Sanatoci 46 ne kacal ke tare da Shugaban kasa Buhari yayin da ‘Yan Majalisar ke kokarin takawa Shugaban burki na yunkurin hana su canza tsarin gabatar da zabe mai zuwa na 2019.
Kwanan nan ma wani Sanata 1 ya rasu.A kwanakin baya Majalisa ta kawo kudirin da zai sa a maida zaben Shugaban kasa karshe wanda hakan na iya kawowa Shugaba Buhari matsala a 2019. Shugaban kasar dai yayi watsi da wannan kudiri na Majalisar Kasar tuni.
‘Yan Majalisa sun ce za su yi amfani da karfin da dokar kasa ta ba su wajen shigar da wannan kudiri na su cikin tsarin zabe. Magoya bayan Shugaban kasar dai sun fara kokarin ganin wannan yunkuri bai samu goyon baya ba.
Labari ya zo mana cewa a Majalisar Wakilan Tarayya ana sa ran a samu ‘Yan Majalisa 260 da za su hana wannan kudirin ya kai labari. A Majalisar Dattawa kuwa dai akwai Sanatoci 46 da ba su tare da sauran ‘Yan Majalisa kan wannan.
Masu goyon bayan Shugaban kasar dai tuni su ka shiga neman a marawa Shugaba Buhari baya a Majalisa. Shugabannin APC da Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar su na cikin masu kokarin hana ‘Yan Majalisa cigaba da wannan nufi.
Source :naij hausa
Title :
Fiye Da Rabin Yan Majalisar Dattawa Sun Juya Wa Buhari Baya
Description : Sanatoci 46 ne kacal ke tare da Shugaban kasa Buhari yayin da ‘Yan Majalisar ke kokarin takawa Shugaban burki na yunkurin hana su canza tsar...
Rating :
5