Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne uban kasa sannan kuma yana iya ziyartan ko wani jiha a duk lokacin da ya yi ra’ayi.
Gwamna Ortom wanda yayi magana ta baki sakataren labaransa, Terver Akase ya bayyana cewa Benue na daga cikin yankin Najeriya sannan kuma yana iya ziyartan su.
Da aka tambaye shi ko gwamnati na farin ciki da ziyarar da kuma zaton su, Terver yace, “babu wani abu da zan fada sama da haka.“Shugaban kasar keda kasa sannan kuma yana iya ziyartan ko ina a duk lokacin da ya so.
”A baya jaridar Naij ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata ci gaba da karfafa alaka tare da hukumomin gargajiya a kasar domin samar da mafita mai dorewa ga rikicin makiyaya da manoma.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu a Jalingo.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Na Iya Ziyartan Duk Inda Yaso Akowani Lokaci-Ortom
Description : Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne uban kasa sannan kuma yana iya ziyartan ko wani jiha a d...
Rating :
5