Daga 4 ga watan Yuni na wannan shekarar ne, za'a kara kudin tsababa kan taba sigari da giya da sauran kayan maye, domin harajin da aka sanya musu zai ribanya. Hakan na nufin duk mai son ya cutar da hantarsa ko huhunsa sai ya kashe kudin da yafi na da.
Ministar kudi ta kasar nan Madam Kemi Adeosun ce ta fadi hakan ta hannun kakakinta a yau lahadi, inda ta tabbatar da cewa shugaba Buhari ya sahalewa shirin wanda aka baje shi shekaru ukku daga nan har 2020.
A karkashin shirin dai gwamnati zata kara haraji, inda shi kuma kayan cutar zasu qara kudi, wanda hakan zai sanya a rage shan su, ko kuma mutane su guje su baki-daya.
Source :naij hausa
Title :
Zamu Kara Wa Sigari Da Giya Tsada Don Kare Lafiyar Jama'a-Buhari
Description : Daga 4 ga watan Yuni na wannan shekarar ne, za'a kara kudin tsababa kan taba sigari da giya da sauran kayan maye, domin harajin da aka s...
Rating :
5