Tabbas dukkan mai rai mamaci ne wata rana. Kamar dai yadda muka samu daga majiya mai tushe, fitaccen jarumin nan na masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakabi da Kannywood watau Malam Muhammad Umar Waragis ya rasa ransa da safiyar yau Talata 13 ga watan Maris, 2018.
Marigayin dai ya sha fama ne da matsananciyar jinya kafin rasuwar ta sa kamar dai yadda daya daga cikin 'ya'yan sa ya shaida mana.
NAIJ dai a baya ta kawo maku labarin cewa Iyalan fitaccen dan fim din sun bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin wadataccen kudin da za su ci gaba da jinyarsa a asibiti.
Kamar yadda jaridar naij ke da labari, an kwantar da Malam Waragis ne a wani asibiti dake garin Jos sakamakon ciwon koda da yake fama da ita.
Haka ma dai a yayin tattaki tun daga Kano domin duba lafiyar Malam Waragis da ya yi, fitaccen mawakin finafinan Hausa Sa'eed Nagudu ya baiwa iyalansa gudummawar kayan masarufi da kuma kudi, inda kuma ya yi fatan Allah ya tashi kafadun mara lafiyan.
Allah yaji kanshi..... AMEEN
SOURCE :NAIJ HAUSA
Title :
Allah Yayi Wa Fitatcen Jarumin Film Din Hausa Waragis Rasuwa
Description : Tabbas dukkan mai rai mamaci ne wata rana. Kamar dai yadda muka samu daga majiya mai tushe, fitaccen jarumin nan na masana'antar shirya...
Rating :
5