1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Fadakarwa » Falalar Azumin Shura

Falalar Azumin Shura

By Abdul Mk
Add Comment
Saturday, 24 October 2015

Wannan cikakkrn bayani ne daga ZAUREN FIQHU dangane da Azumin Tasu'ah da Ashurah.
Hakika ranar ashura, rana ce wacce babu irinta acikin ranakun shekara baki daya. Domin kuwa rana ce wacce manyan Muhimman al'amura na tarihi suka faru acikinta.
Rana ce wacce addinin Musulunci ya sunnanta yin azuminta domin koyi da Manzon Allah (saww). Kamar yadda zamu gani acikin hadisai Sahihai masu zuwa in sha Allahu.
Daga Abu Hurairah (ra) yace "An tambayi Manzon Allah (saww) "Shi. wacce Sallah ce tafi falala bayan Sallolin farillah?". Sai yace ".YIN SALLAH CIKIN TSAKAR DARE".
Sai aka ce "Wanne Azumi ne yafi falala bayan na Ramadhan?" Sai yace: "WATAN NAN NA ALLAH WANDA KUKE KIRANSA ALMUHARRAM".
(Muslim da Ahmad da Abu Dawud ne suka ruwaitoshi).
Kunga wannan hadisin ya nuna mana cewa falalar wannan azumin da akeyi acikin Almuharram wato Ashura da Tasu'ah kenan sun zarce falalar yin azumi awani watan in banda Ramadhan.
Daga Sayyiduna Mu'awiyah bn Abi Sufyan (ra) yace "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa: "HAKIKA WANNAN ITA CE RANAR ASHURA. DUK DA CEWA BA'A FARLANTA MUKU YIN AZUMINTA BA, NI DAI INA AZUMI. WANDA YAGA DAMA YAYI AZUMI. WANDA KUMA YAGA DAMA YACI ABINCI".
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Wannan hadisin yana karantar damu cewa hakika ba'a wajabta mana yin azumin Ashura ba. Sai dai Sunnah ce. Wanda yake da iko yayi. Wanda kuma bai yi ba, to bashi da laifi. Sai dai ya kuskure samun wannan falalar. Domin kuwa akwai Sahihin hadisin da Manzon Allah (saww) yace : "AZUMIN ASHURA YANA KANKARE ZUNUBAN SHEKARA GUDA".
Wasu mutanen saboda son rai da kuma jahilci suna riya cewar wai an Kirkiro yin azumin Ashura ne domin Qiyayyar Imamul Husaini (rta) alhali kuma ba haka abin yake ba. Domin kuwa an fara yin azumin Ashura tun kafin haihuwar Imamul Husaini din (rta).
Ga hadisi nan daga Nana A'isha (rta) tana cewa: "Ranar Ashura ta zamanto wata rana ce wacce Quraishawa suka kasance suna azumtarta tun alokacin Jahiliyyah.
Kuma Manzon Allah (saww) ya kasance yana azumtarsa. Kuma Sannan bayan yayi hijirah zuwa Madina ma ya azumceshi kuma ya umurci mutane su azumceshi.
Amma yayin da aka Wajabta na Ramadhan sai yace "DUK WANDA YAGA DAMA YA AZUMCESHI (WATO ASHURA) WANDA KUMA YAGA DAMA YA BARSHI".
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).
4. Daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) yace : "Manzon Allah (saww) yazo Madeena sai ya tarar da Yahudawa suna azumtar ranar Ashurah.
Da ya tambayesu "MENENE WANNAN?". Sai suka ce "Rana ce mai nagarta wacce Allah ya tseratar da Annabi Musa (as) da Banu Isra'eela daga Makiyinsu (wato Fir'auna). Don haka Annabi Musa (as) yake azumtarta".
Sai Manzon Allah (saww) yace : "NI NA FIKU CHANCHANTA DA ANNABI MUSA". Don haka ya azumceshi kuma yayi umurni da Azumtarsa".
(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Wannan hadisin yana karantar damu abubuwa masu yawa.
*Na farko : halaccin yin wata ibadah ta musamman awasu ranaku na musamman domin nuna murna ko farin ciki akan wani abu na Musamman wanda ya ta'ba faruwa a irin wannan ranar.
2. Na biyu : Soyayyar da Manzon Allah (saww) yake yiwa sauran 'Yan uwansa Annabawa (as).
3. NA UKU : Musulunci ya kan karbi wasu abubuwan daga addinan da suka gabata, Sannan ya gyarashi ya kyautatashi yadda zai yardar da Allah (SWT).
Acikin wani hadisin kuma daga Abu Musal Ash'Ariy (rta) yace : "Ranar Ashura ta zamanto rana ce wacce Yahudawa suke girmamata sun riketa amatsayin Eidi. Don haka Sai Manzon Allah (saww) yace "TO KU AZUMCETA"
(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Acikin wannan ruwayar kamar ya nuna cewa ana yin azumin ne don sa'ba ma Yahudawa. Tunda su suna yin Biki ne aranar, shi yasa musulmai kuma suke Azumi domin mu kauce ma koyi dasu.
Acikin wani hadisin kuma Abdullahi 'dan Abbas (ra) yace "Yayin da Manzon Allah (saww) ya azumci Ashura kuma yayi umurni a azumceshi, Sai (Sahabbai) suka ce "Ai wannan fa rana ce wacce Yahudawa da Nasaara suke girmamata".
Sai Manzon Allah (saww) yace "IDAN SHEKARA MAI TAZO, IN ALLAH YASO ZAMU AZUMCI RANAR TASU'AH MA".
Amma shekara bata zagayo ba sai da M anzon Allah (saww) ya koma zuwa ga Allah.
(Muslim da Abu Dawud ne suka ruwaitoshi).
Acikin wata ruwayar daga Imam Ahmad bn Hanbal, Manzon Allah (saww) cewa yayi : "WALLAHI IDAN HAR NA WANZU ZUWA BA'DI, SAI NA AZUMCI RANAR TARA GA WATA MA".
(Imam Ahmad da Muslim suka ruwaito).
Sayyid Saabiq (Allah yaji Qansa) ya fada acikin littafinsa FIQHUS SUNNAH cewa Malamai sun ce Hakika shi Azumin Ashura martabobi uku ne.
- Martabar farko : Shine mutum ya azumci ranar Tara ga wata, goma ga wata, da kuma Sha-daya ga watan Almuharram.
- Martaba ta biyu : Shine mutum ya azumci ranar tara da kuma goma ga Wata (tasu'a da ashura kenan).
- Martaba ta Uku : Shine mutum ya azumci ranar Goma ga wata kadai (wato Ashurah kenan).
FA'IDAH : Ya halatta mutum yayi azumi ranar Juma'a ko Asabar ko lahadi mutukar dai ranar tazo daidai da ranar wani azumi mai falala. Kamar Ashurah, Tasu'ah, Azumin ranar Arfah, Azumi Uku akowanne wata, etc.
Dukkan Malamai sunyi ittifaki akan halascin yin haka.
FALALAR YALWATA MA IYALI ARANAR ASHURA :
Akwai hadisi daga Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace "Manzon Allah (saww) yace : "DUK WANDA YA YALWATA MA KANSA DA IYALANSA ARANAR ASHURA, ALLAH ZAI YALWATA MASA ACIKIN GABA DAYAN SHEKARAR NAN".
Baihaqiy ya ruwaito hadisin acikin SHU'ABUL EEMAN. Hakanan Ibnu Abdil-Barri ma ya ruwaito.
Hadisin yana da wasu hanyoyin masu yawa wanda aka ruwaitoshi. Sai dai dukkaninsu raunana ne.
Amma Imamus Sakhawiy yace Hanyoyin hadisin suna karfafar Junansu saboda yawaitarsu. Don haka za'a iya yin aiki dashi.
Wannan yalwatawar ta hada da sauyin abinci, abin sha, da sauransu.
Ana so duk wanda yake da iko ya kyautata ma iyalansa awannan ranar ta Ashura.
Mun gabatar da wannan karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP - (2) Kuma ina bama daliban zauren hakurin cewa na gabatar da karatun ne cikin dare sakamakon rashin samun damar yin hakan da rana saboda yawaitar Uzurarruka.

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 05:32
In Fadakarwa
Falalar Azumin  Shura Title : Falalar Azumin Shura
Description : Wannan cikakkrn bayani ne daga ZAUREN FIQHU dangane da Azumin Tasu'ah da Ashurah. Hakika ranar ashura, rana ce wacce babu irinta acikin...
Rating : 5
Related Posts: Fadakarwa

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Falalar Azumin Shura "

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ▼  October (389)
      • Sunayen Ma'aikata Kwastam Wadanda Aka Musu Retaya
      • [Video] Download Highlight Chelsea 1 Liverpool 3
      • [Video] Download Highlight Crystal Palace 0 Manche...
      • Wani Jirgi Ta Fadi, Ta Kashe Mutane 200 A Misira
      • Yadda zaki hada beef fritters.
      • [Video] Download Highlight Swansea 0 Arsenal 3
      • [Video] Download Highlight Real Madrid 3 La Pasma 1
      • Dan jaridar Freedom na fuskantar barazana
      • An Kashe 'Yan Al-shabab Hamsin
      • Najeriya za ta kara da Brazil a gasar cin kofin du...
      • Kotu ta dakatar da Sarki Sanusi II rushewa ko sauy...
      • Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 23 Super Eagles
      • Nafisat Abdullahi ta maida martani ga Adam Zango d...
      • Klopp ya ce Mourinho mutumin 'kirki ne'
      • Wa'adin rijistar BVN a Nigeria ya cika
      • Kwastam ta yi wa jami'anta 34 ritaya
      • Gwamnonin APC na so a cire tallafin man fetur
      • Yadda ake alalan shinkafa.
      • Samuel Eto’o ya taimaka da dala 75,000 wurin yakan...
      • Buhari Na Magana Kan Tattauna Da Yan Boko Haram
      • An rufe makarantar da ake zargin yi wa yara fyade ...
      • [Tafsir] Download Tafsir Wacece Mace Musulma By Sh...
      • Photos: Nafisah Abdullahi Tare Da Kcee
      • Jam'iyyar APC Ta Gode Ma Buhari, Majalisa
      • Bamu Amince Da Dambazau Ba - Kungiya
      • 'Zargin yi wa yara maza fyade a Kano'
      • A Karshe An Amince Da Rotimi Amaechi Da Saura Muta...
      • [Photos] Shin Nafisah Abdullahi Ya Dace Ta Koyar D...
      • Yadda ake yin cus-cus da miyar koda.
      • [New Music] Download Never Take Drugs by Dking ft IMJ
      • Kazamar Gida Part 1
      • [Nishadi] Ma Aikaciya NTA Tana Kwaliya Kafin Tafar...
      • [Photos] Yanda Yan Boko Haram Suke Hada Makamai Su
      • Walcott Da Chamberlain Baza Su Buga Wasa Uku
      • [Photos] El-Rufai Ya Isa Bauchi A Private Jet
      • Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 a Diffa
      • Ouattara ya yi tazarce a Cote d'Ivoire
      • India za ta bai wa Afirka tallafin $600m
      • Labarin Wani Aljanni Musulmi
      • [Photos] Sojin Najeriya Sunyi Mamaye Sambisa, Sun ...
      • [Photos] Manya Yan Boko Haram Guda 100 Wanda Ake Nima
      • [Photos] Buhari with His Former Classmates
      • An sanar da cire ciroman Kano Sanusi tare da nada ...
      • [Photos] Buhari Ya Gana Da Manya Yan Kasuwa A Indiya
      • [Photos] Adam A Zango Ya Kara Aure Aboye
      • Giwa FC ta doke Wikki Tourists da ci 3-2
      • Yanda Ake Hada Kosan Semovita
      • [Graphic Photo] Ta Kona Mijinta Da Ruwan Zafi Dan ...
      • [Photos] Buhari Da yan Najeriya A Indiya
      • “Yaki Da Boko Haram Ba Aikin Gwamnati Ba Ne Kadai”
      • Matasa Sun Koka Da Rashin Tafiya Da Su A Gwamnatin...
      • Masallatai Sun Karfafa Matakan Tsaro a Adamawa
      • Amurka Ta Aika da Sakon Ta'aziya ga Jihohin Borno ...
      • Mutane bakwai na takarar shugabancin Fifa
      • Ana taron tallafa wa 'yan hijira a Nigeria
      • Biritaniya na horar da sojojin Nigeria
      • Ouattara ya sake lashe zaben Ivory Coast
      • Boko Haram: Sojin Nigeria sun ceto mutane 338
      • [Photos] Buhari Ya Isa Indiya
      • An tuhumi Mourinho da halin rashin da'a
      • An fitar da Arsenal daga Capital One Cup
      • An soke zaben 'yan majalisar dokokin Ribas
      • Majalisa ta tantance karin ministoci biyar
      • An kafa sabuwar runduna a Benisheikh
      • Faransa za ta jagoranci taron tattauna rikicin Syria
      • Yoyon fitsari na karuwa a Nigeria
      • Yanda Ake Yin Binciken Kafin Aure
      • An cafke ‘Yan Boko Haram 45 a Lagos
      • Najeriya ta tsallake zuwa gasar Afrika a Rwanda
      • Ta yi wa kishiyarta dukan kawo wuka
      • Yanda Ake Hada Shinkafa Da Kwakwa
      • Shugaban Karuwai Najeriya Jessica Elvis Ta Mutu
      • Falana Zaya Kai Buhari Kotu
      • Buhari Zaya Halarci Wani Taro A Indiya
      • Bosho ya gaji Ibro a fim din "Zalimu"
      • Girgizar kasa a Afghanistan
      • NCC ta ci tarar MTN naira tiriliyan daya
      • [Photos] Wani Kauyen Igbo Da Aka Gina Amurka
      • [Video] Download Highlight Barcelona 3 Eibar 1 201...
      • Yanda Ake Hada Kunun Shinkafa
      • [Video] Download Highlight Manchester United 0 Man...
      • Aston Villa ta sallami Tim Sherwood
      • Yan Boko Haram sun kama garin Kerewa na arewacin K...
      • Rasha ta amince ta hada hannu da Amurka domin yaka...
      • Ana gudanar da zaben shugaban kasa a Tanzania
      • Wani Tsohon Da Shekara 60 Yayi wa Jikarsa Ciki
      • Halin da na samu kaina tare da ’yan Boko Haram a S...
      • Wani Magidanci Ya Kashe mahaifiyarsa
      • Maganin Ciwon Sanyi Na Maza
      • [Graphic Photos] ISIS Sun Kashe Wani Ta Hayan Taka...
      • Ana Mastala Mai A Najeriya
      • Nyesom Wike Zai Daukaka Kara
      • [Photos] Jackie Appiah Ta Saya Sabon Mota
      • [Graphic Photos] An Kashe Shugaban Al-Qaeda Na Syria
      • Mayweather Ya nuna Duka Bel Din Dayaci A shekara 19
      • [Photos] Osinbajo da El-Rufai Tare Da Yan Najeriy...
      • Yanda Ake Hada Fura
      • Yanda Ake Hada Yoghurt
      • [Download] Download Highlight Arsenal 2 Everton 1
      • Mutane 5 Sun Mutu A Harin Maiduguri - NEMA
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger