Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi barazanar tsige manyan ma'aikata da kuma shugabannin wasu hukumomin gwamnatin tarayya muddin suka ki gurfana a gaban majalisar tarayya domin kare kasafin kudin da aka ware masu na 2018.
Mun samu cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan barazanar ne a lokacin da ya gana da shugabannin majalisar tarayya din na majalisar dattijai da kuma wakillai a yayin wata liyafar cin abincin dare da ya shirya masu a cikin satin da ya gabata.
A wani labarin kuma, Manyan hukumomin dake kula da yalwatar abinci na duniya sun yi kakkausan gargadin yiwuwar samun matsalar yunwa matsanciya sakamakon karacin abinci da za ta iya shafar akalla kusan mutanen da suka kai miliya 4 dake zaune a jihohi 16 na arewacin Najeriya.
Kamar yadda muka samu, hukumomin abinci da kuma bunkasar aikin gona mallakin Majalisar Dinkin Duniya wata FAO a takaice da kuma wata hukumar ta bayar da agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya din watau WFP sun ce matsalar za ta iya shafar garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Source :naij hausa
Title :
Zanyi Wa Manya Ma'aikata Aika Aika - Buhari
Description : Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi barazanar tsige manyan ma'aikata da kuma shugabannin wasu hukumomin gwamnatin tarayya mu...
Rating :
5