Wani rahoto da hukumar kididdiga ta Birtaniya ta fitar ya nuna cewa sunan Muhammad ya samu gagarumar karbuwa a Ingila, inda ya kasance cikin sunaye 10 da iyaye suka fi sanya wa 'ya'yansu a yanzu.
Sunan na Muhammad wanda kafin wannan lokaci ba ya cikin goman farko da suka fi farin jini, a yanzu ya kawar da sunan William ya hau gurbi na goma a jerin sunayen da aka fi rada wa yara.
A alkaluman da hukumar ta fitar ta ce sunan Oliver wanda shi ne na daya cikin sunayen da iyaye ke sanya wa 'ya'yansu maza, ya ci gaba da rike wannan matsayi nasa a yawancin sassan Ingila da yankin Wales, in banda yankin Arewa maso yammaci inda sunan Harry har yanzu shi ne na daya, da kuma Landan da yankunan tsakiyar yammaci inda nan kuma Muhammad ne ya fi farin jini.
A bangaren sunayen mata kuwa Olivia ya maye gurbin Amelia daga matsayi na daya a Ingila da yankin na Wales, kamar yadda kididdigar ta nuna.
Sunan na Olivia ya sake dawowa da tagomashinsa, domin daman shi ne mafi farin jini da iyaye ke sanya wa 'ya'yansu mata a tsakanin shekarun 2008 da 2010.
Sunan Harper shi ne ya fi samun tagomashi sosai, cikin sunayen da ake rada wa 'ya'ya mata, kamar yadda Jaxon shi kuma ya samu cirawa fiye da kowane suna a bangaren maza, a wannan lokacin.
Sunan Harper din dai shi ne David Beckam da matarsa Victoria suka rada wa 'yarsu, inda a shekara ta 2011 da aka haife ta, an samu jarirai mata 42 da aka sa musu sunan a Ingila da Wales.
Zuwa shekara ta 2016, sunan shi ne na 44 a sunayen da aka fi sanya wa mata, wanda a lokacin an samu jarirai 1,256 da ke da sunan.
A shekarar kuma sunan mata na Lily ya kawar da Poppy daga cikin goman farko, ya maye gurbinsa.
Duk da cewa Olivia ne ya fi yawa a sunayen da ake radawa 'ya;ya mata a gaba daya, Armelia har yanzu shi ne ya fi farin jini a Yorkshire da Humber da yankunan tsakiya na gabashi da na yamma da kuma na Birtaniyar da kuma Landan.
Sabbin fina-finan Star Wars ga alama sun yi tasiri kan yadda iyaye ke zabar suna yen da suke sanya wa 'ya'yansu.
Iyaye sun rika sa wa 'ya'yansu sunayen jaruman cikin fina-finan, ta yadda aka samu karuwar sunaye irin su Rey a mata, da Jaxon a maza da Arlo shi ma a maza da kuma Luna a mata.
Haka kuma a lokacin da aka haifi Gimbiya Charlotte, ta hudu a jerin masu jiran gadon sarautar Ingila, sunan ya zama na 12 a jerin wadanda aka fi sanya wa jarirai mata, inda ya yi tashin gwauron zabi ya wuce mataki 13, a wannan shekara ta 2015.
Shi ma dan uwanta Yarima George haihuwarsa ta sa sunansa ya samu tagomashi.
Sunan shi ne na 10 a wadanda iyaye suka fi sa wa 'ya'yansu maza, a 2013, shekarar da aka haife shi, inda shi ma ya ci gaba zuwa matsayi na bakwai a 2014, har ya kai na hudu a 2015.
A shekara ta 2016, ya zamanto na uku, inda aka samu yara masu sunan har 5,263.
Hukumar kididdigar ta Birtaniya ba ta lissafa da sunayen da aka sanya wa yara kasa da uku ba a Ingila da Wales gaba daya domin kare sirrinsu.
Hukumar kididdigar ta Birtaniya ta ce, ta fitar da wannan sakamako ne bisa alkaluman da ta tattara na sunayen da ake rijistar haihuwar yara da su.
Source: BBC Hausa
Title :
Sunan Muhammad Ya Sami Matsayi A Burtaniya
Description : Wani rahoto da hukumar kididdiga ta Birtaniya ta fitar ya nuna cewa sunan Muhammad ya samu gagarumar karbuwa a Ingila, inda ya kasance cikin...
Rating :
5