Fitaccen jarumin nan a shire-shiren fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood kuma mawaki Adam A. Zango, ya bayar da sanarwar cewa ya kammala shire-shiren sa na dawowa jihar Kano dake zaman tamkar cibiya ga harkokin fina-finan da zama.
Jarumin wanda dan asalin karamar hukumar Zangon Kataf ne na jihar Kaduna har ila yau ya kuma sanar da hakan ne cikin wani sakon da ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram.
Jaridar naij dai ta samu cewa jarumin ya rubuta sako kamar haka a shafin na sa: "My Kano cribbbb!! The city need me that's why came back".
A baya dai mai karatu zai iya tuna cewa jarumin ya kwashe kayan sa gaba daya ya bar zaman garin na Kano biyo bayan wata 'yar rashin jituwa da ya samu da mutanen garin kan wata waka da ya yi ya kuma fitar mai taken 'Bahaushiya' da ta zama tamkar cin mutunci a garesu.
Source :naij hausa
Title :
Nadawo Kano Da Zama- Adam A Zango
Description : Fitaccen jarumin nan a shire-shiren fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood kuma mawaki Adam A. Zango, ya bayar da sanarwar cewa ya k...
Rating :
5