Wani Bawan Allah mai suna Amir Abdulazeez ya bayyana yadda ta kaya lokacin da su ka ziyarci tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata yanzu Rabiu Musa Kwankwaso domin wani aiki a gidan sa a Abuja wanda aka kawata da ja da kuma fari.
Amir Abdulazeez ya lura cewa Jama'a daga ko ina a fadin kasar nan su na zuwa wajen Sanata Kwankwaso kuma wadanda su ka fi kusa da Sanatan a Birnjn Tarayya Abuja su ne Talakawan da yake tare da su da a Kano komai runtsi.
Mafi yawan masu zuwa wajen Sanatan, sun zo ne domin gaisuwa ba don a ba su wani abu ba kamar yadda ya lura. Daga cikin su akwai yaran da ba 'Ya 'yan kowa ba da aka tura karatu su ka kammala a kasar waje a lokacin yana Gwamnan Jihar Kano.
A wannan ziyarar, wannan Bawan Allah ya lura cewa Kwankwaso ya wuce kallon da ake yi masa don kuwa siyasar sa ta ratsa ko ina a Najeriya. A gidan, za ka ga motoci daga ko ina a fadin kasar nan sun domin su ga Jagoran na Kwankwasiyya.
Bayan Buhari dai da wuya a samu mutum mai farin jini irin Kwankwaso. Sai dai kuma shi rikakken 'Dan siyasa ne wanda ya san ta. Ko da wannan mutumin ya bar gidan Kwankwaso a gajiye cikin dare, da safe kurum sai ya ji Kwankwaso har ya isa Garin Fatakwal.
Source :naij hausa
Title :
Kwankwaso Na Kokari Dare Da Rana Don Zama Shugaban Kasa - Amir Abdulazeez
Description : Wani Bawan Allah mai suna Amir Abdulazeez ya bayyana yadda ta kaya lokacin da su ka ziyarci tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata yanzu Rabi...
Rating :
5