A jiya ne labari ya zo mana cewa Babban Kotun Najeriya na koli ya daga karar Bukola Saraki har sai baba ta gani. Ana karar Shugaban Majalisar ne da laifin kin bayyana ainihin kadarorin da ya mallaka kamar yadda doka ta tanada.
Bukola Saraki da Gwamnatin Tarayya sun shigar da kara zuwa babban Kotun kasar ne inda ake kalubalantar hukuncin wani Kotun daukaka kara game da shari'ar da ake yi ta fama yi da Shugaban Majalisar a Kotun CCT na kasar.
Lauyan da ke kare Gwamnati Rotimi Jacobs ya nemi a ba sa lokaci wanda babban Lauyan da ke kare Bukola Saraki watau Kanu Agabi ya ki amincewa sa shi. Jacobs yace ya na bukatar lokaci kafin ya duba karar sannan ya bada martani.
Babban Alkali mai shari'a Muhammad Musa Dattijo yace za su daga shari'ar zuwa nan gaba. Alkalin yace ba su ranar sake zama ba tukun. Da zarar dai Kotu ta yanke shawarar ranar da za a dawo, za a sanar da masu karar a rubuce.
Source :naij hausa
Title :
Andaga Karan Bukola Saraki Har Sai Baba Ya Gani
Description : A jiya ne labari ya zo mana cewa Babban Kotun Najeriya na koli ya daga karar Bukola Saraki har sai baba ta gani. Ana karar Shugaban Majalisa...
Rating :
5