Wani dan shekara 45 mai suna Shehu Ibrahim, tare da dan sa mai suna Farooq mai shekaru 22, sun shiga hannun hukuma bisa ga laifin sayar da kwayar Tramadol da Tramol ga yara ‘yan makarantun frimare da Sakandare a unguwar Itire na jihar Legas.
Hukumar yan Sanda ta 'Rapid Response Squad' na jihar Legas suka yi awon gaba da su a ranar Juma’a, bayan da wasu ma’aikatan hukumar Ilimi ta kai ko ke akan yanda yara ke shan kwayoyi a makarantu.
Inda bayan bincike da sa ido akan al’amuran yara aka yi nasarar kama masu saida masu, wanda aka same su da kwayoyin na Tramadol da Tramol har ma da wasu kalar kwayoyinIbrahim yayi musu akan maganar sayar wa yaran kwayoyi, shima dan nasa ya nuna bashi da masaniya a kan hakar inda ya ke cewa baban nasa yana sayarwa manya ne kawai da kwayar. Amma wani karamin yaro ya taba zuwa siya saidai shi bai sayar ma sa ba amma bai sani ba ko mahaifin nasa ya sayar masa daga baya.
Kwamishinan na ‘Yan Sanda, Edgal Imohimi, ya shawarci iyaye da ma’aikatan da su zama masu sa ido kan yaransu. Bayan nasarar da ya samu ta kara kama wasu ‘yan fashi da makami wanda suka kware a bangaren satar motoci, suna daukar motocin daga
Source :naij hausa
Title :
Ankama Wasu Gurba Tattun Uba Da Da A Legas
Description : Wani dan shekara 45 mai suna Shehu Ibrahim, tare da dan sa mai suna Farooq mai shekaru 22, sun shiga hannun hukuma bisa ga laifin sayar da k...
Rating :
5