1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kazamar Gida Part 6

Kazamar Gida Part 6

By Abdul Mk
Add Comment
Monday, 9 November 2015
Rayuwar Jafar da Siyama sai godiyar Allah domin a kashi d'ari na k'azantarta,ta rage ashirin. Har lokacin dai shine mai yiwa kanshi gyaran d'aki da band'aki. Tun wata rana da tace ya bar mata zatayi. Dadi ya cikashi ya cire mukullayen daya had'asu dana mashin d'insa ya damk'a mata. Saidai fa ya dawo yaga ba daidai ba,domin saika ka rantse yarinya mai shekaru goma tayi gyaran,k'asan ma sai k'arni,da yayi magana tace ai daga mopper d'inne. Band'akin ma tashin k'arni yake,nan ma tace ita kam batasan matsalar ba. (Alhalin Dauda ne mai wankin toilet d'in).
Tun ranar ya daina bar mata mukullayensa acewarsa nauyi yayi nata yawa ga ciki ga ayyuka? Hakan yayi mata dad'i,har ma alokacin ta kasa b'oye farin cikin nata.
Watarana suna zaune a falonta,Siyama tana kwance tayi matashi da cinyarsa tana game d'in Candy Crush a wayarta. A hankali kuma yake shafa gashinta yana bin d'akin da kallo. Ya dubi sama yanda yaga Yana ta cika d'akin. Girgiza kansa yayi ya dubeta
"Siyama na tambayeki mana."
Ta dubeshi alamar tana saurare
"A gida bakya yiwa Hajiya aikin komai ne?"
Ta tab'e baki tana girgiza kanta
"Gaskiya Hajiya bata sanyani aiki,komai sai 'yar aikinta ce takeyi. Sannan kaima shaida ne batason bacin raina,koda an sanyani wani aikin girkin,musammanma yaya hanif yafi kowa matsamin anan bangaren. Matukar na b'ata raina Hajiya sai tace nayi zama na. Sukan yawaita yin fad'a da Hajiya akan ta hanani koyon aiki musamman girki wai wannan ba yi bane. Amma Hajiya saita bud'e mishi wuta. Akwai sadda Hajiya ta fita unguwa,Abba ya shigo ya hangi Saude a kicin tana fama da girkinsa. Ya k'araso d'akin Hajiya ya iskeni ina chatting. Wallahi Jafar saida ya zanemin jikina,sannan yace daga wannan ranar kada na k'ara tsallakewa har a gama aikin abinci bai ganni a kicin d'in ba.
Tun daga ranar na soma jagwalgwalawa har na iya kad'an kad'an,don sai naji muryar Abba nake fad'awa kicin d'in.
Kafin auren su anti rumaisa,sune masu yiwa Hajiya gyara sai bayan anyi musu ne Saude keyi. Hum,a wannan lokacin Hajiya shiyasa tafiso nayi aure da wani mai kudin wanda acewarta saidai ina kwance ayimin kowace hidima."
Jafar ya jinjina zancen bayan ta kammala,
"Ke kuma kika nace sai talaka ko?"
Ta muskuta tana duban fuskarta
"Kaima kasan alokacin ko yankani za'ayi,bazan fasa sonka ba."
Yayi murmushi kawai.
********
Misalin takwas na dare sukaci kwalliya ya dauketa a mashin sai gidan Haris. Dayake sun san da zuwansu,suna isowa Haris ya fito ya tarbesu da murna. Ya dubi Siyama
"Amarya munyi maki fushi."
Tayi dariya "Ayi hakuri,kaga mai laifi nan."
"Kuma fa gaskiyane. Ku k'araso mana."
Suka shiga,kamshi mai dad'i ya bugi hancinsu. Komai tsaf yake gwanin sha'awa. Yaron Haris mai suna Aliyu yana rarrafe abinsa. Jafar ya d'agashi cak yana mishi wasa sai b'angala dariya yakeyi. Yana son yaron,ji yake tamkar shine ya haifeshi. Haris yayi ciki yana kira
"Ummina! Ummina!!"
Jafar ya saci kallon Siyama wacce ke k'arewa gidan kallo cike da sha'awa. Ita kanta komai na falon ya burgeta,saidai ta soma tunanin Kawai don Ummin ta kasance 'yar gidan masu hannu da shuni shiyasa falonta ya k'awatu batasan cewa gyara ma wani abun bane!
Suka dawo tare da Ummi. Matashiya ce bata wuce shekarun Siyama ba,ashirin da biyar. Taci ado cikin doguwar rigar nan ta kanti 'yar yayi. Fuskarta ba wata kwalliya tayi ba daga hoda sai lipgloss data sanya amma tayi kyau. Tana murmushi ta zauna kusa da Siyama daidai lokacin da Jafar ke zolayarta
"Uwargidan Rahma."
Ummi ta harareshi tana dariya
"Wacece Rahma? Na gayamaku bana kishi da ita."
Haris da Jafar sukayi dariya,Jafar yace
"A'a fa maman Aliyu,kada fa kiga abu ya tashi gadan gadan ki nuna bakisan zance ba."
Ummi ta tab'e baki had'e da dariya
"Ai na gayamaka ko Albarka ne sunanta ni Ummi bata gabana. Yaje yayi aurensa mana. Nidai ka gayamasa kada ma ya had'ani da ita zaman gida d'aya."
"Ballantana ma ba auren nayi niyyar yi ba."
Haris yayi saurin fad'a cike da fargaba. Ya tuna farkon ranar da ta daga wayarsa yana band'aki jin mai kiran tace rahma ce, a daren basu kwashe da dad'i ba.
Ummi dai ta mik'e tana jan hannun Siyama
"Ku kuka sani, nidai na fadamaku sharad'ina amma ban hanaku aurenku ba. Kawata zo muje ciki ko?"
Jafar wanda ke dariyar mugunta ba tare da ya lura da hararar da Haris ke watso mishi ba yace
"Toh bari nayi mishi rakiya zance."
Bata ce uffan ba,haushin Jafar duk ya cikata. Ummi itama fa akwai kishi.
Suna shigewa,haris ya kai mishi duka
"Kaidai anyi d'an iska,wallahi yau fa ka had'amin bomb. Shikenan yau za ayimin bore."
Suka sanya dariya
"Ai gwara dai ka fad'a mata tun abu baizo ya kankama ba."
Haris ya girgiza kanshi cike da damuwa
"Nifa ina ganin na fasa auren nan tunda Ummina bataso na hakura. Ranar nan nake gayamaka kada kaso kaga da yanda muka shirya da ita."
Jafar ya girgiza kansa ya zama serious
"Ba don raya sunna kakeson yi ba dana baka shawarar ka hakura. Kai bari na fadamaka,kaga Siyama ta isheni a rayuwa. Banga wata a duniya da zata isheni kallo ba. Koda Allah Ya kaddaro zan k'ara aure ko?"
Ya tab'e baki yana girgiza kansa
"Badai don inaso ba,sai don KADDARA."
Haris yayi murmushi
"Nikam son Rahma nakeyi. Jafar ni kaina koda a mafarki ban taba zaton bayan Ummi zanso wata d'iya mace ba,duba dai ka gani. Ummi bata rage a komai ba,tana da tsafta ladabi da biyayya. Tana bani kulawa sosai da sosai,kawai dai a lokaci guda Allah Ya sanyamin kaunar Rahma a zuciyata."
Jafar ya jinjina kansa,shima fatansa Allah Yasa matarsa ta gyara d'abi'unta. Babu laifi dai a yanzu ana kokarin bashi hakkinsa,ana kulawa dashi,saidai har yanzu tsaftar ragaggiya ce ba kad'an ba.
Sukayita hira abinsu.
A d'aki ma Ummi albums na biki dana sunan Aliyu ta ajiyewa Siyama. Tana kallo suna hirarsu. Can Ummi ta fito ta jera abinci akan kafet bayan ta shimfida leda.
Suka had'u gaba daya,sai lokacin ummi ta sakarwa Jafar har suna dariya don d'azun ma kishi ne.
Basu bar gidan ba sai goma da mintoci na dare. Siyama ta samu alheri mai yawa a wajen Ummi dana sutura dana kaya! Tayi godiya sosai,suka rakosu har wajen mashin d'in Jafar sannan suka koma ciki.. !
**
Ladi tana daga cikin d'an d'akin da suke ajiye kayayyakin kwanukansu da tukwane harma da sauran tarkacensu na girki,kamar daga sama taji muryar Jafar suna gaisawa da Mama. Tayi wuf ta fito har tana kokarin fad'uwa. Suna had'a ido ta sauke ajiyar zuciya tana murmushin farin ciki. Kamar bashi ba,yayi y'ar k'iba.
Jafar yana dariya yace
"Yar nijar kwana biyu?"
Ladi fuska a sake ta gaidashi,taji dad'in ganinshi har ma ta kasa b'oyewa. Bayan sun gaisa tace
"Yayana ai kaine ka b'uya,shiru ba'a ganinka."
Jafar ya shafi sumar kansa
"Ya za'ayi,sai a hankali. Yau ai ganinan ko? Ya karatun?"
Ta d'ago ta dubeshi tana murmushi
"Karatu alhamdulillah gashi muna ta shirye shiryen zana jarrabawar karshe na sakandire. A sanyamu a addu'a."
Ya bud'e baki
"Ikon Allah,yanzu Ladi har zaki kammala sakandire? Kina kankanuwa dake?"
Taji babu dadi,ita fa bata daukar kanta a yarinya kwata kwata. Saidai gaskiyarsa,shekaru sha bakwai ai dole a kirata yarinya. Ta wayance da dariya cikin marairaicewa tace
"Yayana shekaruna sha bakwai fa."
"Oh kina nufin kicemin kin girma ko?"
Ya k'arashe yana dariya. Itama dariyar tayi ta mike
"Oh yayana,nikam bance ba. Za'a kawo wani abu ne?"
Yana murmushi yace
"Bani favourite d'ina saidai fa bada yawa ba."
Cike da farin ciki ta juya,Mamanta tana ta aikin zuba abinci a farantai ta sanar mata yanason tuwo. Kafin mama ta zuba ta mik'awa masu zaman jira nasu sannan ta koma ta karb'o mishi. Duk abunda takeyi idanuwanta bini bini suna gareshi. Hankalinsa yana kan wayarsa har ta dawo ta ajiye mishi. Yayi godiya. Ta koma ta zauna anan wajen Mama. Tana yi tana satar kallonshi daga ta lura zai kallo inda take sai tayi saurin maida kanta ga kwanukan dake gabanta. Can jimawa kuma ta k'ara kallonshi.
Mama tana lura da ita,murmushi kawai tayi cike da tausayin Hadiyya. Lallai kam ta fad'a son maso wani wanda k'arshensa bai fiye zama mai dad'i ba.
Sai bayan Jafar yayi musu sallama zai tafi ne,tayi saurin bin bayanshi. Mamanta ta bita da kallo tana mai mamakin me kuma ladi zata gayamasa? Fargabarta kada ya zamto zata ce sonshi takeyi,amma idan hakane bata kyautawa kanta ba.
Ita kuwa Ladi saida ta bari sun matsa kad'an daga shagon tace
"Yayana daman cewa zanyi ko zaka bamu lambarka,kaga daka jima baka lek'omu ba duk mun damu saidai sanin da mukayi kana da iyali bamu takura ba. Inda hali ko zaka bamu lambarka sai a dunga gaisawa wataran saboda irin haka ko?"
Jafar bai kawo komai ba,murmushi yayi yace
"Kuma nima nayi wannan tunanin,naso sanin gidanku sadda Mama tayi rashin lafiya. Allah baiyi ba."
Ya karb'i wayarta,'yar Nokia ce k'arama "express music" secondhand ce. Ya shigar da lambobinsa ya mik'a mata yana murmushi
"Gashinan 'yar nijar."
Tayi godiya,sukayi sallama yayi kasuwa.
Mama ta dubeta cike da zargi,Ladi ta sakar mata murmushi.
"Me kikace mishi?"
"Bakomai fa mama,lambarsa kawai na karb'a saboda irin haka idan ya tafi mukaji shiru kinga ai da dad'i muji ko lafiya, ko?"
Mama ta tab'e baki,suka cigaba da aikinsu.
*********
yanxu akapara..!
Please like Us On   Facebook
Follow us on   Twitter


Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 14:27
In Hausa Novels
Kazamar Gida Part 6 Title : Kazamar Gida Part 6
Description : Rayuwar Jafar da Siyama sai godiyar Allah domin a kashi d'ari na k'azantarta,ta rage ashirin. Har lokacin dai shine mai yiwa kansh...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kazamar Gida Part 6"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ▼  November (308)
      • Kafin Kayi Barci
      • Yanda Ake Hada Lemon Juice
      • Yan Boko Haram Sun Sace Wasu Mata A Banburaitai
      • Photos: Buhari Ya Isaa Paris Dan Halartar Taron Sa...
      • Ana Ta Samun Nasarar Kwato Shanun Sata a Kano
      • Zargin Kinshiyoyin Ta Sun Mata Asiri
      • Al'ajabi Part 16
      • Hisbah Ta Kama Wani Dan Sanda Da Yi Wa Budurwa Ciki
      • An kaiwa 'yan Shi'a hari a Masallaci a Bangaladash
      • Video: Download Highlight Leicester City 1 Manches...
      • Video: Download Highlight Barcelona 4 Real Sociedad 0
      • Yanda Ake Hada Cake
      • Photos: Yusuf da Zahra Buhari Su Halarci Taron Yay...
      • Photos: Sabin Hotuna Shahida Sanusi Lamido Sunusi
      • Buhari Ya Nada Sabun Alkalai
      • Al'ajabi Paart 15
      • Yan Boko Haram Na Shirin Kaima Abuja Hari
      • Mummunar Shiga Mai Bayyana Tsaraici Da Yan Uwa Mat...
      • New Music: Inda Rai Darabo By Hussaini Danko
      • Graphic Photos :Adadin Mutanen Da Su Ka Rasu A Har...
      • Photos: Gwamna Jihar Bauchi Ya Ziyarci Atiku Abubakar
      • Graphic Photos:Yanayi Wanda Ya Kai Hari Yau A Jiha...
      • Tafsir: Rikicin Duniya Da Na Lahira By Sheikh Isa ...
      • Hanyoyin 25 Masu Sauki Domin Samun Lada Mai Yawa
      • New Music: Kana Raina By Hussaini Danko
      • Bom Ya Tashi Dan Yan Shi'a 15 A Kano
      • Photos: Buhari Ya Gana Da Sarauniyar Ingila A Malta
      • Tafsir: Tambayoyi Tara Bayan Mutuwa By Sheikh Isa ...
      • Graphic Photos: Wani Dalibi Poly Ya Kashe Kansa
      • Buhari Na Neman Jefa Kasar Nan Cikin Mummunan Hali...
      • Yadda Wani Attajiri Ya Yi Wa Kansa Yankan Rago A J...
      • New Film: Zurfin Ciki 2015 Part 2 Starring Ali Nuhu
      • Yan Najeriya Sun Nuna Bacin Ransu Da Buhari
      • Dan Marigayi Audu Abubakar Ne Zai Maye Gurbin Sa A...
      • Kotu Ta Hana Wata Ma'aikaciya Sanya Hijab A Faransa
      • Photos: Buhari Yabar Najeriya Zuwa Malta
      • Photos: An Kaddamar Da Sarkin Kano Mastayi Sabon C...
      • Photos: Gwamna Jihar Nasarawa Ya Kwanta Akan Katif...
      • Nafisah Abdullahi Tayi Allah Wadai Da Matan Da Ke ...
      • Photos: Happy Birthday Haleema Atete, Ga Sabin Hot...
      • New Film : Zurfin Ciki 2015 Part 1 Starring Ali Nu...
      • An Haramta Yi Wa Mata Kaciya A Gambia
      • Magajin Garin Kano Ya Rasu
      • Photos:Buhari,Osinbajo, Saraki, Tinubu Da Amaechi ...
      • Video: Manchester United 0 PSV 0
      • Video: Shakhtar Donesk 3 Real Madrid 4
      • Yanda Ake farfesun kifi
      • Yanda Ake Karya Sihiri Da Lalata Sharrin Aljanu
      • Photos: Buhari Ya Halarci Wajen Binne Matan Awolowo
      • Za A Fara Kama Masu Boye Fetur A Najeriya
      • Abu Ashirin Da Mata Ke So
      • Macen da Aljanna ta fi Karfin ta
      • New Music: Nayi Kira By Hussaini Danko
      • New Music : Kira Nake by Hussaini Danko
      • Yanda Ake Hada Kunu Aya
      • Al'ajabi Part 11
      • Paparoma zai je Kenya
      • An gano wata jigidar bama-bamai a Paris
      • Bangladesh ta haramta amfani da Facebook saboda Tsaro
      • Graphic Photos: Abunda Kishiyarta Ta Mata Ranar Am...
      • Hanyoyin 15 Da Zaka Bi Domin Gujewa Aikata Zinna
      • Al'ajabi Part 13
      • Al'ajabi Part 12
      • Video: Barcelona 6 Roma 1
      • Video: Arsenal 3 Dinamo Zagreb 0
      • Video: Maccabi Tel-Aviv 0-4 Chelsea
      • Photos: An Ba wa 2face Sarauta A Kaduna
      • Buhari Ya Bada Sakon Ta’aziyya Ga Iyalan Audu
      • APC Za Ta Tsayar Da Sabon Dan takara
      • New Music: Mafita By Hussaini Danko
      • New Music: Rabin Mutum By Hussaini Danko
      • Al'ajabi Part 14
      • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
      • Graphic Photos: Wata Yarinya Tana Bukatar Taimako ...
      • Hakurin Zama Da Mace Mara Biyayya
      • Photos: Aisha Buhari A Offishin FIRST LADY
      • Photos: Major AL Ayangbesan, Soja Najeriya Wanda B...
      • Boko Haram, ISIS, Al-Qaeda Na Shirin Kai Hari — Am...
      • Photos: Sabin Hotuna Iyalan Marigayi Sani Abacha
      • New Music: Shakuwa By Hussaini Danko
      • Photos: Buhari Ya Halarci Taron Kasashen Masu Arzi...
      • An rataye 'yan adawa biyu a kasar Bangladesh
      • Darussa Bakwai Game Da Rasuwar Dan Takarar Gwamna...
      • Photos: Isar Buhari Iran
      • Abunda Dokar Zabe Tace Akan Mutuwar Audu
      • An yi jana'izar Abubakar Audu
      • Mutane 8 sun mutu a harin Maiduguri
      • Film: Download Hausa Shargalle Part 2 Starring Sul...
      • Photos: Adama Indimi A Sabon Hotuna
      • New Music: Sirrina By Hussaini Danko
      • Photos: Ali Artwork Ya Ziyarci Rahma Sadau
      • Prince Abubakar Audu Dan Takara Gwamna Jihar kogi ...
      • An Kai Hari A Garin Kauye Mafe Dake Borno
      • Photos: Buhari Yabar Najeriya Zuwa Iran
      • Photo; Aisha Buhari, Ambode Da Bola Tinubu Wajen W...
      • Film: Download Hausa Film Shargalle Part 1
      • Al'ajabi Part 10
      • List: Makarantu Sakandare Da Suka Fi Kowani Makara...
      • Photo: Buhari Tare Da Tsohon Direban Sa Da Yar sa
      • Music: SO by Hussaini Danko
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • Sadiya Gombe Ft Al'ameen Bauchi (Ra'ayin Ki Ne Nawa) Sabuwar Waka
  • Zanga-zanga A Bauchi-Gwamnatin Ta Saka Dokar Hana Fita Da Zirga-Zirga Ac...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger