Tsohon shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu na fuskantar tuhume-tuhume makonni kadan bayan an tilasta masa sauka daga karagar mulkin kasar.
Tuhume-tuhumen da ake masa sun hada da cewa ya karbi wasu kudaden haram gabanin zamansa shugaban kasa.
Jacob Zuma ya shafe shekaru yana kauce wa tuhumar cin hanci da rashawa, kuma lauyoyinsa sun rika daukaka kararrakin da ak yi a kansa cikin nasara.
Masu sukar lamirin Mista Zuma sun rika zargin masu shigar da kara da cewa suna tsoron sa ne.
Amma a watan jiya sai gashi an tilastawa Mista Zuma sauka daga mukaminsa na shugaban kasa.
Cikin rana guda sai ya koma wanda ba shi da wata gata ta musamman, kuma yanzu yana fuskantar gagarumar matsala.
A halin yanzu, babban jami'i mai shigar da kara, Sean Abrahams ya ture koken Mista Zuma, kuma ya ce tsohon shugaban mai shekara 75 da haihuwa zai fuskanci shari'a akan laifukka 16 da suka jibanci zamba, halasta kudin haram da cin hanci da rashawa.
Ana tuhumarsa da cewa a shekarun 1990 ya nemi wani kamfanin kera makamai na Faransa ya rika daukar nauyin bukatun Mista Zuma.
A wancan lokacin an sami wani mai ba shi shawara da laifin neman wanna cin hancin.
A yanzu dai gwamnatin ce za ta ci gaba da biyan kudaden da Mista Zuma zai bukata a wajen wannan shari'ar, kuma idan aka same shi da laifi, sabon shugaban kasar na iya yafe masa.
Duk da haka, wannan wani babban kalubale ne ga jam'iyyar ANC da take son nuna cewa ta juya wa dukkan batutuwan cin hanchi da rashawa baya gaba daya.
Source :naij hausa
Title :
Tsohon Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Zai Fuskanci Shari'ah
Description : Tsohon shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu na fuskantar tuhume-tuhume makonni kadan bayan an tilasta masa sauka daga karagar mulkin kasar. ...
Rating :
5