Soyayyar Manzo kuma Annabin mu, Tsira da Aminci Allah su kara tabbata a gare shi da Ahalinsa, za ta ci gaba da kwaranya a zukatan musulmi da a yanzu ta zamto wata tabo a addinin Musulunci.
Wannan soyayya da musulmi ke bayyanawa ga Fiyayyen Halitta ta zarce soyayyar dake tsakanin su da Mahaifa, 'ya'ya da kuma rayuwar kawunan su, da hakan ya bambamta su da wadanda suka juya baya ga adinin.
Dalilin haka ya sanya maƙiya Addinin Islama ke fafutikar kai hari kan Manzon Tsira, inda suka yi yunƙurin sace Gawarsa daga Makwacinta dake Masallacin sa na birnin Madina a kasar Saudiyya.
Maruwaita tarihi sun bayyana cewa, anyi yunƙurin sace Gawar Fiyayyen Halitta har a karo uku, inda hari na farko ya afku a shekarar 557 bayan Hijirar sa daga birnin Makka zuwa Madina a yayin Halifancin Nur ad Din Mahmud Zanki.
Imam Muhammad Ibn Jarir Al-Tibri, ya bayyana yadda hari na uku ya afku a lokacin shugabancin Shamsu ad-Din Shawab Lamti a matsayin jagoran masu hidima ga masallancin Haram na Madina.
Takaitaccen tarihi ya bayyana cewa, a wani dare bayan sallar Isha'i, an kwankwashi Baab al-Salaam, daya daga cikin kofofin masallacin Annabi, bayan Shamsu ad-Din Shawab ya budi wannan kofa sai yayi kacibus da maharan su 40 dauke da fitilu da kayan aiki na rusau.
Shigar su ke da wuya cikin masallacin suka nufi Makwancin Tsarkakakken Halittu, wanda a wannan lokaci Mai jiya da yau da gobe ya zartar da buwayar sa, inda ƙasa ta tsage suka nutse cikin ta gaba daya.
Allah ya ƙara daukaka da darajar Annabi Muhammad, Tsira da Aminci su kara tabbata a gare shi da Ahalinsa.
Source :naij hausa
Title :
Wasu Mutane Sunyi Yunkurin Sace Gawar Fiyayyer Halitta Daga Makwancinsa
Description : Soyayyar Manzo kuma Annabin mu, Tsira da Aminci Allah su kara tabbata a gare shi da Ahalinsa, za ta ci gaba da kwaranya a zukatan musulmi da...
Rating :
5