1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Fasaha » Addinin Musulunci Baihana Binciken Kimiyya Ba-Hayat Al-Sindi

Addinin Musulunci Baihana Binciken Kimiyya Ba-Hayat Al-Sindi

By Unknown
Add Comment
Wednesday, 20 December 2017

Ba kasafai aka faye samun mace musamman musulma ba da ta yi nisa sosai a bangaren kimiyya.

Sai dai Hayat Al-Sindi, wadda 'yar asali kuma haifaffiyar kasar Saudiyya ce, ta ciri tuta a wannan fanni.

Hayat Al-Sindi ta kuma kasance mai bai wa shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmai, Islamic Development Bank, IDB, shawara kan kimiyya da fasaha.

A hirarta da Halima Umar Saleh, ta shaida mata cewa ta taso da son kimiyya ne tun tana karama, kuma ba ta taba cin karo da wani abu da ya saba da addininta ba a wannan bangare.

Kazalika ta fadi irin hobbasar da bankin ke yi don tallafawa mata a kasashen musulmai.

Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:

Tambaya: Me ya ja hankalinki wajen zama gogaggiya a fannin kimiyya tun farko?

Amsa: Wannan tambaya ce mai kyau. Abun ya faro ne a lokacin da nake da shekara biyar. Kimiyya na matukar ban sha'awa.

Ina tuna lokacin da nake da wani dan karamin kati da nake wasa da shi, wanda ake iya duba yanayin dare da sararin samaniya. To wannan ya kan sani tunanin duniyar da samaniya da abun da zai faru nan gaba.

Kuma na yi sa'a ina da mahaifin da ke koya min duk abun da nake so. Don haka ya taimaka min kwarai wajen bani labaran masanan da suka yi wa al'umma wani abu na bajinta ta bangaren lafiya da adabi da kuma ilimin kimiyyar Physics.

Kuma ina karanta littatafan manyan masana kimiyya da ma na malaman musulunci irinsu Ibn Sina da Jabir bn Hayyan. Kuma gaskiya ni su ne gwarazana.

Tambaya: Wasu lokutan idan mutum musamman musulmi ya yi nisa a fannin kimiyya, ya kan ci karo da wasu batutuwa masu sarkakiya da suka yi hannun riga da addininsa, kuma za su iya saka masa shakku. Ganin cewa ke musulma ce da ta fito daga cibiyar musulunci wato Saudiyya, ko kin taba cin karo da wani abu a kimiyya da ya saba da addininki?

A gaskiya a lokacin da na bar kasata don zuwa Ingila don karantar kimiyya, ina jin duk duniya ta yi amanna cewa kimiyya ta yi hannun riga addini, sai dai ba haka abun yake ba a musulunce, saboda a musulunci ayoyin Al-kur'ani da dama da hadisan Manzon Allah SAW, sun ba mu kwarin gwiwa mu kirkiri wani abu, mu yi bincike a kansa, mu yi sharhi, mu kuma yi tambaya a kansa.

Amma a kasashen yamma suna ganin kamar kimiyya ta yi hannun riga ne da addini.

To ni a ganina idan muna kimiyya ba wai za mu yi bincike kan wanene ya samar da wani abu ba, kamata ya yi mu yi bincike kan dalilin da ya sa aka samar da abun, ta haka ne za mu kasance cikin wadanda suka yi nasarar gano wani abu, ba wai batun waye ya yi halitta ba, Allah ne ko kuwa komai samuwa ya yi haka nan.

Idan mutane ba su gane ba, ya kamata mutum ya yi musu bayani cewa idan mutum yana da addini hakan ba zai hana shi kirkiro abubuwa ba, kamar misali Elbert Einstein,Bayahude ne amma kuma masanin kimiyya.

Don haka ni dai a bangarena, addinina da al'adata ba su hanani yin binciken kimiyya ba.

Kuma a al'adar kasashen yamman ma ba wai suna nufin idan kana da addini shi kenan kuma ba za ka shiga cikin al'amuran kimiyya ba.

Babban abun da ake bukata shi ne ka gano mece ce kimiyya, ka yi binciken me ya sa aka samar da abu kaza ta hanyar da abun yake. Don haka ina ganin za ka ilimintar da mutane ne idan ka yi binciken da ya kamata.

Wasu mutanen sun sha gaya min cewa ba zan iya kimiyya ba saboda yadda nake rufe jikina suna ganin kamar ba zan sake ba wajen yin bincike, amma ni na san a addinina da al'adata ba haka ba ne, abun da nake bukata shi ne na yi bincike, na yi tambayoyi don gano abun da nake son ganowa.

Tambaya: Bari mu dawo kan batunwajen aikinki na bankin IDB, wanne irin kalubale mata ke fuskanta a kasashen Musulmai,kuma wane taimako bankin IDB ke ba su?

Amsa: Wannan tambaya ce mai kyau. A gaskiya mata kan fuskanci matsaloli a ko wanne yanki na duniya, sai dai matsalolin sun sha bambam daga yanayin al'adun ko wacce kasa.

Muna da mata da suke aiki kuma suna fuskantar matsaloli har ta bangaren kimiyya da fasaha ma kamar a Amurka da Turai da Afirka da Gabas Ta Tsakiya.

Kuma muna kokarin magance matsalolin da mata ke fuskanta ne a kasashen Musulmai ta hanyar shigo da mata cikin al'umma ta hanyar ba su abubuwan da suke bukata da kuma ba su damar da ta dace.

Idan ki ka duba, mata sun fi maza tagomashi a fannin kimiyya da fasaha ba wai don ina nufin maza ba su iya ba. Kuma ko da mun tallafawa al'umma to muna kuma tallafawa mata daban.

Kuma a yanzu muna da wani sabon shiri a IDB ta yadda za mu karfafawa mata su zama injiniyoyi masu nazarin hasken rana, da kuma tallafa musu da kayan aikin da suke bukata har ma a yankunan karkara da ba su da isasshen ilimi ta yadda za su bunkasa su ma.

Mun kuma gano cewa idan ka tallafawa mace daya to tamkar ka tallafawa dukkan karkarar ne, saboda shi namiji idan ka tallafa masa to daga baya barinka zai yi ya je ya nemi wani aikin a wani wajen daban.

Saboda shi haka Allah ya yi shi yana bukatar yin gogayya da neman wani aikin da ya fi wanda yake yi.

Amma mata suna da jajircewa da tsayawa kan aikin da suka fara, kuma manyan masu kawo sauyi ne a al'umma, su kan koyar da maza da mata, kuma suna iya fara wata hobbasa don samar da wani abu na kimiyya.

Don haka IDB ya yarda kwarai da karfafawa mata saboda yana daga cikin al'adar al'umma a taimakawa mata.

Kuma za a yi hakan ne ta hanyar samar musu da hanyoyin da suka dace da damarmaki, sannan kuma dole a fahimci irin al'ummar da suka taso a ciki da al'adarsu da kuma girmama al'adar tasu da addininsu.

Kuma a samar musu da wadannan abubuwa a cikin al'ummarsu saboda abu mafi kyau da za a iya shi ne a ba su abubuwan da suka dace, sai a bar su su yi amfani da abubuwan ta yadda suke ganin ya fi dacewa a al'ummarsu, ba wai sai lallai an tilasta musu yin wani abun da al'adarsu ba ta yarda da shi ba kamar ilimi ko koya musu dabaru, a dai ba su kayan aikin sai a ga yadda za su yi amfani da nasu dabarun wajen yin abun da ya dace wanda zai amfani al'ummarsu.

Sannan kuma muna bayar da tallafin karatu ga mata da sanya kyaututtuka da samar musu da damarmaki da koyar da su salon shugabanci.

Tallafin karatun kuwa sun hada har da yin digiri na biyu da digirin-digirgir a kowanne fanni musamman ma fannnin injinya,saboda shi ne fannin da har yanzu ba mu da mata da yawa da suka kware kuma muna bukatar tallafawa mata ta wannan fannin saboda muna bukatar baiwarsu da kulawarsu.

Kuma ina so na bayar da misali, a lokacin da aka kirkiri balam-balam din da ke kare mutum a yayin da hadari ya afku a cikin mota, wato Airbag, yawancin wadanda suke da hannu a kirkirar maza ne, don haka sun kirkire ta ne kawai don maza a bangaren zaman direba, har sai zuwa lokacin da aka samu mace cikinsu sannan ta yi tunanin cewa ya kamata a yi wata balam-balam din a wajen zaman na kusa da direba.

Don haka muna bukatar mata da maza a kimiyya amma ko wanne da bangarensa. Don haka muna bukatar karfafawa mata sosai, muna da bukatar nuna damuwa ga matsalar mata da halin da suke samun kansu a ciki don kuwa wadannan manyan abubuwa ne da za su taimaka wajen ciyar da al'umma gaba.

Tambaya: Shugabanni daga kasashe daban-daban na neman tallafi daga IDB, amma a lokuta da dama tallafin ba ya kai wa ga matan da suke karkara a wadannan kasashe. Ta yaya ku ke tabbatar da cewa irin wannan tallafin ya isa gare su?

Amsa: Wannan matsala a gaskiya tana faruwa ba ma ga mata kawai ba, ana bayarda tallafi har ma ga mabukata amma ba zai kai wajensu ba.

Ana bayar da tallafin maganuguna da na abinci amma a wasu lokutan ba ya kai wa wajensu. Don haka a kokarin ganin tallafin ya cimma al'umma dole sai an bi matakan IDB na karfafawa mutane gwiwa.

Don haka muna kokarin ganin mun yi aiki tare da hada gwiwa da al'ummar da muke son tallafa kai tsaye da kuma jagororinsu. Don haka ba wai zuwa muke kai tsaye mu bai wa matan taimako ba, dole sai mun bi ta hannun shugabannin al'umma da duk wadanda suka dace.

Kuma na tabbata ko wanne shugaba zai so ya yi wa al'ummarsa abun kirki don haka dole mu yi aiki da su.

Don haka a yanzu muna aiki tukuru don samar da wata kafa ta intanet da za ta hada dukkan masu ruwa da tsaki don gano hukumomin gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba da 'yan kasuwa wadanda za mu iya aiki da su don sanin hanyoyin da za a bi a yi aikin tare don kai wa gaci, ta yadda a duk lokacin da muke wani babban aiki za mu hada kai tare da su don samun nasara da kuma amfanar dukkan al'umma.

Source: BBC Hausa

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Unknown at 23:26
In Fasaha
Addinin Musulunci Baihana Binciken Kimiyya Ba-Hayat Al-Sindi Title : Addinin Musulunci Baihana Binciken Kimiyya Ba-Hayat Al-Sindi
Description : Ba kasafai aka faye samun mace musamman musulma ba da ta yi nisa sosai a bangaren kimiyya. Sai dai Hayat Al-Sindi, wadda 'yar asali kum...
Rating : 5
Related Posts: Fasaha

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Addinin Musulunci Baihana Binciken Kimiyya Ba-Hayat Al-Sindi"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ▼  2017 (1438)
    • ▼  December (129)
      • Wasu Labarun Afirka Da Baku Saniba A 2017
      • Nada Matattu A Gwamnatin Buhari Rashin Iya Aiki Ne...
      • Tir:Ankama Uban Daya Shekara 20 Yana Lalata Da Yarsa
      • An Shiga Kwana Na Uku Ana Zanga Zanga A Iran
      • Bawanda Zaa Hukunta Saboda Nadin Matattu-Buhari
      • Kudaden Dana Kashe A Manchester Basu Isaba-Mourinho
      • Tsohon Danwasa Yazamo Shugaban Kasan Liberiya
      • Wayafi Samun Nasara A Gasar Premier Tsakanin Fergu...
      • Bana Tsoron Ficewar Sanchez Daga Kulob Dinnan Duk ...
      • Abubuwan Mamaki Takwas Na Kimiyya Dasuka Faru A 2017
      • Kamfanin Apple Ya Nemi Afuwar Abokan Huldansu
      • Fina-Finan Kannywood 12 Dasuka Shahara A 2017
      • Gobara Ta Hallaka Mutane 12 A Amirka
      • Aikin Agaji Yafara Kaiwa Ga Yara A Syria
      • Karanta Yanda Ake Cin Zarafin Matan Nijeriya A Fac...
      • Fursinoni 36 Sun Gudu Daga Gidan Yari
      • Gwamnati Ta Musanta Kai Dan Shugaban Kasa Asibitin...
      • Jonathan Ya Jajanta Wa Buhari
      • Dan Shugaba Buhari Ya Karye Sanadiyyar Hadarin Babur
      • Barayin PDP Ne Suka Kafa APC-Sule Lamido
      • Harry Kane Yawuce Messi Da Alan Shearer Cin Kwallaye
      • Ansawa Jami'an Koriya Ta Arewa Takunkumi
      • Ana Jigilan Marasa Lafia Zuwa Damascus
      • An Nemi Wata Mata Ta Biya $284 Kudin Wutan Lantarki
      • Obama Yayi Gargadi Kan Amfani Da Shafukan Sada Zum...
      • Liverpool Tasayi Virgil Van Dijk Daga Southampton
      • Mbappe Yace Ya Tattauna Da Madrid
      • Anci Kwallo 504 A Gasar Premier Ingila
      • Tunusiya Tahana Jiragen Emirate Sauka A Kasar Sabi...
      • Talakawa Na Matukar Kaunata-Buhari
      • Wahalar Rayuwa Ta Hana Kiristoci Ziyara Lokacin Ki...
      • Rikicin Kabilanci Ya Barke A Wani Yankin Abuja
      • Angano Gawar Wani Alkali Da Aka Sace A Saudiyya
      • Yawan Marasa Aiki Sunkaru A Nijeriya-Rahoto
      • Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram A Maiduguri
      • Yan Kannywood Sunzama Dankali Sha Kushe-Hadizan Saima
      • Trump Ya Yabi MDD Kan Takunkumin Koriya Ta Arewa
      • Wani Ya Kirkiri Injin Bada Wutan Lantarki
      • Yadda Zaayi Aiki Tareda Mata-Maza
      • Everton Tahana Chelsea Shanawa A Gasar Premier
      • Barca Ta Baiwa Madrid Tazarar Maki 14
      • Guguwa Ta Hallaka Sama Da Mutum Dari
      • Man City Taci Wasa 17 A Jere
      • Hamsik Ya Buge Tarihin Maradona
      • Motar Bas Tafado Daga Kan Gada A Indiya
      • Trump Ya Tari Aradu Da Ka
      • Mutum Miliyan Guda Nafama Da Kwalara A Yemen
      • Yadda Adam A Zango Ya Gagari Hukuma A Gwaska Return
      • Gobara Ta Kashe Mutum 29 Agun Motsa Jiki
      • Wani Yakashe Matan Dataki Aurensa a Indiya
      • Messi Zai Ziyarci Bernabeu A Wasan El-Classico
      • Ansace Mutum 10 Daga Jirgin Ruwansu A Niger Delta
      • Foden Yatafi Hutun Jinya
      • Amurka Tasha Kaye Agun MDD Kan Birnin Kudus
      • Yan Nijar Na Adawa Da Karin Haraji
      • Ina Sane Da Kasashe Dasuka Juya Mana Baya Kan Kudu...
      • Wenger Na Neman Daukan Fansa Akan Liverpool
      • Addinin Musulunci Baihana Binciken Kimiyya Ba-Haya...
      • Interpol Tayi Dirar Mikiya A Kasuwar Magani A Legas
      • Anraba Ma'aurata Bayan Shekaru 70 Tare
      • Majalisar Shari'ah Tasoki Buhari Kan Kin Zuwa Taro...
      • Dino Melaye Ya Fito A Wakar Hip Hop
      • Ankashe Wani Attajiri Da Matarsa A Canada
      • Fifa Ta Gargadi Spain Akan Zuwa Rasha
      • Muzamu Roki Buhari Yayi Takara 2019-Malami
      • Madrid Na Zawarcin Salah
      • Anyanke Ma Wani Sojan Nijeriya Hukuncin Kisa
      • Rashin Miji Babban Tashin Hankali Ne
      • Anyanke Wa Tsohon Ministan Hukunci Daurin Shekara ...
      • Tottenham Tasha Ruwan Kwallaye Agun City
      • Klitschko Ya Sayar Da Riginsa Naira Miliyan 78
      • Malika Sharewat Takasa Biyan Kudin Hayan Gida A Paris
      • Kunsan Kasan Da Beraye Ke Aikin Likitoci?
      • Kotu Ta Dakatar Da El-Rufai Daga Koran Malaman Fir...
      • Andakatar Da Zirga Zirgan Jiragen Sama A Babban Fi...
      • Anhana Wasan Wuta A Ghana Lokacin Kirismeti
      • Ankashe Musulmi 6,700 A Myanmar
      • Zaa Fara Shariar Magajin Garin Dakar Kan Almundahana
      • Ankori Yan Sanda Masu Fataucin Wiwi
      • An Gurfanar Da Maryam Sanda Da Mahaifinta A Kotu
      • Ministan Farin Ciki Ya Haddasa Bakin Ciki
      • Eric Bailly Yaji Rauni Sosai-Mourinho
      • Gwamnoni Sun Amince Akashe Dala Biliyan 1 Don Yaka...
      • Antuhumi Mourinho Akan Man City
      • Ana Zubar Da Ciki Miliyan 15 Kowani Shekara A Indiya
      • PDP Na Rarrashin Ya'yanta Dasuka Fusata
      • Turai Nada Hanu A Cin Zarafin Yan Ci Rani A Libya
      • Meyasa Baa Daina Wahalar Man Fetur A Nijeriya Ba?
      • Kane Yakusa Kai Alan Shearer Kwallaye
      • Saraki Zai Sake Shiga Kotu
      • Tsananin Sanyi Yasa Andage Wasan FA A Ingila
      • Madrid Na Harin Kofin Duniya Na Uku
      • Rashin Bin Dokane Ke Haddasa Rikici Tsakanin Manom...
      • Har Yanzu PDP Basu Hankalta Ba
      • Bikin Cikar Kaduna Shekara 100 Da Kafuwa
      • El Rufai Ya Tantance Har Masu Gadi Don Koyarwa
      • Ansauke Kwamadan Rundunar Yaki Da Boko Haram
      • Ronaldo Ya Doke Messi A Gasar Dan Kwallon Duniya
      • Ankarbe Wasan Kofin Turai Daga Brussels Zuwa Wembley
      • Wani Sauyi Ziyarar Buhari Kano Zai Haifar?
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger