Rundunar Yansandan jihar Borno ta bankado wani kulalliyar shiri da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ke yin a kai munanan hare haren bama bamai a kwaryar garin Maiduguri, inji rahoton The Cable.
Rundunar ta bayyana cewa kungiyar ta shirya kai wadannan hare hare ne ta hanyar amfani da motoci da zata cikasu makila da ababen fashewa tare da bama bamai, kamar yadda mataimakin kwamishinan Yansanda Ahmed Bello ya tabbatar.
Majiyar NAIJ ta ruwaito Jami’in dansandan na fadin yan ta’addan da zasu kai harin sune wadanda Sojoji suka fatattaka daga dajin Sambisa, amma ya bada tabbacin jami’an tsaro a shirye suke su tare su, inda yace;“Rundunar Yansandan na shawartar jama’a da su kasance masu lura da duk wani mutum ko wata motar da basu gamsu da kasancewar a inda suke ba, don daukan matakin da ya dace.
Ina tabbatar muku da cewa duk wanda ya kawo mana ire iren bayanan sirrin nan, ba zamu bayyana shi ba,don kuwa aikin mu ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a.” Inji shi.
Wannan sanarwa dai yazo ne kimanin awanni 24 da yan ta’addan suka kai wani harin kunar bakin wake a kusa da barikin Sojoji na Giwa, inda suka jikkata mutane tara a yayin harin.
Source :naij hausa
Title :
Mayakan Boko Haram Na Shirin Kai Wani Gagarumin Hari Maiduguri
Description : Rundunar Yansandan jihar Borno ta bankado wani kulalliyar shiri da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ke yin a kai munanan hare haren bama ba...
Rating :
5