1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Fadakarwa » Slider » Cikakken Bayani Akan Daren Lailatul Kadari( Dare Daya Tamkar Dubu)

Cikakken Bayani Akan Daren Lailatul Kadari( Dare Daya Tamkar Dubu)

By Abdul Mk
Add Comment
Sunday, 26 June 2016

DAREN "LAILATUL QADARI" ITA Ce MAFI GIRMAN DARARE

: Lallai daren "Lailatul qadari" shi ne mafificin darare, kuma Allah ya sauce alqur'ani ne xungurugum a cikinsa, Sannan Allah ya bayyana cewa shi wannan dare ya fi watanni dubu, kuma dare ne mai albarka, wanda a cikinsa ne kuma ake rabe lamurra masu hikima, kamar yadda Allah (سبحانه وتعالى) ya ke faxa a farkon "suratud dukhan":
(حم * والكتاب المبين * إنا أنزلناه في ليلة مباركة إنا كنا منذرين * فيها يفرق كل أمر حكيم * أمرا من عندنا إنا كنا مرسلين * رحمة من ربك إنه هو السميع العليم) [الدخان: ١ – ٦].
Ma'ana: "Ina rantsuwa da wannan littafi mabaiyani * Lallai mu ne muka sauqar da shi a cikin dare mai albarka, lallai mu mun kasance masu gargaxi * A cikinsa ne ake rarrabe dukkan lamari mai hikima * Lamari ne daga wurinmu, lallai mun kasance masu tura manzanni * Rahama ce daga wurin Ubangijinka, lallai shi mai ji ne masani" [Ad-dukhan: 1-6]. Allah (سبحانه وتعالى) ya ce:
(إنا أنزلناه في ليلة القدر * وما أدراك ما ليلة القدر * ليلة القدر خير من ألف شهر * تنزل الملائكة والروح فيها بإذن ربهم من كل أمر * سلام هي حتى مطلع الفجر) [القدر: ١ – ٥].
Ma'ana: "Lallai mu muka sauqar da alqur'ani a cikin daren qaddara * Me ya sanar da kai abinda ake ce: lailatul qadar? * Daren qaddara ya fi alheri fiye da watanni guda dubu * Mala'iku suna sassauka da Mala'ika jibrilu a cikinsa * Da izinin Ubangijinsu, da kowani lamari * Aminci ne wannan dare har zuwa fudowar alfijir" [Alqadar: 1-5].
Kuma ya tabbata daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce:
«مَنْ قَامَ لَيْلَةَ الْقَدْرِ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا، غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Ma'ana: "Duk wanda ya yi tsayuwan lailatul qadari yana mai imani da Allah, da kuma neman lada to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". Bukhariy da Muslim su ka rawaito shi([2]).
"Tsayuwan wannan dare" kuma na kasancewa ne da yin salloli, zikiri, da addu'oi, da sadaka, da makamantan haka na fiskokin alheri.
Kuma lallai "suratul qadari" ta yi nuni cewa yin aiki a wannan dare ya fi alheri akan yin aiki a watanni dubu da babu lailatul qadari a cikinsu. Wannan kuma falala ne mai girma, kuma rahama ce daga Allah zuwa ga bayinsa, Don haka; ya dace ga musulmai su girmama wannan dare, su kuma raya shi da bautar Allah.
Kuma haqiqa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada labari cewa a cikin darare goman qarshen ramadhana wannan daren ya ke, kuma a cikin dararen mara (wato; 21, 23, 25, 27, da 29) aka fi fatan samu ko dacewa da wannan dare, a inda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ke cewa:
«الْتَمِسُوهَا فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَان، الْتَمِسُوهَا فِي كل وِتْرٍ».
Ma'ana: "Ku nemi lailatul qadari a cikin goman qarshe na ramadhana, ku nemi shi a cikin kowani dare na mara"([3]).
Kuma haqiqa hadisai ingantattu daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) sun yi nuni cewa lallai wannan dare yana ciratuwa a cikin kwanaki goman qarshe, ba wai da'iman har a bada a cikin dare ayyananne guda xaya ya ke ba; don haka ta yiwu ya zama shi ne daren ashirin da xaya (21), wani lokaci kuma daren ashirin da uku (23), wani lokacin kuma daren ashirin da biyar (25), wani lokacin kuma ashirin da bakwai (27); wanda shi ne aka fi tsammanin samunsa a cikinsa, haka kuma zai iya kasancewa shi ne daren ashirin da tara (29), kamar yadda kuma zai iya yiwuwa a same shi a tsakanin dararen shafa'iy (wato: 22, ko 24, ko 26, ko kuma 28), don haka; Duk wanda ya yi tsayuwar dare na dukkan dararen goman qarshen ramadhana gabaxayansu yana mai imani da Allah da kuma neman ladanSa to lallai babu makawa ya riski wannan dare mai albarka, kuma ya rabauta da alherin da Allah ya yi alkawari ga wanda su ka aikata hakan.
Kuma haqiqa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance ya kan keve waxannan darare goman da qarin zabura da himma wajen bautar Allah da irin abinda baya aikata shi a cikin sauran kwanaki ashirin na farkon, A'ishah (رضي الله عنه) ta ce:
«كَانَ النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَجْتَهِدُ فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مِنْ
Ma'ana: "Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana qara qoqarin ibada a cikin kwanaki goman qarshen ramadhana irin qoqarin da baya yinsa a cikin wassunsu"([4]). Ta sake cewa:
«كَانَ النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ أَحْيَى لَيْلَه وَأَيْقَظَ أَهْلَهُ وَجَدَّ وَشَدَّ الْمِئْزَرَ».
Ma'ana: "Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan goman qarshe suka shiga ya kan raya darensa, ya kuma tayar da iyalansa daga barci, ya zage damtse ya qara xaure kwarjallensa"([5]).
Kuma ya kasance ya kan yi i'itikafi a cikinsu a mafi rinjayen lokaci, Allah mabuwayi da xaukaka kuma yana cewa:
(لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة) [الأحزاب: ٢١].
Ma'ana: "Kuma haqiqa ya kasance a gare ku dangane da rayuwar Manzon Allah abun koyi mai kyau" [Ahzab: 21].
Kuma A'ishah (رضي الله عنه) ta tambaye shi ta ce:
«إِنْ وَافَقْتُ لَيْلَةَ الْقَدْرِ فَمَا أَقُولُ فيها؟ قَالَ: "قُولِي: اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي».
Ma'ana: "Idan na yi dacen lailatul qadari to me zan riqa faxa a cikinsa? Sai yace: Ki ce: Ya Allah lallai kai mai afuwa ne, kana son afuwa; to ka yi min afuwa"([6]).
Kuma sahabban Annabi (صلى الله عليه وسلم) Allah ya qara yarda a gare su da kuma magabatan kwarai bayansu sun kasance suna girmama waxannan darare guda goma, kamar yadda kuma suke qoqarin aikata dangin alkhairi nau'i-nau'i a cikinsu.
Don haka abunda aka shar'anta wa musulmai a ko-ina suke shine su yi koyi da Annabinsu (صلى الله عليه وسلم), da kuma sahabbansa masu karamci Allah ya qara yarda a gare su, tare da kuma magabantan wannan al'umma mutanen alkhairi, Sai su riqa raya waxannan dararen da yin sallah, da yin karatun alqur'ani, da kuma nau'ukan zikirori da ibadu, suna masu imani da Allah da kuma neman lada, saboda su rabauta da gafarar zunubansu, tare da 'yantawa daga shiga wuta, a matsayin falala daga gare shi (), da kyauta mai karamci.
Kuma lallai dalilan alkur'ani da sunna sun yi nuni cewa lallai wannan falala mai girma ana samunta ne idan aka nisanci manyan laifuka da ake ce da su: alkaba'ir, kamar yadda Allah (سبحانه وتعالى) ya ke cewa:
(إنْ تجتنبوا كبائر ما تنهون عنه نكفِّر عنكم سيئاتكم وندخلكم مدخلا كريما) [النساء: ٣١].
Ma'ana: "Idan ku ka nisanci manya-manyan laifukan da aka hane ku za mu kankare mu ku kananan laifukanku, mu kuma shigar da ku mashiga mai karamci", [Nisa'i: 31]. Annabi (صلى الله عليه وسلم) kuma ya ce:
«الصَّلَوَاتُ الْخَمْسُ، وَالْجُمْعَةُ إِلَى الْجُمْعَةِ، وَرَمَضَانُ إِلَى رَمَضَانَ، مُكَفِّرَاتٌ لمَا بَيْنَهُنَّ إِذَا اجْتَنَبَ الْكَبَائِرَ».
Ma'ana: "Salloli guda biyar, da juma'a zuwa juma'a, da ramadhana zuwa ramadhana, masu kankare abunda ya kasance a tsakaaninsu ne matuqar an nisanci manya-manyan laifuka". Muslim ne ya ruwaito shi a cikin "sahihinsa"([7]).
Yana daga abinda ya kamata a fadakar: Lallai wassu musulmai su kan yi iya qoqarinsu wajen bautar Allah a cikin watan azumi na ramadana, su kuma tuba zuwa ga Allah (سبحانه وتعالى) daga abinda ya gabata na dukkan zunubansu, sannan bayan fitan watan ramadhana sai su koma zuwa ga aiyukansu munana, to lallai akwai hatsari mai girma a cikin haka, kuma wajibi ne ga musulmi ya nisanci hakan, ya kuma yi niyya ta gaskiya cewa zai doge kan biyayya ga Allah, ya kuma bar yin savo a gare shi, kamar yadda Allah mabuwayi da xaukaka yake faxa wa Annabinsa (صلى الله عليه وسلم):
(واعبد ربك حتى يأتيك اليقين) [الحجر: ٩٩].
Ma'ana: "Kuma ka bauta ma Ubangijinka har mutuwa ta zo maka", [Hijri: 99]. Ya kuma ce:
(يا أيها الذين ءامنوا اتقوا الله حق تقاته ولا تموتن إلا وأنتم مسلمون) [آل عمران: ١٠٢].
Ma'ana: "Ya ku wadanda su ka yi imani ku ji tsoron Allah iyaka tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmai", [Ali-imraan: 102]. Allah (سبحانه وتعالى) yana cewa:
(إن الذين قالوا ربنا الله ثم استقاموا تتنزل عليهم الملائكة ألا تخافوا ولا تحزنوا وأبشروا بالجنة التي كنتم توعدون * نحن أولياؤكم في الحياة الدنيا وفي الآخرة ولكم فيها ما تشتهي أنفسكم ولكم فيها ما تدعون * نزلا من غفور رحيم) [فصلت: ٣٠ – ٣٢].
Ma'ana: "Lallai waxanda suka ce Ubangijinmu shi ne Allah, sannan suka tsayu, Mala' 'iku suna sassauka akansu cewa kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki, ana kuma yi muku albishir da aljannar da aka kasance ake muku alkawari * Mune majibintanku a rayuwar duniya da kuma a lahira, kuma a cikinta kuna da abin rayukanku suke sha'awa, kuma kuna da duk abinda kuka nema * Liyafa ne da mai gafara mai rahama", [Fussilat: 30-32].
Ma'anar wannan ayar shi ne: Lallai waxanda su ka tabbatar da cewa Ubangijinsu shi ne Allah, suka yi kuma imani da shi, suna masu ikhlasin bauta a gare shi, sannan suka tsayu akan haka, to Mala'iku suna yi musu albishir a lokacin mutuwarsu da cewa kada su ji tsoro, kada kuma su yi baqin ciki, kuma lallai makomarsu itace aljannah; saboda imaninsu da Shi Allah (سبحانه وتعالى) da kuma tsayuwarsu akan addininSa, ta fiskar yi masa biyayya da barin sava masa, tare da kevance Shi da yin bauta.
Kuma ayoyin alqur'ani da suke nuna irin wannan ma'anah suna dayawa; dukkansu kuma suna nuna wajabcin tabbatuwa a kan gaskiya, tare nisantar savon Allah ta'alah da kiyayanSa.
Yana kuma daga cikinSu faxinsa maxaukakin sarki:
(وسارعوا إلى مغفرة من ربكم وجنة عرضها السموات والأرض أعدت للمتقين * الذين ينفقون في السراء والضراء والكاظمين الغيظ والعافين عن الناس والله يحب المحسنين * والذين إذا فعلوا فاحشة أو ظلموا أنفسهم ذكروا الله فاستغفروا لذنوبهم ومن يغفر الذنوب إلا الله ولم يصرّوا على ما فعلوا وهم يعلمون * أولئك جزاؤهم مغفرة من ربهم وجنات تجري من تحتها الأنهار خالدين فيها ونعم أجر العاملين) [آل عمران: ١٣٣ – ١٣٦].
Ma'ana: "Kuma ku yi gaggawa zuwa ga wata gafara daga Ubangijinku, da kuma aljannar da faxinta shine kamar faxin sammai da qassai; an tanade ta ga masu taqawa * Waxanda suke ciyarwa a halin wadaci da qunci, da kuma masu haxiye fushi, da masu afuwa ga mutane, Kuma lallai Allah yana son masu kyautatawa * Kuma sune waxanda idan suka aikata alfasha ko suka zalunci kansu suke tuna Allah Sai su nemi gafara ga zunubansu, Kuma wanene ke gafarta zunubai in banda Allah, kuma basa dogewa akan abunda suke aikatawa alhalin suna sani * Waxancan sakamakonsu shine gafara daga Ubangijinsu da aljannonin da qoramu suke gudana a qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinSu, Madalla da sakayyar masu aiki!", [Ali-imraan: 133-136].
Daga qarshe muna roqon Allah da ya datar da mu da sauran musulmai a cikin waxannan dararen da wassunsu, zuwa ga abinda ya ke so ya kuma yarda da shi, ya kuma tsare mu gabaxaya daga sharrin kayukanmu da kuma munanan aiyukanmu; Lallai shi mai kyauta ne mai karamci.
$&$

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 18:08
In Fadakarwa, Slider
Cikakken Bayani Akan Daren Lailatul Kadari( Dare Daya Tamkar Dubu) Title : Cikakken Bayani Akan Daren Lailatul Kadari( Dare Daya Tamkar Dubu)
Description : DAREN "LAILATUL QADARI" ITA Ce MAFI GIRMAN DARARE : Lallai daren "Lailatul qadari" shi ne mafificin darare, kuma Allah ...
Rating : 5
Related Posts: Fadakarwa, Slider

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Cikakken Bayani Akan Daren Lailatul Kadari( Dare Daya Tamkar Dubu)"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ▼  June (74)
      • Ibrahimovic Zai Koma Club Din Manchester United
      • Gwamnatin Legas Ta Rufi Coci 70 Da Masallatai 20
      • Photos: Wani Yaro Dan Shekara Tara Zai Wakilci Naj...
      • Sanata Ekweremadu Ya Kai Karar Buhari Majalisar Di...
      • Macen Da Ta Fi Alheri Da Wadda Ta Fi Sharri
      • An Tursasa Musulmai Cin Kashin Shanu A Kasar India
      • Su Wanene Yajuju Da Majuju - Muhammad Sani R/Lemu
      • Photos: Wani Dan Jihar Yobe Ya Samu Lambar Yabo A ...
      • Photos: Anyi Nasara Yi Wa Fati Sulaiman Tiyata
      • Buhari Ya Gana Da Obasanjo A Villa
      • Cikakken Bayani Akan Daren Lailatul Kadari( Dare D...
      • A'isha Buhari Za Ta Raba Kayan Abinci A Jihar Gombe
      • Fati Nijar Ta Dauki Nauyin Jinyar Fati
      • Matar Fayose Za Ta Ziyarci EFCC Don Amsa Tambayoyi
      • Kalubale Ga Yan Fim Din Hausa
      • Photos: Buhari A Offishin Sa..Ya Koma Bakin Aikin Sa
      • Photos: Buhari Ya Dawo Najeriya
      • Photos: Yan Acaba Sun Kona Motan Tifa
      • EFCC Ta Garzaya Da Tsohon Gwamnan Adamawa Zuwa Asi...
      • Kotun Misra Ta Yanke Wa Morsi Hukuncin Daurin Rai ...
      • Uwani Muhammad Ta Na Neman Taimako
      • Gwanatin Jigawa Na Binciken Sule Lamido
      • Yan Majalisan Najeria Sun Musanta Neman Karuwai
      • Photos:Bola Tinubu Da Oba Sikiru Adetona Sun Ziyar...
      • Zan Bude Wuta Ga Tsagerun Niger Delta Har Sai Sun ...
      • Alamomin Tashin Al-Kiyama Guda 100 ( Kashi Na Farko)
      • Abin Al'ajabi A Jihar Osun
      • Gwamnonin PDP Sun Nesanta Kansu Da Modu Sheriff
      • Abin Al'ajabi A Jihar Osun
      • Photos: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Ware Milyan A Sh...
      • Majalisar Ministoci Ta Amince Da Sabon Tsarin Karb...
      • Photos: Safiya Musa Ta Haihu
      • Buhari Ya Yaudari Yan Najeriya - Shekarau
      • Gwamnatin Buhari Ta Yarda Da Sabon Tsarin Hada-Had...
      • Photos: Wata Mata Ta Haifi Ya Hudu A Jihar Bauchi
      • Dan Bindiga Ya Hallaka Mutane Hamsin A Birnin Orla...
      • List: Sunayen Manyan Hafsoshin Sojoji Gusa 47 Da R...
      • Watanni Shida Da Kisan Kiyashin Zariya - Muna Jira...
      • Mai Sabawa Iyaye Kayi Kuka Da Kanka - Mal.Aminu Ib...
      • Shawari Ga Shugaba Kasa Najeriya
      • Photos: Sarkin Kano Yayi Murna Cika Shekara Biyu A...
      • Photos: Aisha Buhari Ta Hada Liyafa Wa Tsoffin Mat...
      • Tsohon Kocin Najeriya Amodu Shu'aibu Ya Rasu
      • Graphic Photos: Sojojin Nijeriya Sun Kashe Yan Bok...
      • An Fara Shari'ar Wadanda Suka Kashe Misis Bridget ...
      • Tafsir: Isah Ali Pantami 2016 Ramadan Tafsir Day 4
      • Tafsir: Isah Ali Pantami 2016 Ramadan Tafsir Day 3
      • Video: Wata Masoyan Adam A Zango Ta Masa Kuka
      • Tambayar Da Ta Sanya Sheik Mufti Ismail Menk Kuka
      • Photos: An Halaka Dan Shekara Goma A Kano Bayan An...
      • Babu Alaka Tsakanin Boko Haram Da Kungiyar IS - Am...
      • Photos: A'isha Buhari Ta kaddamar Da Tallafi A Jih...
      • Maganin Daukewar Sha'awa
      • List: Lokunta Shan Ruwa A Jihohin Najeria
      • Tafsir: Isah Ali Pantami 2016 Tafsir Day 2
      • Tafsir: Isah Ali Pantami 2016 Tafsir Day 1
      • Manchester United Ta Siya Eric Bailly
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Jihar Bauchi
      • Gwamnatin Tarayya Ta Soma Yunkurin Samar Da Ayyuka...
      • Baza Muyi Sulhu Da Gwamnati Ba - Tsagerun Niger D...
      • Wanda Yayi Sahur A Zatonsa Alfijir Bai Keto Ba
      • Gwamna Ganduje Ya Tallafawa Mata Sama Da Dubu Daya...
      • Tsohon Kocin Najeriya Stephen Keshi Ya Mutu
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 8
      • An Ga Watan Ramadan A Najeriya
      • Gwamnan Jihar Ekiti Ya Fara Yajin Aiki
      • Gwamnati Ta Bayyana Kudade Da Kadarori Da Aka Kwat...
      • Buhari Na Fama Da Gajeruwar Rashin Lafiya
      • Abbas Sadiq Ya Yi Hadarin Mota
      • Graphic Photos: An Yi Wa Wata Mata Yankan Rago A K...
      • Video: Hadiza Gabon Tare Da Marayu A Bikin Zagayow...
      • List Na Malamai Da Zasu Yin Tafsirin Bana A Jihohi...
      • Photos: Sojojin Nijeriya Sun Sake Nasara Akan Yan ...
      • Photos: Goodluck Jonathan Ya Dawo Najeriya
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger