Labarin da ke iske mu yanzu yanzu na nuni ne da cewa Sanatan dake wakiltar mazabar yankin majalisar dattijai ta jihar Bauci ta Kudu watau Sanata Ali Wakili rasuwa.
Mun dai samu labarin hakan ne daga majiyar mu ta wani shahararren mai sharhi akan lamurran yau da kullum a kafar sadarwar zamani ta Tuwita watau Saleh Shehu Ashaka kamar dai yadda ya ayyana a shafin na sa mai adrreshin @AshakaSaleh da safiyar yau.
Jaridar naij ta samu cewa shi dai Sanata Wakili an haifeshi ne a shekarar 1960 inda kuma yayi karatun Firamaren sa a makarantar Lere sannan kuma ya je makarantar Damaturu inda yayin Sakandare.
Haka ma dai mun samu cewa yayi karatun jami'ar sa ne a jami'ar Bayero dake Kano sannan kuma tsohon jami'in Kwastam ne kafin daga bisani ya shiga harkar siyasa a shekarar 2015.
Source :naij hausa
Title :
Da Dumi Dumi:Allah Yayi Wa Sanata Ali Wakili Rasuwa
Description : Labarin da ke iske mu yanzu yanzu na nuni ne da cewa Sanatan dake wakiltar mazabar yankin majalisar dattijai ta jihar Bauci ta Kudu watau Sa...
Rating :
5