Wata kungiyar matasan jam'iyyar adawa ta kasa watau Concerned Peoples Democratic Party Youths a turance sun fitar da gwamnan jihar Gombe takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2019 mai zuwa.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar matasan Malam Sani Bello ya fitar dauke da sa hannun sa a jiya Talata.
Jaridar naij ta samu cewa kungiyar ta bayyana gwamnan da yanzu haka yake da shekaru 55 a duniya kacal a matsayin wanda yafi kowa cancanta da ya shugabancin kasar nan musamman ma saboda irin yadda aka ga kamun ludayin sa a jihar ta Gombe.
A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa a jihar Kwara ta Peoples Democratic Party, Cif Iyiola Oyedepo ya sanar da cewa jam'iyyar ta sa ta karbi akalla magoya baya 800 daga jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress cikin 'yan kwanaki kadan da suka wuce.
Shugaban jam'iyyar dai Cif Iyiola shine ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da majiyar mu a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Juma'ar da ta gabata inda kuma ya bayyana cewa wani babban dan siyasa ne Dakta Hanfi Alabere ya jagoranci magoya bayan.
Source :naij hausa
Title :
Dankwambo Ne Kawai Zai Iya Maye Gurbin Buhari - Kungiyar Matasa
Description : Wata kungiyar matasan jam'iyyar adawa ta kasa watau Concerned Peoples Democratic Party Youths a turance sun fitar da gwamnan jihar Gombe...
Rating :
5