In dare ya yi kuma su kan hana mutane barci da kuka da guje-guje. In sun ga jikin mutum waje, sai su kama da cizo, wai za su cinye shi. To, kada ka zargi mutanen garin, ka ga kamar sakarci ya hana su kasha su. Bala’I sai sa’ad da Mai abu ya sawwake abinsa. Da sun ga kare sai su tasam masa, su nuna masa Sarkin Yawa ya fi Sarkin Karfi. Don kyanwa kuwa, wannan karamar alhaki, ba su kula da ita ba. Abin mamaki, mutane kuma in sun tasam ma kasha su, sai ka ga kamar kara su su ke yi. Don a sa tarko kuwa, ko a sa dafi cikin abinci a ajiye, duk wannan ba ya rudinsu. Da sun gani sai su kewaye, kamar gaya musu a ke yi. Duk mutanen gari suka rasa yadda za su yi, sai suka tasam ma mai garin, suna cewa shi ne ke da gashin tsiya, don tun da aka halicci duniya ba su taba jin irin wannan ba, sai cikin wannan zamani da ya ke sarauta. Suka ce ko dai ya san yadda zai yi da berayen nan, ko kuea su fitad da shi, su kore shi daga kasar. Sarkin ya rasa inda zai sa kansa. Mutanen gari kuwa sai kara matsa masa lamba su ke yi. Ran nan yana zaune zugum, wadannan dattijai su zo su zazzage shi su wuce, wadannan su zo su zunzungure shi su wuce. Sai ga wani dan tsoho bako ya zo, ya duka ya gai da Sarki. Sarki ya dube shi, ya gan shi wani iri, sai ya ce, “Malam, daga ina? Wace sana’a ka ke yi?” Tsoho ya ce, “Ga ni dai. Inda na fita da nisa, amma sana’ata busa, har mutane na kirana Sarkin Busa.” Sarki ya ce, “To, sai ka je ka sauka, in kana iya sauka nan, mu ba ta busa mu ke yi ba yanzu, ta kawunammu mu ke yi da wannan bala’i.” Sarkin Busa ya ce, “Ai ni ma ba busar banza na ke yi ba, wani asiri Allah ya ba ni wanda in na yi busa duk ko wane abu mai rai ya biyo ni. Da kwadi, da macizai, da beraye, da dukan naman ruwa da na tudu, da tsuntsaye, har da masu tafiya da kafa biyu, duk wanda ya ji na yi busa, ba sauran zama, sai ya yi ta bi na. Don wadannan ‘yan berayen da suka dame ku, in ka iya ba ni abin da na ce, yanzu sai in raba ku da su?” Sarkin ya dube shi, ya ce, “Yau ga abin mamaki, mene ne sule dari kuma! Sule dubu goma ma, in kana so sai in ba ka. Kai dai mu rabu da wannan bala’i.” Sarkin Busa ya ce, “To, madalla.” Ya sa wata irin mabusa bakinsa, ya yi ta busa, yana yawo cikin gari rariya rariya. Sai berayen nan suka yi ta fitowa ko ta ina, suna binsa tururururu, wadansu manya, wadansu kanana, wadansu tultul, wadansu kyamas-kyamas. Ga wadansu ja wur, wadansu fari fat, abin har da shudda da rawaya. Ka ga wadansu ruku-ruku da ciki wadansu suna ‘yan kuka tsui tsui, kamar suna fara’a da wata bushara. Da ya kwashe duk, sai ya nufi kogi yana busa, suna biye, mutane na kallo na murna. Da isarsa bakin kogi sai ya fada cikin ruwa yana busa, beraye kuma ba su san sa’ad da suka bi shi ba, yi ta yi wa juna barka. A tsaya ma a fadi farin cikin da mutanen garin nan su ke yi da rabuwa da wannan bala’I, ya zama kauyanci. Inda Allah ya kyauta wa Sarki da ya ke mutane ba su san rashin tsaida maganarsa ta sa wannan abu ya faru gare su ba. Da sun sani nan take su ke halaka shi duk da zuriyarsa. To, ga shi kuma duk nasa sun bace, balle a ce wani makirci aka kulla da shi. Da uban yaron nan mai dingishi ya ga abin da ya faru, sai ya ruga ya jawo dansa, yana murna. Aka tambayi yaro me ya sa su ke bin mutumin nan? Yaro ya ce, “Ai mun ji yana cewa mu biyo shi, duk abin dad’ na duniya ya ba mu. Ya ce akwai tabkin zuma, da nono, mu yi ta sha. Ga nama soyayye da dafaffe, wai inda zai nu-nu mana shinkafa ba a maganarta. Ni yanzu, duk bakin ciki na ke yi da aka bar ni baya. Yanzu suna can suna cin dadinsu, ni ina nan.” Beran nan guda kuwa da ya haye, sai ya tafi ya iske wadansu yana cewa, “Ba ku sani ba, na yi daron cin dadi. A can ketaren banza, ga nama. Ga mai, ga abinci iri iri, ba mai hana ka ci. Ya ce wajen nan da zai nuna mana ba a taba sanin akwai wani abu wai shi kare ba balle kyanwa, karamar alhaki. Zan isa, saura kadan, sai na ji na fada cikin ruwa. Yanzu ‘yan’uwana na can sun yi kiba ni rashin sa’a ya sa ni na tabe!” Saura suka yi ta cewa, “Allah ya sa wata rana mai busan nan ya zo nan kasar, ya tafi da mu mu ma!” Sarki ya baza mutane cikin duniya, ko sami labarin ya bulla wani wuri da ‘ya’yansu. Aka yi nema, ko labari. Suka gaji suka dangana. Manyan gari suka ce, “Kai, ba ku sani ba fa, Sarkin nan ke da duk wannan gashin tsiya. Tun da aka halicci duniya kun taba ko jin inda irin wadannan al’amura suka faru?” Saura suka ce, “A’a, lalle in ba tasam masa muka yi ba, har mu kuma zai sa a halaka mu.” Sai suka taru suka tafi gidan, suka kunna masa wuta. Mai gari ya fito da gudu, suka bi shi da jifa, suka kore shi garin, ya fita tsirara. Ilyalinsa kuwa suka fid da su, kowace ta nufi gidansu. Suka kwashe dukiyar da ya tara, da akwatunan kudi da ya jibge. Suka kona gidan, don kada sabon Sarkin da za su yi ya kwashi ciwon wancan na tsiya. [insert picture here, lower right-page 86] Ka ji abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa. Musa ya duba ya ga wuri ya yi haske, ashe har rana ta fito ba su sani ba. Sai ya ce wa aku, “Na ji abin da ke aukuwa ga mai alkawari ba ya cikawa. To, me ke faruwa ga irinku masu hana a cika alkawari? Bai tsaya garin jiran amsa ba, sai ya shiga gida a fusace. Da azahar ta yi Waziri ya kira tsohuwan nan ya yi mata kwando goma na zagi, don har yanzu ta kasa dabarar da za ta yi tfito da Musa. Tsohuwan nan ta ce, “Kullum ina kokari, wani dan aku gare shi mai tsai da shi da labaru ko yaushe har gari ya waye.” Waziri ya tashi ya mangare ta, ya ce, “Tun da ba ki da wata dabarar da za ki wayace dan tsuntsu, tafi, yau na sa wani.” Sai ya kira bawansa Barakai, wannan da ya aika wajen Sarkin Sinari kwanan baya, ya gaya masa abin da ya ke so, da kuma yadda aku ke hana Musa zuwa da labaru. Barakai ya yi shiri irin na mata, ya tafi gidan Sarki, ya tarad da Musa inda tsohuwan nan ta yi masa kwatanci. Ya yi masa maganar Mahmudu na can rai ga Allah, ya ce wai Mahmudu ya ce a gaya masa, tun da ba ya kaunar zuwa su gana, shi ma ko lahira kada Allah ya gama su. Musa ya fashe da kuka, ya ce, “Kullum ina so in tafi, dan akun nan ke tsaishe ni da labari. Ga ko Sarki ya ce in na yi wani abu ba da na shawarce shi ba, bai yarda mini ba duniya da lahira.” Barakai ya ce, “Don dai wannan dan tsuntsu, yau ka tafi. Nan zan kwana, da mun ji bayin nan sun yi barci mu je tare ka salami akun, in hana shi ya tsai da kai.” Musa ya ce, “Da kin kyauta.” {Don yana tsammani mace ce.) Suka zauna nan, har barci ya share bayin da ke saure. Suka tashi suka nufi wajen aku. Ko da aku ya hango su tafe su biyu, sai ya gane Barakai namiji magana, ya riga su ya ce, “Don Allah, yallabai, yau ka tafi. Ni ba na iya ba ka wani labari. Duk inda ka ke son zuwa, ka tafi.” Barakai da dubi aku, ya ce, “Ko ba ka ce ba, da ma yau ba mu son wani labari naka.” Aku ya langabe kai kurum, sai tausayi ya kama Musa, ya ce masa, “Me ya same ka yau?” Aku ya ce, “Tunani na ke yi.” Da ya ke Musa ba ya son ya yi wa akun nan abin da zai motsa masa rai, sai ya tambaye shi tunanin da ya ke yi. Aku ya ce, “Ina ya tara five da abin da Allah ya ba shi.” Musa ya ce, “Wannan masassaki ya ja wa kansa halaka.” Aku ya ce, “Da ma ka ji abin da ya same shi, ai da ka san lalacewar ba ta da iyaka.” Bai tsaya a ko ce ya fadi ba, sai ya fara.

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 13:02
In Hausa Novels
Title : Labarin Sarkin Busa
Description : Abin da ya sa na ce haka, a wani gari can ketaren Bahar Maliya a cikin kasar Jamus, tun shekaru da yawa da suka wuce, Allah ya saukar musu d...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Labarin Sarkin Busa"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ▼  June (216)
      • CBN extends deadline for BVN registration
      • Facebook ya bude ofishin farko a Africa
      • Sojoji sun yi wa mata fyade a Sudan
      • Zurfin Ciki 1----1
      • HUKUNCIN AZUMIN WANDA YAYI MAFARKIN SADUWA
      • I don't have a house outside Nigeria - Aliko Dangote
      • Chadi ta yi wa Boko Haram luguden wuta
      • HUKUNCIN JININ HAILA MAI RIKICI
      • Carlos Tevez ya koma Boca Juniors
      • Wikki Tourists ta doke IfeanyiUbah da ci 1-0
      • Hisba ta kama mutane ‘aljannu’
      • Yadda ’yan Boko Haram suka kashe mijina suka maida...
      • Yadda muka yi azumi a kasar Switzerland
      • Tsohon shugaban Nigeria Gowon ya goyi bayan an cir...
      • An kai harin bam a Maiduguri
      • Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 5 a Maidu...
      • RAHOTO Kan Sabuwar Kungiya Mai Kama Da Boko Haram ...
      • HUKUNCIN SAYAR DA KAYAN ADO
      • RASHIN GAMSAR DA MATARSA
      • LABARIN WANI BARAWO
      • TANA AZUMI AMMA BATTA SALLAH
      • SALATUT–TASBEEHI DAGA ZAUREN FIQHU
      • BAI HALATTA KA RIKE KUDIN WANI
      • Buhari ya rushe hukumar zartarwar NNPC
      • MATSALAR CHANZAWAR HALITTA
      • Obama ya gayyaci Buhari zuwa Amurka
      • An yanke wa mutane 9 hukuncin kisa a Kano
      • Musulman China da aka hana azumi sun fafata da 'ya...
      • YADDA ZAKA FITA DAGA DUK WANI TSARI DA MTN SUKE CI...
      • Budurwar da ta yi Tayin Mota da Gida Na Asibiti a ...
      • Yan Boko Haram sun Halaka Mutane 42 A Biu
      • Yadda ake goge account ɗin mutumin da ya mutu a Fa...
      • Liverpool ta saya Roberto Firmino
      • Cutar Kwalara ta barke a Sudan ta Kudu
      • Buhari ya gargadi gwamnoni Akan Cuwa-Cuwa
      • What should the fasting person do and what is obli...
      • Leaving Off Fasting During Ramadhaan Due To Exams ...
      • He had Sexual Relations With his Wife During the D...
      • If a Fasting Person Masturbates, Does This Break H...
      • Using an Inhaler During for the Fasting Person
      • Bleeding from the Mouth/Nose Whilst Fasting
      • She Fasted During Her Days of Menstration
      • Fast what is upon you from missed fasts first
      • Can I kiss my wife while fasting
      • [Music] Download Autar Mata by Nura M Inuwa ft Uma...
      • CIKIN DARE Part 1
      • DUK ABINDA KAKEYI DAKATA KA KARANTA TAMBAYOYIN NAN...
      • YA KAMATA KUJI LABARIN WANNAN MATAR
      • Mata 10 Wadanda Allah Ya Tsine Musu
      • Sabuwar Gwamnatin Najeriya Zata Inganta Rayuwar Na...
      • Arsenal na daf da daukar Petr Cech
      • An umurci soji su cire shingaye a Nigeria
      • Du'a Gamai Azumi Idan Zaiyi Buda Baki.
      • Yadda Zaka Sami Kyautar 1GB A Layinka Na Glo
      • Does Masturbation Break the Fast?
      • Birnin Tsafi [Part 1]
      • President Buhari to remove oil subsidy?
      • HUKUNCIN ORAL SEX
      • TSOKACI AKAN WA'AZI DA MASU YINSA
      • United na zawarcin Ramos da Schweinsteiger
      • Juventus ta dauki Mario Mandzukic
      • Zan yi wa Buhari biyayya — Atiku
      • Bam ya hallaka mutane 20 a Maiduguri
      • Mayakan IS Sun Yi Awan Gaba Da Wasu Limaman Massal...
      • [Pictures ] President Muhammadu Buhari In His Farm
      • President Buhari Moves Into Presidential Villa
      • CIN NAMAN MUTANE DA AZUMI
      • Messi ya jajantawa Neymar bisa jan kati
      • Limamai sun soki daina ciyarwa da azumi
      • Rahmatullah Part 7
      • MAGANIN CIWON MARA
      • Dan-Maraya Jos ya rasu
      • [Tafsir] DR SANI UMAR RIJIYALLEMU
      • [Tafsir]Download Ramadan Day 1 Tafsir By Sheikh Am...
      • [Mp3 Tafsir] Download Ramadan Day 1 Tafsir By Shei...
      • [Mp3 Tafsir] Download Ramadan Day 1 BySheik Kabir ...
      • Dan Marayan Jos Is Dead
      • Kakuta ya koma Sevilla
      • Gwamnatin Bauchi ta kwato motoci 28
      • FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU
      • Rahmatullah Part 6
      • SHIN AURENSU ZAI GYARU?
      • Bauchi Govt Seizes 22 Vehicles From Yuguda’s Wives
      • Rahmatullah Part 5
      • SIFFOFIN ALJANNAH
      • SHIN KOYA HALATTA MUSULMI YAYI AIKI A CHOCHI, DON ...
      • ADDU'A GAMAI AZUMI IDAN ZAIYI BUDA BAKI.
      • Sani Musa DanjaYayi Rabon Shinkafa A Kano
      • Kano Pillars ta doke Giwa FC da ci 4-1
      • [MUSIC] Download Kololuwar Fahimta By Naziru M Adam
      • A Touching Hadith About Dua During Iftar
      • Summary Of Things That Nullify A Person's Fast (sawm)
      • FIQHUN AZUMI DAGA ZAUREN FIQHU
      • NAIMAKA RANA PART 10
      • HUKUNCIN CIN NAMAN SADAKAR ALJANU
      • IYAYENTA SUN HANA TA KOMAWA WAJEN MIJINTA
      • Wani dan bindiga ya kai hari a South Carolina
      • Dangote ya dade yana sha’awar Arsenal
      • Bam ya hallaka mutane 23 a Monguno
      • Ni ma ina kaunar Nafisa — Adam Zango
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Zanga-zanga A Bauchi-Gwamnatin Ta Saka Dokar Hana Fita Da Zirga-Zirga Ac...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Fantyz Guy ft Mr SPYZY - ALKALERI GARINA (Official Hausa HipHop Music Video...
        Bauchi Base Popular HipHop musician FANTYZ GUY release hit track ALKALERI GARIN Featuring Mr SPYZY 
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Sadiya Gombe Ft Al'ameen Bauchi (Ra'ayin Ki Ne Nawa) Sabuwar Waka

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger