Wani babba kuma sanannen malamin addini dake shugabantar rukunin majami'u na Eternal Light of World Christian mai suna Dakta Adol Awam ya fito ya bayyana kudurin sa na neman tikitin takarar gwamnan jihar Ebonyi a zaben 2019 mai zuwa a karkashin jam'iyyar APC.
Kamar yadda muka samu, Awam ya bayyana kudurin na sa ne a garin Abakalki, babban birnin jihar ta Ebonyi a jiya Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai.
Jaridar naij ta samu cewa babban malamin ya kuma bayyana cewa ya yanke shawarar ya shiga siyasa ne domin tabbatar da samun shugabanci na garin ga al'ummar jihar wadanda yake da kudurin jagoranta indan har suka bashi dama.
Source :naij hausa
Title :
Wani Malamin Addini Zai Nemi Takarar Gwamna A Zabe Mai Zuwa
Description : Wani babba kuma sanannen malamin addini dake shugabantar rukunin majami'u na Eternal Light of World Christian mai suna Dakta Adol Awam y...
Rating :
5