Fargaba a jihar Bayelsa saboda an rufe babbar hanya dan za’ayi sallar juma’a, sakamakon wani hoto da aka sanya a shafin labarai na yanar gizo, na wasu musulmai suna sallah akan wani bangare na titin hanyar zuwa Asibitin Diete Koki.
Hoton ya janyo maganganun bacin rai daga mutanen jihar, na cewa an yadda musulmai su rufe hanya; 'Wannan ibada ta addini watau sallah akan hanya a hana wasu masu hakkin amfani da hanyar amfani da ita bazasu yadda ba kuma a daina.
'A wata Pasta da aka sanya a gari anyi kira ne ga gwamnan Jihar ta Bayelsa, Mr Seriake Dickson, da kuma Chairman din karamar hukumar ta Yanaguwa, wanda ya fito daga Opolo, dasu gargadi musulmai dasu daina rufe hanya lokacin sallar Juma’a.
Duk da kace-nace din da akeyi amma ko mutum daya cikin jami’an gwamnati an rasa wanda keda niyyar yin wani jawabi akan al’amarin.
Source :naij hausa
Title :
Sallah Akan Titi Yakusa Tada Rikici A Bayelsa
Description : Fargaba a jihar Bayelsa saboda an rufe babbar hanya dan za’ayi sallar juma’a, sakamakon wani hoto da aka sanya a shafin labarai na yanar giz...
Rating :
5