Shugaban jam'iyyar adawa a jihar Kwara ta Peoples Democratic Party, Cif Iyiola Oyedepo ya sanar da cewa jam'iyyar ta sa ta karbi akalla magoya baya 800 daga jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress cikin 'yan kwanaki kadan da suka wuce.
Shugaban jam'iyyar dai Cif Iyiola shine ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da majiyar mu a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Juma'ar da ta gabata inda kuma ya bayyana cewa wani babban dan siyasa ne Dakta Hanfi Alabere ya jagoranci magoya bayan.
Jaridar naij ta samu cewa haka zalika shugaban jam'iyyar a jihar ya bayar da tabbacin cewa a shirye suke su karbi mulki daga hannun 'yan APC a jihar idan zaben 2019 ya zo.
Source :naij hausa
Title :
APC Tasha Kashi A Hanun PDP A Jihar Kwara
Description : Shugaban jam'iyyar adawa a jihar Kwara ta Peoples Democratic Party, Cif Iyiola Oyedepo ya sanar da cewa jam'iyyar ta sa ta karbi aka...
Rating :
5