1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Kannywood » Fina-Finan Kannywood 12 Dasuka Shahara A 2017

Fina-Finan Kannywood 12 Dasuka Shahara A 2017

By Unknown
Add Comment
Friday, 29 December 2017

Duk da babban kalubalen matsalar satar fasaha da masana'antar finafinan Kannywood ke fuskanta, amma an fitar da fina-finai da dama a cikin shekarar 2017, da suka kunshi masu kayatarwa da marar kyau da matsakaita.

Kuma kafin shekarar ta kawo karshe ana sa ran fitowar wasu sabbin fina-finai, kamar Juyin Sarauta, Sabon Dan Tijara, Dan Sarkin Agadaz, Mu Zuba Mu Gani, Dan Kuka a Birni da dai sauransu.

Don haka daya ko biyu daga cikinsu na iya shiga sahun Fina-finan 2017.

1. There's a Way

Ana ganin wannan ne Fim na Inglishi na farko a masana'antar Kannywood, wanda furodusansa shi ne babban malamin Ingilishi Kabiru Jammaje, sannan Falalu Dorayi a matsayin darakta.

Fim din ya bayar da labari ne akan gwagwarmaya tsakanin masu karamin karfi da attajirai.

An fito da halayyar wasu 'ya'yan attajirai a Jami'a da kuma rayuwar mata, wanda a haka aka tsara labarin.

Soyayya ce tsakanin Isham (Nuhu Abdullahi) Dan talaka amma hazikin dalibi da kuma Fadila (Hajara Jalingo) 'yar wani babban hamshakin attajiri Alhaji Mahdi (Sani Mu'azu) wanda ba ya kaunar hada zuri'a da talaka inda ya bi duk hanyoyin da zai bi domin ganin ya raba su.

Ana sa ran This is the Way, zai fito kafin karshen shekara. Raunin Fim din shi ne karshensa da kuma amfani da salon harshe mai sarkakiya.

Amma tsarin fim din baki dayansa ya kayatar wanda hakan martani ne ga sukar da ake wa masu shirya finafinan Hausa cewa jahilai ne, da ba su iya da turanci ba.

2. Umar Sanda

Kamal S. Alkali ne Daraktan Fim din, labarin ya mayar da hankali ne a kan mai ra'ayin rikau Umar Sanda (Ali Nuhu) da iyalinsa.

Ko da yake ma'aikaci ne, kuma yana kokarin ganin iyalinsa na cikin wadata. Ana zaman lafiya har zuwa lokacin da 'yarsa ta hadu da wani abokin karatunta Dan shugaban 'Yan sanda da aka shagwaba, wanda kuma ta kashe shi a kokarin kare kanta.

Umar Sanda ne ya binne gawar a yayin da 'yan sanda ke bincike mai tsauri.

Duk da cewa an kwaikwayi fim din ne daga wani fim na Indiya, amma yadda aka tsara shi zai iya kasancewa daya daga cikin mafi shahara a bana. Ya nuna girman gaskiya da hadin kai da dabi'u masu kyau.

3. Ankon Biki

Ali Gumzak ne daraktan Fim din, kuma Ankon Biki ya mayar da hankali ne a kan muhimmin batu da ake fuskanta a yanzu.

Mubarak (Adam Zango) da Fa'iza (Sadiya Bulala) suna shirin aure, sai Fa'iza ta kawo batun "Anko" da bukatar a hada wani babban bikin kasaita a wani wuri mai tsada.

Mubarak da abokansa sun yi iya kokarin ganin sun biya bukatar Amarya da kawayenta amma sun gagara, amma Amaryar ta dage a kan bukatar har ta bayar da kanta a madadin kudin kama wajen da za a yi bikin.

Ya fasa aurenta a ranar bikin bayan asirinta ya tonu, kuma a madadinta ya auri kawarta ta kud da kud. Fim din ya nuna girman nisan da wasu mata ke dauka don cimma bukatunsu.

Duk da yake wasu wuraren a fitowar fim din na da tsayi amma an yi amfani da Hausa mai kyau da salon magana.

Sauran taurarin fim din sun hada da Hafsar Idris da Umma Shehu da Al Amin Buhari da dai sauransu.

4.Rariya

Yaseen Auwal ne Daraktan Rariya, kuma fim na farko da Rahama Sadau ta dauki nauyin fitowarsa, wato matsayin furodusa.

Labarin Fim din ya danganta tasirin wayar salula ta zamani da ake kira "komi da ruwanka". Fim din ya shafi yadda wasu 'yan matan Jami'a ke amfani da wayar salula domin janyo hankalin maza.

Yadda aka hada fim din ya kayatar. Babban muhimmin abu shi ne yadda daya daga cikin 'yan matan ta banbanta da saura inda har ta yi kokarin kammala karatunta.

Mutane da dama ba za su so haka ba, musamman iyaye da ke da'awar karatun 'ya'ya mata. Amma duk da haka linzamin labarin ya shafi abin da ke faruwa kuma ke shafar jama'a.

Taurarin Fim din sun kunshi Ali Nuhu da Rabiu Rikadawa da Rahma Sadau da Fati Washa da Hafsar Idris da sauransu.

5.Mijin Yarinya

Ali Gumzak ne Darakta, kuma Mijin Yarinya ya shafi labarin wani Dattijo Attajiri Bashir Nayaya (Alhaji).

Wata rana ya ji matansa guda biyu da Allah bai ba su haihuwa ba suna ma shi addu'ar mutuwa domin gadon dukiyarsa kuma don su aure yara samari, su yi sabuwar rayuwa.

Saboda haka ne ya je ya auri budurwa Maryam Yahaya bayan ya saye imanin iyayenta da saurayinta da kudi.

Wannan ne ya fusata manyan 'ya'yansa Aminu Sharif da Sadiya Bulala, inda suka taya iyayensu mata kishi.

Bayan shafe lokaci ana makirci da takaddama, Alhaji ya yanke shawarar sakin dukkanin matansa, hadi da amaryarsa. Fim din na kunshe da darussa masu yawa a yadda aka tsara fim din.

Sabuwar 'yar fim Maryam Yahya ta yi kokari a fim din mai kunshe da gwanaye. Ba tare da zuzutawa ba fim din na cike da ban dariya da ilmantarwa.

6.Kalan Dangi

Wannan ma wani fim ne na barkwanci da Ali Gumzak ya bada umurni wato a matsayin Darakta, Fim din ya nuna yadda talakawa ke neman arziki da kuma attajirai.

Yayin da kuma masu arzikin ke kaskanta Talakawa. Ali Nuhu da Aminu Sharif da Sadiq Sani Sadiq da Jamila Nagudu da Fati Washa da Aisha Tsamiya na rayuwa ne ta nuna arziki da karya da makirci da nuna karfin iko. Idan kana neman nishadantarwa, to ka nemi Kalan Dangi.

Sai dai an raba fim din biyu, na daya da na biyu. Amma an takaita labarin da kuma karshensa, wanda ake sa ran fitarwa a shekara mai zuwa.

Kamar taken fim din Karshen Kalan Dangi zai iya kawo karshen duk wani rikici.

7.Makaryaci

Kamar sauran shahararrun fina-finan barkwanci da aka fitar a 2017, Ali Gumzak ne daraktan Makaryaci.

Sadiq Sani Sadiq ne da Allah ya ba basirar wasan kwaikwayo, ya daukaka fim din a matsayin daya daga cikin fitattu a bana. Labarin Fim din ya shafi yadda kwadayinsa na dukiya ya kai shi ga samun kudi ba tare da ya sha wata wahala ba.

Yakan je ya yi hayar tufafi ya harde cikin babbar motar mai gidan Rabiu Daushe ana tuka shi zuwa wurare har zuwa cikin Jami'a. Yakan yi wa dalibai karyar cewa shi dan gidan minista ne ko ambasadlakar

A hakan ne ya fara soyayya da daya daga cikin daliban Hafsat Idris. Ba tare da bin umurnin kakanninsa ba, ya je ya kadar da dabbobinsa na gado, domin ya kashe wa budurwarsa kudi wacce daga baya ta gano asalinsa.

Taurarin Fim din sun kunshi Sulaiman Bosho da Mama Tambaya da Mustapha Nabaruska da Musa Maisana'a da sauransu.

8.Husna ko Huzna

Husna (Jamila Naguda da Abdul (Adam Zango) sun shirya yin aure, yayin da kuma Huzna (Fati Washa) ta yi kokarin hana auren saboda matukar son da ta ke wa Abdul.

A yayin da suke hamayya, wata rana Husna ta watsa wa Huzna guba a fuska, ba tare da sanin cewa ashe fatalwa ce. Washegari Huzna ta tafi gidansu ta mallaki Husna.

Wannan ya bude wani sabon babin hamayya tsakaninsu inda Huzna ta shiga jikin Husna kuma ta ci gaba da zama a gidanta. Yadda aka tsara fim din ya ja hankali.

Amma duk da aoamu, n na iya zama daya daga cikin manyan fitattu finafinai a Kannywood.

Fim din dai bai kasance wani abin muni ga mata ba, kamar yadda aka tsara labarin fim din irin na ban tsoro, a rikicin rayuwar aure tsakanin mata don mallakar namiji.

Rawar da Washa ta taka ya kayatar. Falalu Dorayi ne Daraktan Fim din.

9.Burin Fatima

Wasu za su yi mamakin yadda wannan fim ya shigo sahun fitattu. Ya cancanta. Labari ne akan wata matar aure da ta fada tarkon shawarar kawarta.

Aisha Tsamiya tauraruwar fim din ita ce kuma ta dauki nauyin fitowarsa a matsayin furodusa.

Fim din ya ba da labarin wata mata (Tsamiya) da mijinta, Adam Zango a yayin da ta ke makaranta, wata kawarta ta ba ta shawarar ta zubar da juna biyu da take dauke shi don ta samu sukunin karatu.

Ta karbi shawarar kuma ta yi wa mijinta karya cewa cikin ya bare, ba tare da sanin cewa ba ta kara haihuwa ba. Ta fuskanci kalubale daga sarakuwarta kan rashin haihuwa inda ta tursasawa Zango ya kara aure.

Ali Gumzak ne ya bayar umurni a fim din da ba a kashewa kudi ba. Sannan bai samu karbuwa ba.

Amma ba don haka ba da zai kasance daya daga cikin finafinan da suka samu karbuwa ga jama'a. Wannan dai ci gaba ne ga Tsamiya, kasancewar fim dinta na farko a matsayin furodusa.

10.Mansoor

Fim din Mansoor na FKD yana cikin wadanda ake kururutawa a matsayin gwarzon shekara. Ali Nuhu ne Darakta.

An fara fim din ne da soyayyar wasu matasa daliban makaranta, Maryam Yahaya da Umar M. Sharif.

Amma mahaifin Sharif ne ya kawo karshen abotar, saboda yana zargin Sharif ba ya da uba, wanda wannan ya ba shi kwarin guiwar gudanar da bincike domin gano asalin mahaifinsa, ba tare da sanin cewa ashe gwamnan jiha ba ne mahaifinsa.

Labari ne ya mamaye fim din. Kuma ko shakka babu, fim din ya kasance kamar a zahiri. Baki dayan fim din ya shafi labarin matasan masoya tsakaninsu da iyayensu.

An aiwatar da fim din da kyau. Taurarin fim din sun hada da Ali Nuhu da Abba El Mustapha da Baballe Hayatu da Teema Yola da dai sauransu.

11. Dawo Dawo

Fim din Kabuwagawa ne wanda Ali Gumzak ya bayar da umurni.

Dawo-Dawo labari ne game da wasu da suka reni yaro (Adam Zango) tun kuriciya har girmansa inda suka kuma aurar ma shi da 'yarsu (Maryam Gidado).

Amma daren farkon aurensu, amaryar ta yi karyar cewa tana da aljannu, ta tursasa ma shi ya sake ta. Nan take iyayen suka daura ma shi aure da kanwarta (Aisha Tsamiya).

Ita kuma (Gidado) ta koma ga tsohon saurayinta (Zahraddeen Sani) wanda saboda shi ta kulla makircin. Daga baya ya yi watsi da ita, inda ta shiga wani hali ta koma kamar mahaukaciya lokacin da ta fahimci cewa ta dauke da cikin Zaharaddeen.

Fim din na cike da makirci da rikici, kuma taurarin fim din Zango da Tsamiya da Gidado suna yi kokari sosai. Wannan ya sa fim din ya sha gaban takwarorinsa a bana.

12. Ta Faru ta Kare

Aminu Saira ne daraktan Ta Faru ta Kare, labarin fim din ya shafi rayuwar Hafsat Idris, gurguwa, makauniya amma 'yar attajiri, da kuma Aminu Sharif (Momo) wanda ya aure ta kuma yake cin amanarta yana kawo 'yan matansa a gidanta har zuwa lokacin da dubunsa ta cika.

Inda Adam Zango, abokin wasanta wanda Momo ya yi wa kanwarsa ciki ya yake shi har ya fitar da shi daga gidan.

Fim din na tattare da nishadi. Hafsat Idris da ta fito mai nakasar jiki da kuma Momo sun yi kokari a rawar da suka taka a fim din.

Sauran taurarin fim din sun hada Hadiza Gabon da Hauwa Waraka da sauransu.

Source: BBC Hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Unknown at 08:38
In Kannywood
Fina-Finan Kannywood 12 Dasuka Shahara A 2017 Title : Fina-Finan Kannywood 12 Dasuka Shahara A 2017
Description : Duk da babban kalubalen matsalar satar fasaha da masana'antar finafinan Kannywood ke fuskanta, amma an fitar da fina-finai da dama a cik...
Rating : 5
Related Posts: Kannywood

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Fina-Finan Kannywood 12 Dasuka Shahara A 2017"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ▼  December (129)
      • Wasu Labarun Afirka Da Baku Saniba A 2017
      • Nada Matattu A Gwamnatin Buhari Rashin Iya Aiki Ne...
      • Tir:Ankama Uban Daya Shekara 20 Yana Lalata Da Yarsa
      • An Shiga Kwana Na Uku Ana Zanga Zanga A Iran
      • Bawanda Zaa Hukunta Saboda Nadin Matattu-Buhari
      • Kudaden Dana Kashe A Manchester Basu Isaba-Mourinho
      • Tsohon Danwasa Yazamo Shugaban Kasan Liberiya
      • Wayafi Samun Nasara A Gasar Premier Tsakanin Fergu...
      • Bana Tsoron Ficewar Sanchez Daga Kulob Dinnan Duk ...
      • Abubuwan Mamaki Takwas Na Kimiyya Dasuka Faru A 2017
      • Kamfanin Apple Ya Nemi Afuwar Abokan Huldansu
      • Fina-Finan Kannywood 12 Dasuka Shahara A 2017
      • Gobara Ta Hallaka Mutane 12 A Amirka
      • Aikin Agaji Yafara Kaiwa Ga Yara A Syria
      • Karanta Yanda Ake Cin Zarafin Matan Nijeriya A Fac...
      • Fursinoni 36 Sun Gudu Daga Gidan Yari
      • Gwamnati Ta Musanta Kai Dan Shugaban Kasa Asibitin...
      • Jonathan Ya Jajanta Wa Buhari
      • Dan Shugaba Buhari Ya Karye Sanadiyyar Hadarin Babur
      • Barayin PDP Ne Suka Kafa APC-Sule Lamido
      • Harry Kane Yawuce Messi Da Alan Shearer Cin Kwallaye
      • Ansawa Jami'an Koriya Ta Arewa Takunkumi
      • Ana Jigilan Marasa Lafia Zuwa Damascus
      • An Nemi Wata Mata Ta Biya $284 Kudin Wutan Lantarki
      • Obama Yayi Gargadi Kan Amfani Da Shafukan Sada Zum...
      • Liverpool Tasayi Virgil Van Dijk Daga Southampton
      • Mbappe Yace Ya Tattauna Da Madrid
      • Anci Kwallo 504 A Gasar Premier Ingila
      • Tunusiya Tahana Jiragen Emirate Sauka A Kasar Sabi...
      • Talakawa Na Matukar Kaunata-Buhari
      • Wahalar Rayuwa Ta Hana Kiristoci Ziyara Lokacin Ki...
      • Rikicin Kabilanci Ya Barke A Wani Yankin Abuja
      • Angano Gawar Wani Alkali Da Aka Sace A Saudiyya
      • Yawan Marasa Aiki Sunkaru A Nijeriya-Rahoto
      • Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram A Maiduguri
      • Yan Kannywood Sunzama Dankali Sha Kushe-Hadizan Saima
      • Trump Ya Yabi MDD Kan Takunkumin Koriya Ta Arewa
      • Wani Ya Kirkiri Injin Bada Wutan Lantarki
      • Yadda Zaayi Aiki Tareda Mata-Maza
      • Everton Tahana Chelsea Shanawa A Gasar Premier
      • Barca Ta Baiwa Madrid Tazarar Maki 14
      • Guguwa Ta Hallaka Sama Da Mutum Dari
      • Man City Taci Wasa 17 A Jere
      • Hamsik Ya Buge Tarihin Maradona
      • Motar Bas Tafado Daga Kan Gada A Indiya
      • Trump Ya Tari Aradu Da Ka
      • Mutum Miliyan Guda Nafama Da Kwalara A Yemen
      • Yadda Adam A Zango Ya Gagari Hukuma A Gwaska Return
      • Gobara Ta Kashe Mutum 29 Agun Motsa Jiki
      • Wani Yakashe Matan Dataki Aurensa a Indiya
      • Messi Zai Ziyarci Bernabeu A Wasan El-Classico
      • Ansace Mutum 10 Daga Jirgin Ruwansu A Niger Delta
      • Foden Yatafi Hutun Jinya
      • Amurka Tasha Kaye Agun MDD Kan Birnin Kudus
      • Yan Nijar Na Adawa Da Karin Haraji
      • Ina Sane Da Kasashe Dasuka Juya Mana Baya Kan Kudu...
      • Wenger Na Neman Daukan Fansa Akan Liverpool
      • Addinin Musulunci Baihana Binciken Kimiyya Ba-Haya...
      • Interpol Tayi Dirar Mikiya A Kasuwar Magani A Legas
      • Anraba Ma'aurata Bayan Shekaru 70 Tare
      • Majalisar Shari'ah Tasoki Buhari Kan Kin Zuwa Taro...
      • Dino Melaye Ya Fito A Wakar Hip Hop
      • Ankashe Wani Attajiri Da Matarsa A Canada
      • Fifa Ta Gargadi Spain Akan Zuwa Rasha
      • Muzamu Roki Buhari Yayi Takara 2019-Malami
      • Madrid Na Zawarcin Salah
      • Anyanke Ma Wani Sojan Nijeriya Hukuncin Kisa
      • Rashin Miji Babban Tashin Hankali Ne
      • Anyanke Wa Tsohon Ministan Hukunci Daurin Shekara ...
      • Tottenham Tasha Ruwan Kwallaye Agun City
      • Klitschko Ya Sayar Da Riginsa Naira Miliyan 78
      • Malika Sharewat Takasa Biyan Kudin Hayan Gida A Paris
      • Kunsan Kasan Da Beraye Ke Aikin Likitoci?
      • Kotu Ta Dakatar Da El-Rufai Daga Koran Malaman Fir...
      • Andakatar Da Zirga Zirgan Jiragen Sama A Babban Fi...
      • Anhana Wasan Wuta A Ghana Lokacin Kirismeti
      • Ankashe Musulmi 6,700 A Myanmar
      • Zaa Fara Shariar Magajin Garin Dakar Kan Almundahana
      • Ankori Yan Sanda Masu Fataucin Wiwi
      • An Gurfanar Da Maryam Sanda Da Mahaifinta A Kotu
      • Ministan Farin Ciki Ya Haddasa Bakin Ciki
      • Eric Bailly Yaji Rauni Sosai-Mourinho
      • Gwamnoni Sun Amince Akashe Dala Biliyan 1 Don Yaka...
      • Antuhumi Mourinho Akan Man City
      • Ana Zubar Da Ciki Miliyan 15 Kowani Shekara A Indiya
      • PDP Na Rarrashin Ya'yanta Dasuka Fusata
      • Turai Nada Hanu A Cin Zarafin Yan Ci Rani A Libya
      • Meyasa Baa Daina Wahalar Man Fetur A Nijeriya Ba?
      • Kane Yakusa Kai Alan Shearer Kwallaye
      • Saraki Zai Sake Shiga Kotu
      • Tsananin Sanyi Yasa Andage Wasan FA A Ingila
      • Madrid Na Harin Kofin Duniya Na Uku
      • Rashin Bin Dokane Ke Haddasa Rikici Tsakanin Manom...
      • Har Yanzu PDP Basu Hankalta Ba
      • Bikin Cikar Kaduna Shekara 100 Da Kafuwa
      • El Rufai Ya Tantance Har Masu Gadi Don Koyarwa
      • Ansauke Kwamadan Rundunar Yaki Da Boko Haram
      • Ronaldo Ya Doke Messi A Gasar Dan Kwallon Duniya
      • Ankarbe Wasan Kofin Turai Daga Brussels Zuwa Wembley
      • Wani Sauyi Ziyarar Buhari Kano Zai Haifar?
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger