Tsohon shugaban kasar Zimbabwe ya gana da manema labarai inda ya ce rashin adalcin ne da aka tsige shi daga mulki a watan Nuwambar bara.
Yawancin 'yan kasar ba su zaku da ganin ya koma kan mulki ba. Yawancin su na ganin lamarin kamar wani mafarki ne ya nuna yana son komawa kan mulki bayan ya shafe fiye da shekara 30 yana mulkin kasar.
Babban dalilin da ke bayan kalaman fatar Mugabe na neman ya koma kan mulki bai wuce na rarrabuwar kawunan 'yan kasar ba.
A bayyane ta ke cewa bangaranci ya riga ya yi wa kasar illa - kamar yadda lamarin ya ke a makabciyar ta - Afirka ta Kudu.
Kuma a halin da ake ciki yawancin 'yan kasar na fama da matsalolin yau da kullum, kuma fatar su ita ce sabon shugaban kasa Mnangagwa ya iya kawo sauyi mai ma'ana a rayukansu ta farfado da tattalin arzikin kasar.
Mugabe ya gana da manema labarai ne a gidansa da ke kusa da birnin Harare, inda yarika kokarin nuna cewa har yanzu yana da sauran iko a siyasar kasar.
Ya bukaci da lallai sai a gayyace shi ya shiga tafiyar mayar da kasar kan tafarkin tsarin mulki a siyasance, kuma ma ya ce dole sai da shi wannan gyara zai yiwu
Source :bbc hausa
Title :
Inason Komawa Karagar Mulki - Robert Mugabe
Description : Tsohon shugaban kasar Zimbabwe ya gana da manema labarai inda ya ce rashin adalcin ne da aka tsige shi daga mulki a watan Nuwambar bara. Ya...
Rating :
5