Mutanen Kano za su yi bore ganin yadda baki ke zuwa daga wasu Garuruwa su na karbe ayyukan su wanda ya kamata ace al’ummar Jihar ne su ka fi kowa amfana. Yanzu za a nemi Majalisa ta kawo dokar da za ta sa a fara daukar na gida tukuna a Jihar.
Labari ya zo mana daga Jaridar Vanguard cewa wata Kungiya ta ‘Yan Arewa sun shirya wani gangami da za su yi inda za su yaki yadda ake warewa wadanda ba asalin ‘Yan Jihar Kano ba ayyuka a Ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya a Jihar.Sani Salihu wanda shi ne Shugaban wata Kungiya a Kano yace kashi 70% na ayyukan da su ke Jihar su na karewa ne hannun wadanda su ka zo daga wasu wurare dabam.
Salihu yace da gan-gan ake sabawa dokar kasar na raba dai-dai kuma dole a gyara.
Shugaban wannan kungiyar yace bayan aikin Gwamnati, har sauran ayyuka a kamfanonin kasuwanci da sauran su, su na karewa ne a wajen bare don haka ya nemi hada kai da ‘Yan Majalisa da Malamai da sauran jama’a don kawo karshen wannan abu.
Source :naij hausa
Title :
Bamu Amince Abawa Wanda Ba Dan Garinmu Aikiba - Jama'ar Kano
Description : Mutanen Kano za su yi bore ganin yadda baki ke zuwa daga wasu Garuruwa su na karbe ayyukan su wanda ya kamata ace al’ummar Jihar ne su ka fi...
Rating :
5