Mutane a kalla 50 ne ‘yan gudun hijira daga Najeriya aka ceto daga cikin daruruwan mutane dajamia’n tsaro na kasar Libiya da kuma kungiyar agaji ta kasa da kasa suka ceto daga cikin Teku.
‘Yan Najeriyar na cikin Jirgin Ruwan ne tare da wasu mutum 110 masu hijira. An ceto ne da wani Jirgin Ruwa mai lakabin Aquarius, wanda hukumar Likitoci marasa iyakar aiki (MSF), ke amfani dashi, mil 21 daga Yammacin yankin.
Jirgin zai kai ‘Yan gudun hijirar ne zuwa kasar Italiya, wanda suka hada da mata 18 sai yaro daya.Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewa fiye da rabin mutanen dake cikin Jirgin Ruwan ‘yan Najeiya ne, sauran kuma daga kasashen kusa da sahara sai mutum biyu ‘yan kasar Palastin.
Jami’an tsaro na kasar Libiya sun jajirce wurin tare Jiragen ruwa na ‘yan gudun hijira kafin su kaiga isa tashar manyan minyan Jirage na duniya da zasu shigar dasu Turai.
Source :naij hausa
Title :
Ankamo Wasu 'Yan Nijeriya A Sahara Zasu Gudu Turai
Description : Mutane a kalla 50 ne ‘yan gudun hijira daga Najeriya aka ceto daga cikin daruruwan mutane dajamia’n tsaro na kasar Libiya da kuma kungiyar a...
Rating :
5