Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da dokan canza jadawalin zaben 2019 wanda yan majalisa suka samar kwanakin baya.An samu rahoto daga DailyTrust cewa shugaba Buhari ya bada dalilai uku da rashin amincewa da wannan doka da majalisar wakilan tarayya da kuma na dattawa suka samar.
Labarin da aka samu daga majiya mai karfi ya bayyana cewa shugaba Buhari ya aika sakon rashin amincewarsa ga shugaban majalisan wakilai, Yakubu Dogara, da kuma shugaban Majalisan dattawa, Bukola Saraki.
Ana sa ran shugabannin majalsun zasu karanta wannan wasika tsakanin yau da ranan Alhamis.Ana sa ran shugabannin majalsun zasu karanta wannan wasika tsakanin yau da ranan Alhamis.
Gabanin yanzu, kungiyoyin fafutuka, manyan lauyoyi da wasu shahrarrun yan Najeriya sun bayyana rashin yardarsu da wannan doka kuma sunyi kira ga shugaba Buhari kada ya sake ya amince da shi.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Yayi Watsi Da Batun Canza Fasalin Zabe
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da dokan canza jadawalin zaben 2019 wanda yan majalisa suka samar kwanakin baya.An samu rahoto daga Dai...
Rating :
5