A karon farko a tarihin manyan gasar kwallon kafa ta maza a Turai, wata 'yar sanda ta yi alkalancin wasan Bundesliga ta Jamus.
Bibiana Steinhaus, mai shekara 38 ta yi alkalanci a karawar da aka yi tsakanin Hertha Berlin da Werder Bremen ranar Lahadi, wadda aka tashi kunnen doki, 1-1, da kuma katin gargadi daya kawai.
Kafin Bibiana ta yi jagoranci a wannan wasa da aka yi a fitaccen filin wasan nan na Olympic Stadium da ke Berlin, babu wata mata da ta taba alkalancin wani babban wasa a manyan gasar Turai ta maza ta Jamus ko Ingila ko Faransa ko Italiya ko kuma Spaniya.
Kafin wasan ta ce tana matukar farin ciki da aka ba ta wannan dama.
Ita dai Bibiana tana da kwarewa a aikin alkalancin wasan kwallon kafa, inda ta yi alkalanci a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai na mata na shekaran nan.
Tana kuma yin alkalancin wasa a gasar rukuni na biyu ta Jamus.
Ta ce ba ta da wani bambanci da alkalan wasa maza, in banda cewa ita kadai ce mai gashin mata kawai a cikinsu.
Source: BBC Hausa
Title :
Yar Sanda Tayi Alkalancin Wasan Maza
Description : A karon farko a tarihin manyan gasar kwallon kafa ta maza a Turai, wata 'yar sanda ta yi alkalancin wasan Bundesliga ta Jamus. Bibiana ...
Rating :
5