1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kazamar Gida Part 1

Kazamar Gida Part 1

By Abdul Mk
Add Comment
Thursday, 29 October 2015

afar yana tsaye a tsakar gidansa bayan ya fito daga wanka ya kulle bandakin da mukulli wanda ya maidashi wajen shigarsa shi d'aya domin hatta matar gidan bai barinta ta shiga.
Gidan yake k'arewa kallo, rike yake da k'ugunsa. Alokacin bai wuce goma na safe ba amma har lokacin matar gidan bata da niyyar motsawa daga shimfida tun bayan daya matsa mata tayi sallar asuba ta koma gadon bata k'ara juyi ba ballantana takai ga tashi. Ya kai kallonsa ga tukunya wacce ke cike da sauran abinci tun na shekaranjiya,gasauran kayan wanke wanke nan da ta bada wankinsu ga almajiri har ruwa ya dakesu sunyi k'ura bata kwashesu ba. Cikin bakin ciki yakai dubansa inda ta tula uban shara har ya cika dustbin yana zuba,ga wani danko danko da k'asan gidan yayi wanda ke tabbatar da ba a wankeshi sai iyakar abunda ruwan sama ya wanke.
Ya girgiza kansa kawai ya ja kafarsa zuwa falon. Ko yunkurin cire takalminsa baiyi ba hakanan ya taka kafet din ya nufi dakinsa. Sai alokacin ya iya sauke numfashi mai dad'i,wani k'arni falon yakeyi wanda shiyasa sam bai kaunar matarsa tayi girki da kifi duk kuwa sanda tayi toh zaman falon ya gagareshi kenan. Daman ya take a kazanta ballantana ace tayi aikin kifi. Ranar babu zaman falon.
Gaba daya Jafar bashi da inda zai zauna yaji sanyi a gidansa daya wuce dakinsa. Duk da dakuna hud'u ne a gidan da katon falo guda daya sannan bandaki har uku ne amma kazancewarsu bazai bari ko kusa mutum mai tsafta yayi marmarin shigarsu ba. Dakinsa da kanshi yake gyarawa ya sanya turaren tsinke,wani lokacin idan yaga lokacin kasuwa zai kure sai ya gyara gadonsa ya kulle ya tafi da mukullin idan ya dawo yayi sharar tunda yasan koda yabar mukullin bazata gyara ba saima ta shige dakinsa ta kwanta ta k'ara hargitsa gadon a cewarta duk gidan babu inda tafison kwanciya sai dakin nasa.
Saida ya gama shirinsa tsaf ya sanya takalmansa sannan yayi duba ga matarsa dake sharar bacci babu abunda ya dameta. Cikin bakin ciki ya daki cinyarta da karfi,a firgice ta farka tana susa,kallon rain in wayo ta hau yi mishi. Shima harararta yakeyi
"Tashi ki koma dakinki zan fita na makara."
Ta ja tsaki tana wani marairaice murya irin ta masu bacci
"Haba jafar(sunansa take kira kai tsaye),meye hakane? Ka dauki alhakina wallahi."
Bai iya cewa komai ba,kayan daya cire ya shiga linkesu ya ajiye a saman akwatinsa. Ta mike tsaye tana gyara zaman zanin da tasha aikin girki dashi na dare har lokacin shine a jikinta.
"Ai na tuna,gwara daka tasheni. Ashe yau suna muke dashi a hotoro. Anti amina ai kasan ta haihu ko?"
Jafar dai gadonsa ya gyara tsaf ya jera filo. Jin da tayi baice komai bane ta kara matsowa tana goge miyan bacci
"Wai jafar bakaji bane?"
Sai lokacin ya dago ya dubeta,gaba daya tasha jinin jikinta ganin yanda ya hade rai tamkar wanda aka aikomasa da sakon mutuwa.
"SIYAMA!!!"
Ya kira sunanta a fusace. Ta turo baki don tasan sauran zancen,fadan nan dai data tsana zaiyi. Ba tare data amsa ba ta kauda kanta gefe.
"Siyama ke wace irin jinsi ce? Anya zan yarda ke din mutum ce kamar sauran mutane? Na soma tsorata ni Jafar kodai aljana na kawo gidana! Bakisan abunda ya dace ba siyama, na soma yarda kanki ba daya bane! Banda haka! Na tashi ko gaisuwar arziki ban samu awajenki ba! Ke baki iya ki tashi ki taimakamin da ko abin karin kumallo ba bayan kina sane cewa ba zama zanyi gidan ba zan fita neman kudi ne. Kin kwanta tamkar mai baccin mutuwa sai bacci kike shararawa! Yanzu kuma daga tashinki don son ki kara tabbatarwa da mutum ke cikakkiyar mara tunani ce shine har kike da bakin tambayata fita unguwa! Toh wallahi muddin kika sa kafarki kika fita daga gidan nan sai na sab'a maki Siyama! Saikin raina kanki wallahi. Sannan wallahi na dawo na sami gidan nan yana wannan tashin karnin sai kinsan namiji kike aure ba wanda ya rako maza ba. Ga shara can zan turo maki almajiri ki hadamishi ya zubar ya wanke dustbin da parker din. Fita ki bani waje zan rufe dakina."
Siyama ta riga ta gama kaiwa bango,a fusace ta fita tana mai buga kofar da karfi. Har iska tana kad'o labulen dak e jikin windon d'akin. Jafar ya girgiza kansa bakin ciki goma da ashirin suka tarar masa. Ko shekara basu rufa ba da aure amma matsaloli sunfi adadin kwanakin dake cikin shekara guda yawa. Ya dauki wayoyi da mukullin mashin dinsa ya fito. Gam ya rufe dakinsa da mukulli ya jefa a aljihu ya fito. Tamkar zaiyi amai yakeji dakyar ya shiga dakin nata.
Tana zaune ta hade rai,wayarta a hannu da alama kira takeson yi. Ya bi dakin da kallo ya yamutse fuska,daki duk tarkacen kaya babu inda mutum zai zauna yaji sanyi. Bai damu da kallon da take watso mishi ba ya jefo mata dari biyar
"Gashi sai dare zan shigo kada kisa girkin rana dani."
Da sauri ya fice domin ya gaji da jin warin dake busowa ta bandakinta wanda ke a wangale.
Ya ja mashin dinsa waje ya rufe mata kofa.
Ihun kukan bakin ciki siyama ta sanya,banda Allah Ya isa ba abunda take jerowa Jafar. A ganinta ai ya cuceta ace matar yayanta guda ta haihu,haihuwar ma na fari amma yace babu inda zataje.
Batayi wata wata ba ta lalubi lambar yayarta rumaisa ta danna mata kira.
Ringing biyu,ana uku ta amsa.
"Hello siyama ya dai? Kin fito?"
Siyama ta ciji lebbanta,hawayen bakin ciki suka k'aru
"Ina fa! Jafar ya cuceni anti rumaisa,yace babu inda zanje."
Rumaisa ta runtuma ashariya
"Amma jafar dan kaza kaza ne! Banda ya rainawa mutane hankali yaushe akayi auren naku sannan duka duka fitarki nawa ne da har zaice kin fiye yawo bazakije ba? Yanaso ya soma raba zumunci tun ba'aje ko'ina ba? Wallahi bai isa ba,rabu dashi bari na yiwa Hajiya magana."
Siyama ta tare ta da sauri
"A'a don Allah anti rumaisa ki rabu dashi kawai. Na amince bazan fita ba tunda yace zai dauki mataki muddin na yarda na fito bada izninsa ba."
Rumaisa taja tsaki
"Banza uwar son miji,sai kiyita zama kin kare a haka jafar yana juyaki. Ki buga ki bawa aminar hakuri,amma tabbas ya dace ki tashi tsaye ki kwaci y'ancinki don wannan ba yi bane!"
Daga haka rumaisa ta yanke kiran. Siyama ta sharb'i kukanta har bataji sadda almajiri yayi ta kwada sallama ba. Saida ta nutsu sannan taji. A fusace ta fito idanuwanta cike taf da bala'i
"Wai lafiya ka ishi mutane da sallama? Menene?"
Yaron yace
"A'a maigidan ne yace nazo wai zan kwashe shara."
Ta harareshi taja tsaki,shi dai yaro duk ya firgita kada ta kai mishi duka. Ta nuna inda dustbin din yake
"Ai gashican,kaje kayi ta kwasa."
Daga haka tayi dakinta ta rufe kofar ta soma kiciniyar yin wanka saboda tsamin jikinta ya soma isarta. Idan bata mance ba rabonta da wanka tun safiyar jiya da Jafar ya matsa da bukatarsa,dolenta kuwa tayi wankan da babu niyya ba don haka ba yanda a kwana biyun nan takejin sanyin gari bazatayi ba. Ita kam tak'i jinin wanka da ruwan sanyi kamar yanda take jin kasalar d'ora ruwan zafi a risho.
Jafar kuwa tunda ya zauna a shago cikin kasuwa ya kasa maida hankali sosai kan sana arsa. Tunaninsa kacokam yana ga wannan muguwar halayya ta Siyama wanda yake neman hanyar kawo karshenta. Toh kodai 'yar aiki zai nema mata ne? Saidai kuma ta yaya? Domin tun farko saida ya nemi hakan a wajenta ta hayayyako masa,wai ita sam bata son 'yan aiki nan da nan sai su kwace maka miji su barka baki hangame. Karshe tace tafison almajiri ya barta duk da dai hakan bai kwanta masa ba sai don su zauna lafiya. Duk da d'abi'un Siyama,yana sonta matuk'a. Y'ar uwarsa ce kuma matarsa,ta yaya zai k'i d'iyar kanin mahaifinsa? Bayason kai k'ararta kada ayi mishi kallon marar hakuri ace ko shekara bata rufa ba ya soma k'orafi.
"Jafar wai yau lafiya kake?"
Ya dago kansa ya dubi abokin aikinsa,Ibrahim. Murmushin yak'e yayi
"Lafiya,kaina ke d'an ciwo."
"Allah Ya sauwake toh."
Ya amsa da amin. Ya tuno a matsalarsa har da yunwa,dole ya mik'e ya shiga cikin kasuwa don ziyartar Ladi mai abinci. Yana son cin abincinta,gata dai k'aramar yarinyar da bata fi shekaru goma sha shida ba amma akwai tsafta hakanan abincinta zakaci shi lafiya lau. Sam,bata da hayaniya irin ta sauran masu siyar da abinci.
Tare sukeyin aikin dahuwar da mamanta,saidai kwana biyu Maman babu lafiyar jiki,ladi keyi.
Har nauyi yakeji ace da m atarsa amma yana cin abinci a waje duk saboda rashin tsaftar muhalli da rashin gyara tukunya. Ladi har ta sanshi sosai saboda babu ranar da baya zuwa shagonsu cin abinci.
Tunda ya shiga shagon ta hangoshi. Ta sakar masa murmushi adaidai lokacin da take ajiye kwano taf da abinci agaban teburin wasu. Ya maida mata martanin murmushin kafin ya maida hankali kan wayarsa.
"Assalamu alaika. Barka da zuwa yayana. An iso lafiya? Ya antina?"
Wani sanyi ya kwanta luf a zuciyarsa,abunda ya gaza samu kenan a gidansa. A rayuwar Jafar yanason a bashi girma muddin ya zamana ya girmewa mutum koda da mintoci ne. Shiyasa Ladi take burgeshi,murmushi ya k'ara sakar mata alokacin da yake amsa sallamarta.
"Wa alaikissalam 'yar nijar. Lafiya lau nake,ya jikin mama?"
Ladi wacce har lokacin murmushi bai kaura daga kan fuskarta ba ta bashi amsa
"Mama ai ta samu sauki sosai,mungode Allah. Watakila ma gobe ka ganta tazo. Ai tana yawan tambayarka kasan bata mance manyan customers d'inta."
Yayi 'yar dariyar yak'e saboda kunyar da yaji,kenan dai har an sanyashi layin manyan customers? Hum! Siyama ta cuceshi. Ladi ta katse mishi tunani
"Bari na hado maka abincin."
Tayi gaba ba tare data jira abunda zai umarci a kawomasa ba. Toh menene bata sani ba tunda ba yau ne ya soma zuwa shagonsu ba?
Minti biyu sai gatanan da saurinta,hannunta dauke da kwanukan abinci ta ajiye agaban teburinsa. Lafiyayyen tuwo ne da miyar danyar kub'ewa yaji nama da ganda sai daddad'an kamshi ke tashi. Kallo d'aya ya yiwa abincin babu wata wata ya soma ci bayan ya wanke hannu da ruwan data ajiye.
Yana ci yana tunanin inama ace haka Siyamarsa ta iya dahuwa,inama tana da tsafta koda rabin ta Ladi ce.
Yunwar daya kwaso ne ya mantar dashi inda yake, hakan yasa bai dago ya kalli kowa ba har saida ya kammala cin abinsa. Rabonsa da abinci tun jiya da rana dayazo shagon Ladi ya narki shinkafa da miya mai d'an karen dadi. Koda ya koma gidan da dare,bai iya cin abincin Siyama ba saboda k'arnin kifi dake tashi.
Ladi kuwa tana wanke kwanuka saidai rabin hankalinta yana ga Jafar. Tana tausaya masa sosai. Bata mantawa a baya kafin Jafar yayi aure,ya kasance mutum ne mai yawan wasa da dariya. Sukanzo harda abokan kasuwancinsa su ci abinci a shagon har ma su jima suna hirarsu kafin su tattara su koma cikin kasuwa. Saidai fa ba sa ido ba,ta fahimci Jafar na baya dana yanzu sun bambanta matuk'ar gaske. Wannan Jafar din ya rame,bashi da wasan nan,dariyarsa bata tsawo. Idan yazo daga gaisuwa ba abunda ke shiga tsakaninsu. A zaton Ladi,aure ai yakan chanja rayuwar mutum daga bakin ciki zuwa farin ciki saidai auren Jafar ba haka yake ba.
Bata da hujjar cewa ba auren soyayya yayi da anti siyama ba,don ita shaida ce akan yanda yake zuzuta siyama a gabansu. Har suyita dariya ita da mama. Hatta hotunan siyama ya tab'a nuna mata don har gajiya tayi ta mik'a masa wayar ganin sunk'i k'arewa.
Duk da bata shiga hurumin da bai shafeta ba,saidai yau kam taci d'amarar tambayar Jafar matsalarsa. Haka kawai tana jinsa tamkar wani yayanta musamman daya kasance bata da wani d'an uwa babba ko k'arami. Ita kadai ce wajen mamanta. Don haka ta kife kwanukan a kwando,ta gyara zaman hijabinta ta nufi inda Jafar ke zaune yana kora ruwan lemo a cikinsa...
Xaki debo ruwan dafa kanki...

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 18:53
In Hausa Novels
Title : Kazamar Gida Part 1
Description : afar yana tsaye a tsakar gidansa bayan ya fito daga wanka ya kulle bandakin da mukulli wanda ya maidashi wajen shigarsa shi d'aya domin ...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kazamar Gida Part 1"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ▼  October (389)
      • Sunayen Ma'aikata Kwastam Wadanda Aka Musu Retaya
      • [Video] Download Highlight Chelsea 1 Liverpool 3
      • [Video] Download Highlight Crystal Palace 0 Manche...
      • Wani Jirgi Ta Fadi, Ta Kashe Mutane 200 A Misira
      • Yadda zaki hada beef fritters.
      • [Video] Download Highlight Swansea 0 Arsenal 3
      • [Video] Download Highlight Real Madrid 3 La Pasma 1
      • Dan jaridar Freedom na fuskantar barazana
      • An Kashe 'Yan Al-shabab Hamsin
      • Najeriya za ta kara da Brazil a gasar cin kofin du...
      • Kotu ta dakatar da Sarki Sanusi II rushewa ko sauy...
      • Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 23 Super Eagles
      • Nafisat Abdullahi ta maida martani ga Adam Zango d...
      • Klopp ya ce Mourinho mutumin 'kirki ne'
      • Wa'adin rijistar BVN a Nigeria ya cika
      • Kwastam ta yi wa jami'anta 34 ritaya
      • Gwamnonin APC na so a cire tallafin man fetur
      • Yadda ake alalan shinkafa.
      • Samuel Eto’o ya taimaka da dala 75,000 wurin yakan...
      • Buhari Na Magana Kan Tattauna Da Yan Boko Haram
      • An rufe makarantar da ake zargin yi wa yara fyade ...
      • [Tafsir] Download Tafsir Wacece Mace Musulma By Sh...
      • Photos: Nafisah Abdullahi Tare Da Kcee
      • Jam'iyyar APC Ta Gode Ma Buhari, Majalisa
      • Bamu Amince Da Dambazau Ba - Kungiya
      • 'Zargin yi wa yara maza fyade a Kano'
      • A Karshe An Amince Da Rotimi Amaechi Da Saura Muta...
      • [Photos] Shin Nafisah Abdullahi Ya Dace Ta Koyar D...
      • Yadda ake yin cus-cus da miyar koda.
      • [New Music] Download Never Take Drugs by Dking ft IMJ
      • Kazamar Gida Part 1
      • [Nishadi] Ma Aikaciya NTA Tana Kwaliya Kafin Tafar...
      • [Photos] Yanda Yan Boko Haram Suke Hada Makamai Su
      • Walcott Da Chamberlain Baza Su Buga Wasa Uku
      • [Photos] El-Rufai Ya Isa Bauchi A Private Jet
      • Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 a Diffa
      • Ouattara ya yi tazarce a Cote d'Ivoire
      • India za ta bai wa Afirka tallafin $600m
      • Labarin Wani Aljanni Musulmi
      • [Photos] Sojin Najeriya Sunyi Mamaye Sambisa, Sun ...
      • [Photos] Manya Yan Boko Haram Guda 100 Wanda Ake Nima
      • [Photos] Buhari with His Former Classmates
      • An sanar da cire ciroman Kano Sanusi tare da nada ...
      • [Photos] Buhari Ya Gana Da Manya Yan Kasuwa A Indiya
      • [Photos] Adam A Zango Ya Kara Aure Aboye
      • Giwa FC ta doke Wikki Tourists da ci 3-2
      • Yanda Ake Hada Kosan Semovita
      • [Graphic Photo] Ta Kona Mijinta Da Ruwan Zafi Dan ...
      • [Photos] Buhari Da yan Najeriya A Indiya
      • “Yaki Da Boko Haram Ba Aikin Gwamnati Ba Ne Kadai”
      • Matasa Sun Koka Da Rashin Tafiya Da Su A Gwamnatin...
      • Masallatai Sun Karfafa Matakan Tsaro a Adamawa
      • Amurka Ta Aika da Sakon Ta'aziya ga Jihohin Borno ...
      • Mutane bakwai na takarar shugabancin Fifa
      • Ana taron tallafa wa 'yan hijira a Nigeria
      • Biritaniya na horar da sojojin Nigeria
      • Ouattara ya sake lashe zaben Ivory Coast
      • Boko Haram: Sojin Nigeria sun ceto mutane 338
      • [Photos] Buhari Ya Isa Indiya
      • An tuhumi Mourinho da halin rashin da'a
      • An fitar da Arsenal daga Capital One Cup
      • An soke zaben 'yan majalisar dokokin Ribas
      • Majalisa ta tantance karin ministoci biyar
      • An kafa sabuwar runduna a Benisheikh
      • Faransa za ta jagoranci taron tattauna rikicin Syria
      • Yoyon fitsari na karuwa a Nigeria
      • Yanda Ake Yin Binciken Kafin Aure
      • An cafke ‘Yan Boko Haram 45 a Lagos
      • Najeriya ta tsallake zuwa gasar Afrika a Rwanda
      • Ta yi wa kishiyarta dukan kawo wuka
      • Yanda Ake Hada Shinkafa Da Kwakwa
      • Shugaban Karuwai Najeriya Jessica Elvis Ta Mutu
      • Falana Zaya Kai Buhari Kotu
      • Buhari Zaya Halarci Wani Taro A Indiya
      • Bosho ya gaji Ibro a fim din "Zalimu"
      • Girgizar kasa a Afghanistan
      • NCC ta ci tarar MTN naira tiriliyan daya
      • [Photos] Wani Kauyen Igbo Da Aka Gina Amurka
      • [Video] Download Highlight Barcelona 3 Eibar 1 201...
      • Yanda Ake Hada Kunun Shinkafa
      • [Video] Download Highlight Manchester United 0 Man...
      • Aston Villa ta sallami Tim Sherwood
      • Yan Boko Haram sun kama garin Kerewa na arewacin K...
      • Rasha ta amince ta hada hannu da Amurka domin yaka...
      • Ana gudanar da zaben shugaban kasa a Tanzania
      • Wani Tsohon Da Shekara 60 Yayi wa Jikarsa Ciki
      • Halin da na samu kaina tare da ’yan Boko Haram a S...
      • Wani Magidanci Ya Kashe mahaifiyarsa
      • Maganin Ciwon Sanyi Na Maza
      • [Graphic Photos] ISIS Sun Kashe Wani Ta Hayan Taka...
      • Ana Mastala Mai A Najeriya
      • Nyesom Wike Zai Daukaka Kara
      • [Photos] Jackie Appiah Ta Saya Sabon Mota
      • [Graphic Photos] An Kashe Shugaban Al-Qaeda Na Syria
      • Mayweather Ya nuna Duka Bel Din Dayaci A shekara 19
      • [Photos] Osinbajo da El-Rufai Tare Da Yan Najeriy...
      • Yanda Ake Hada Fura
      • Yanda Ake Hada Yoghurt
      • [Download] Download Highlight Arsenal 2 Everton 1
      • Mutane 5 Sun Mutu A Harin Maiduguri - NEMA
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Sadiya Gombe Ft Al'ameen Bauchi (Ra'ayin Ki Ne Nawa) Sabuwar Waka
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Zanga-zanga A Bauchi-Gwamnatin Ta Saka Dokar Hana Fita Da Zirga-Zirga Ac...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger