1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kazamar Gida Part 16

Kazamar Gida Part 16

By Abdul Mk
Add Comment
Sunday, 31 January 2016
Yana zaune cikin motarsa ya zuro k'afa d'aya waje. Jafar ya zagaya ya shiga ciki ya zauna sukayi musabaha. Ganin fuskar Haris da alamun damuwa yace
"Lafiya na ganka wani iri kuwa?"
Haris ya sauke ajiyar zuciya
"Dole ai ka ganni haka,Ummina ce take neman rikitani da daren nan."
"Toh,menene ya faru?"
"Kishin fa? Akan tayi kirana har sau biyar ban amsa ba kuma sanin da tayi ina gidana ne ya sanyata zargi. Nayi rarrashin duniya tak'i saukowa. Bayan wannan kuma na kara laifi,kwana biyun da nayi gidan Rahma ayyuka sunmin yawa na kasa lekawa wajensu saidai waya kaga dole nayi laifi. Nidai yanzu taimakamin zakayi muje ka bata hakuri ko zata hakura na gaji da wannan horon rashin kulani da takeyi wallahi na damu sosai na gaza samun kwanciyar hankalina."
Jafar yace
"Shikenan,kayi jirana na chanja kaya."
"Kai haba,muje kawai mana."
Jafar ya harareshi yana kokarin bude motar
"Ta yaya zanje gaban suruka a haka? Nida zanyi sulhu saita rainani."
Sukayi dariya sannan Jafar ya koma ciki. Ya sanya dogon wandon jeans,ya chanja t-shirt sannan ya leka Siyama.
"Madam bari muje mu dawo."
Ta tsaida idanunta gareshi tana k'are mishi kallo. Yayi fes dashi sai kamshi yake. Zargi ya d'arsu a zuciyarta,kada dai zance Jafar zaije?
"Ina zakaje?"
Kallo d'aya ya yiwa kwayar idanunta ya hango matsanancin kishi,wani shu'umin murmushi yayi yana kasheta da kallonsa mai rikita gangar jikinta
"Wajen kanwarki zaimin rakiya,yanzu zamu dawo."
Da sauri ta nufoshi ai kuwa ya juya ya fita a guje yana dariya ya barta tana huci. Ta kasa zaune,wai meke faruwa ne? Ya Salam,no!!! Jafar bazai taba aure ba!!! Bai isa ba!!!!!! Bazai sanya Hajiya da yan uwana suyimin dariya ba!!!!! Har abada!!!!! Nawa ne ni kad'ai!! Babu wacce ya isa ya so!!!
****
"Yana sona,yana kaunata. Naga hakan a kwayar idanuwansa. Bazan barshi ba saidai zan bashi wahala kamar yanda ya wahalarmin da zuciyata. Saidai ina burin zama matar yaya j!!! Allah Ya azurtani da samunshi matsayin mijina!!!"
Cewar Ladi kenan a ranta,tana zaune ita d'aya a falonsu yayin data zubawa lambarsa ido wanda ta riga ta haddace a kwakwalwarta,tana kallo tana murmushi..
Dakyar Jafar ya lallaba Abida ta hanyar nasiha da ban baki har dai ta sauko sai gashi itace har da hira da dariya. Haris kamar ya shige jikinta tsabar jin dadi. Jafar kam wannan ba bakon abu bane a wajenshi,yasan soyayyarsu sosai don Haris bai kunyarsa. Ya mike tsaye yana duban agogon bangon
"Sha daya saura? Lallai na zaunu a gidan nan,nasan madam tana can a cike."
Haris ya mike tsaye yana dariya
"Ahaf,Allah Sarki madam,munyi mata laifi kam."
Jafar na dariya yace
"Don ma bakasan me nace mata bane."
Ya basu labarin yanda sukayi,dariya duk suka sanya har Ummi. Kafin Ummi tace
"Lallai ka b'allo ruwa Jafar. Kishi babu sauki."
Jafar yayi murmushi kawai ya dubi Haris
"Sai kazo ka mayar dani ko?"
Haris ya harareshi
"Gaskiya saidai na baka mukullin idan yaso da safe sai nazo na karb'a. Bazan iya fita ko'ina ba nabar Ummina."
Ai sai ran Ummi ya k'ara sanyi sosai,tayi wani murmushin jin dadi.
Hakan kuwa sukayi,ya rakashi har kofa. Anan ma Jafar ya dubeshi cike da damuwa
"Kasan Allah,nima na soma tunanin k'ara auren nan. Na gaji da halayyar Siyama."
Haris yace
"Wai har yanzu bata chanja zani bane?"
Ya tab'e baki kad'an yana mai numfasawa
"Ta ina fa? Abun ma sai k'ara gaba yakeyi Haris. Nikam na gaji,zan auro wacce ta iya tsafta da girki ko don na more rayuwar aure. Ko a wajen Allah bani da laifi,bayan da auren sama da d'aya ya zama halal,na bawa Siyama dama da yawa don ta gyara saidai hakan ko kadan bai samu ba duk hakurin da nakeyi da ita. Babu mai tsaidani gun k'ara auren nan saidai idan Allah Ya kaddaro bazanyi bane."
Haris cikin damuwa da tausayawa Jafar yace
"Gaskiyane,ni shaidane akan hakurin da kayi. Toh kana da wacce zaka aura ne?"
Jafar ya basar tamkar baiji ba yana mai kauda kansa gefe kafin ya juyo
"Wai ya ciwon k'afar Hajiyarmu ne? Na kwana biyu ban leka ba amma inason shiga wajen gobe. Ga babbar sallah baifi saura wata biyu ba."
Haris yayi dariya
"Hajiya sunje Jeddah a k'ara duba kafar watakila aiki za'ayi mata. Tare da Yaya Muttaka suka tafi. Baka bani amsar tambayata ba,wacece amaryar?"
Jafar ya hau sosa karan hancinsa yana murmushi kafin ya yamutse fuska
"Wai ma meye ruwanka? Kai malam nifa inada kishi ok? So,ka rabu da wannan maganar ma,bazan iya gwada maka ko wacece ba yanzu. Saida safe."
Ya fada motar yana kokarin tayarwa,Haris yana tuntsira dariya
"Dan iskan karya,idan tayi wari zanji ne. Gama kumbiya kumbiyarka..."
Jafar yana dariya yaja motar ya bar layin ba tare da ya bashi amsar komai ba.
Ya kalleta yaga tana faman huci ta cika tayi fam,yayi mugun murmushi
"Zaki bani hanya na shige ko kuwa dai anan zamu kwana?"
Ta kauce tayi ciki a zuciye,har lokacin bai bar murmushinsa ba. Bayan ya rufe kofar ya shiga ciki. Yana kokarin bud'e d'akin yaji muryarta
"Jafar baka isa ka k'ara aure ka kawo wata gidan nan ba wallahi. Har ni zakayiwa haka?"
Baice mata uffan ba har ya shige ya soma rage kayan jikinsa
"Ina magana kayi shiru? Nasan duk wannan zugar daga Haris take. Ganin da yayi ya k'ara aure shine yake neman ya doraka a hanyar daya bi ko? Toh wallahi ku sani,ni ba Ummi bace da kuka rainawa hankali ita kuma ta iya dauka! Dole ne ayau na shaida maka ni Siyama ni kadai ce mallakinka....."
"Ke wai baki da hankali ne? Kin cikamin dodon kunne,ga bacci inaji. Please get out?!!!"
Ya fada cikin daga murya don tun yana dariya har ta soma bashi haushi. Ta juya sumi sumi ta fice tana kunkuni,ashe dai dagaske yake auren yake nema. Lallai Jafar mugun butulu ne,duk yanda ta bijirewa zabin hajiyarta ta amince zata zauna dashi a halin da yake na wanda bai ajiye komai ba shine don tsabagen rainin hankali har yake da bakin ce mata yaje wajen kanwarta?
Daren kwanan bakin ciki Siyama tayi,batasan tana son mijinta ba sai yanzu.
******
Bayan sati daya da yin haka,dakyar tabar fushinta ta sauko da Jafar ya shaida mata wasa yakeyi.
Zuwa lokacin ya gama kaiwa kololuwar damuwana rashin ji da ganin Ladi. Gaba daya ta dauke kafarta daga shagon,gashi yana jin kunyar Mama bazai iya tambayarta komai game da Ladi ba.
Ladi kuwa duk da cewa tana zumudi da son yin tozali da yaya j,wannanbaisa ta amince ta kuma bayar da kanta ba. Tana sane take mishi hakan,taci sa'a lokacin suna kan rubuta exams,da wannan ta fake ta cewa Mama bazata samu damar zuwa shago ba har sai sun kammala.
*****
WATA RANAR ASABAR LADI TA DAUKI MATSANANCIN KWALLIYA.
Wata ranar alhamis Ladi ta dauki matsananciyar kwalliya cikin wani rantsetsan material kalar orange. Mai adon duwatsu,riga da siket ne sun zauna cif a jikinta. Ta tufke gashinta da manyan ribbons guda biyu ana hangensu ta cikin wadataccen mayafin data yafa a saman kanta. Hannunta rike da wayarta sai karamar jakarta data ratayo a kafad'a tana shirin sanya kanta cikin shagon sukayi kicibus dashi yana shirin fitowa.
Kamshin turarensa ya bugi hancinta da sauri taja baya ta d'ago tana dubansa. Ya ganta a rashin zato da tsammaninsa. Tuni ya fidda ran sanyata a idonsa a wannan ranar ma ganin ya kwashi fiye da mintuna talatin saboda son yaga sunyi arba.
Ya cigaba da bin fuskarta wacce tasha kwalliya da kallon da wa Allah Ya had'ani?
Ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta russuna ta gaidashi kamar yanda ta saba. Ya k'i amsawa har tayi zaton kodai baiji ba,tunanin hakan yasa ta k'ara maimaitawa.
"Lafiya lau Deeya."
Ta mike sosai tana jiran ya bata hanya ta wuce, ya matsa gefe yana fadin
"Inason magana dake."
Gabanta yana faduwa ta karasa gefe nesa kadan dashi ta tsaya,ranta fari k'al har rawa takeyi gefeamma a fili sai ta nuna damuwa tana mai daure fuska. Batace komai ba,shi kuwa Jafar mamakinta yakeyi😮,wai daman Ladi ta iya fushi haka?
"Deeya wai har yanzu baki huce bane?"
Ta girgiza kanta,sai lokacin tayi wani Dan dan bazawarin murmushimai hade da fari
"Mekayi gareni yaya j da har zan rikeka?"
Ya kasheta da daya daga gwala gwalan murmushin(lol)
"Haba Deeya,ni nasan mai laifi ne. Toh idan ma kince bani da laifi meyasa kika haramtamin jin voice naki? Ko so kike na mutu? Please ki tausayawa mai kaunarki,ki bani lambarki kinji Deeya? Yaya j ne fa."
Ta rausayawar da kanta kafin ta dubeshi tayi murmushi,kamar bazata bashi ba sai kuma ta mik'a mishi hannu.
Ya dora wayarsa akan tafin hannunta na dama yana kasheta da kallon love,ta rubuta ta mika mishi.
Ya karba ya duba kafin ya saki murmushi karo na ba adadi ya sake kallonta
"Nagode deeya."
Daga haka ya fice, ta bi bayanshi da kallo tana murmushi hakoranta a bayyane.
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 09:18
In Hausa Novels
Title : Kazamar Gida Part 16
Description : Yana zaune cikin motarsa ya zuro k'afa d'aya waje. Jafar ya zagaya ya shiga ciki ya zauna sukayi musabaha. Ganin fuskar Haris da a...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kazamar Gida Part 16"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ▼  January (93)
      • Yadda zaka sauya yanayin kira a layin MTN zuwa kow...
      • Graphic Photos: Daga Wajen Da Boko Haram Suka Kai ...
      • Photos: Buhari, Abdulsalaam and Obasanjo In Addis ...
      • Mun Karya Laggon Barayin Shanu - Gwamnonin Arewa
      • Kazamar Gida Part 16
      • Boko Haram Ta Kai Hari Garin Dalori Dake Maiduguri
      • Jiddah Part 1
      • Kimanin Mutane Takwas Ne Bam Ya Halaka A Jihar Ada...
      • Saurayi Ya Garkame Budurwarsa A Rami Har Tsawon Wa...
      • Tafsir: Sheikh Jafaar Mahmoud Adam Akan Zikirin Ti...
      • An Kama Wani Jigo Na Kungiyar Boko Haram A Jihar Yobe
      • Sojoji Sun Kewaye Wani Gidan Kasa Da 'Yan Boko Har...
      • Jami'ar Kaduna Dakatar Da Wani Malaminta Kan Batan...
      • Tsohon Shugaban 'Yan Sanda Na Kasa, Mike Okiro Ya ...
      • KOTUN KOLI TA AMINCE DA ZABEN JIHAR RIVERS
      • Gobara Ta Hallaka Mutum Biyu Da Lalata Shaguna 700...
      • Sarkin Musulmi Ya Jinjinawa Kokarin Dattawan Kiris...
      • Photos:An Kwakwalewa Wani Yaro Idanunsa Biyu A Zaria
      • ATBU: Photos: Ansamu Gobara A Hostel Din Mata
      • EFCC Na Shirin Kamo Badeh Da Sauransu
      • Messi Ya Lashe Kyautar Kwallon Kafa Na 2015
      • Yan Gudun Hijira Na Ci Gaba Da Dawowa A Wasu Yanku...
      • Kisan Wani Matashi A Garin Kaduna Ya Jefa Jama'a C...
      • Cutar Zazzabin Lassa Ta Shigo Jihar Gombe,
      • Kotu Ta Dage Sauraren Shari'at Dasuki Sakamakon Ra...
      • Photos: Aisha Buhari Da Dolapo Osinbajo Sun Ziyarc...
      • Fasehun Ya Gargadi Buhari Akan Yaki Da Rashawa
      • Photos: Bill Gates Ya Ziyarci Kaduna
      • An Kama Jagoran Boko Haram Da Wasu Membobinta Guda...
      • Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Shugaban Gidan Rediyo B...
      • Kotu Ta Bada Belin Sakataren Jam'iyya PDP, Olisa M...
      • Photos: Buhari A Dubai
      • Photos: Anyi Wa Wata Yarinya Yar Shekara 8 Aure A ...
      • Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Gano Wasu Kudi Fiye Da N...
      • Tafsir: Aguje Auren Shaawa By Sheikh Ahmad Tijjan...
      • Photos: An Tsinta Wani Jariri A Keffi
      • Photos: Sarkin Kano Da Ya'yan Sa Mata Biyu
      • Photos: Buhari An Hayan Zuwa Dubai
      • EFCC Za Ta Soma Gudanar Da Bincike Kan Wasu Manyan...
      • Gwamnatin El-Rufa'i Ta Kafa Kwamitin Bincike Akan ...
      • Buhari Ya Kalubalanci Rundunar Sojoji Kan 'Yan Mat...
      • Shekara 50 Bayan Rasuwar Tafawa Balewa: Ga Takaita...
      • Tafsir: Download Azaba ya Tabbata Ga Mutane 4 By S...
      • Buhari Ya Bada Umarni A Sake Sabon Bincike Kan Sac...
      • PDP Ta Nima A Tsige Buhari Akan Bacewar Takardun K...
      • Photos: Sheikh Isah Ali Pantami Ya Ziyarci Buhari
      • Nijeriya Za Ta Dauki Karin Sojoji Dubu 12 Aiki
      • Ban Karbi Ko Sisin Kobo A Wurin Dasuki Ba, Inji Nu...
      • EFCC Ta Gano Fiye Da Naira Tiriliyan A Asusun Wasu...
      • Takardun Da Aka Baiwa Majalisa Wanda Ke Kunshe Da ...
      • Dalilin da ya sa muka saki Jaafaru Isa amma muka k...
      • EFCC Ta Kama Shugaban NCC Emeka Mba
      • Jafaru Isa Ya Maido Da Milyan Dari Daga Cikin Kudi...
      • Sake Ja'afaru Isa Ya Nuna Cewa 'Yan PDP Kadai Buha...
      • Mun Yi Nasara Kan Boko Haram - Janar Buratai
      • Dikson Na Jam'iyyar PDP Ya Lashe Zaben Gwamnan Jih...
      • Komitin Binciken Kudaden Sayan Makamai Da Aka Ciny...
      • Hukumar DSS Ta Kama Falake Da Dan Marigayi Abubaka...
      • Ana kammala zaben gwamna a Bayelsa
      • Photos An Gina Coci Me Kama Da Takalmin Mata A Ta...
      • Photos: Sarkin Kano Ya Ziyarci Sudan
      • Dubun Babban Dan Safarar Kwaya Da Aka Fi Nema Ruwa...
      • Ba Za Mu Koma Fagen Daga Da Boko Haram Ba, Inji So...
      • Jim Nwobodo Ya Bar PDP Zuwa APC
      • Photos: Ali Nuhu Ya Je Karo Ilmi A Kasar Amurka
      • Kimanin Zabuka 78 Ne Za A Sake Su A Fadin Kasar Nan
      • Tafsir: Matsayin Mata A Musulunci By Sheikh Dr Ibr...
      • Daso Na Daina Fitowa A Matsayin Muguwa Saidai A Fi...
      • Photos :Aubameyang Ne Gwarzon Kwallon Kafar Afrika
      • Boko Haram Ta Kai Hari Garin Gwoza
      • EFCC Tayi Awon Gaba Da Birigediya Jafaaru Isah
      • Buhari Bai Kyautawa Yan Najeriya Ba - Inji TUC
      • Kotun Ta Yaken Wa Abdul Inyass Hukuncin Kisa
      • Indan Wani Abu Yasami Buhari, Sai Mu Durkusar Da K...
      • Kungiyar Maharba Na Neman Izinin Karawa Da Boko Haram
      • An Haifi Tagwaye Manne Da Juna A Jihar Bauchi
      • Real Madrid Ta Kori Benitez Ta Nada Zidane
      • Saudiyya ta kori ma'aikatan jakadancin Iran
      • Photos:Ministan Sufuri Rotimi Amaechi Ya Ziyarci P...
      • Gwamnatin Bauchi Ta Raba Wa Matasa Wayoyin Hannu D...
      • Video: Arsenal 1 Newcastle 0
      • Video: Crystal Palace 0 Chelsea 3
      • Shin Ana Wa Musulmai Adalci Kuwa A Jihar Taraba?
      • Photos: Hotuna Daga Wajen Bikin Auren Yar Sarkin K...
      • An Zatar Da Hukuncin Kisa Wa Malamai Shi'a A Saudi
      • Al'ummar Nijeriya Suna Dandana Kudarsu A Karkashin...
      • AKwai Masu Yunkurin Kashe Buhari – Rev Mbaka
      • Abubuwan Mamaki Da Suka Bayyana A Lokacin Haihuwar...
      • Buhari Na Shirin Hana Sanatoci Da 'Yan Majalisu Sa...
      • Tafsir: Gudummawar Matasa A Musulinci By Sheikh Dr...
      • Tafsir: Suwaye Masoyan Annabi By Sheikh Ahmad Tijj...
      • Ku Sake Mun Mijin Ko Ku Rufe Mu Tare - Matar Samb...
      • Ina Sane Da Wahalhalun Da Kuke Sha, Sakon Buhari G...
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger