1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Article » SOYAYYA TA SANYATA SAUYA ADDINI Part 1

SOYAYYA TA SANYATA SAUYA ADDINI Part 1

By Abdul Mk
Add Comment
Wednesday, 15 April 2015

Wasu 'yan mata ne a can kasar Rasha wani mutum ya yaudaresu ya dauke su ya tafi da su wata kasar larabawa da sunan zai sama musu aiki. Ashe wannan mutumin ba haka ne ke zuciyarsa ba, karuwanci yake son ya sa su.

Lokacin da suka isa wannan kasa, sai mutumin nan ya kwace passport din su. Daga nan sai ya sanar dasu karuwanci ne abin da ya kawo su yi. Duk 'yan matan nan suka yarda saboda babu yadda suka iya sai wata guda daya daga cikinsu ta ki.

Ita wannan baiwar Allah ta taso ne a wani gida na 'yan gani-kashenin Kiristanci. Haka nan suka zauna da wannan mutum kullum tana rokonsa ya bata passport din ta ta koma gida don ita ba za ta iya karuwanci ba, amma ya ki ya bata.

Wata rana mutumin nan ya fita daga gidan da ya kama musu, sai ta shiga dakinsa ta yi ta yin bincike har sai da ta gano wajen da ya ajiyen wannan passport din nasu. Ta sa hanu ta dauko nata, sai ta fita daga wannan gida.

Da ta fito kan hanya, sai ta hango wasu mutane guda uku suna tafowa wajen da take. Da isowarsu sai ta fara musu magana da yarenta na Rashanci su kuma ba sa ji. Daga nan sai ta yi magana da Turanci, Khalid ne da mamansa da kanwarsa. Khalid sai ya amsa mata.

Ta kwashe labarinta ta fada musu, daga nan sai ta roke su don ta zauna a gidansu na kwana uku don tuntubar gidansu da kuma yadda za a yi ta koma gida. Suka tafi da ita gida, ta yi ta kokarin buga waya gidansu a can Rasha amma abu ya gagara.

Yanzu dai ta fara zama 'yar gida. Khalid kan zo su zauna su yi zance. A duk lokacin da aka dauko zancen addini sai ta nuna ba ta so. Da Khalid ya ga haka sai ya canza dabara, sai ya je wata cibiyar yada addinin musulunci yake karbo mata littattafa tana karantawa. Daga nan sai ta fara sauyawa, ta saki jikinta suna tattauna addini.

Ba a sami lokaci mai tsawo ba sai ta yanke shawarar shiga addinin musulunci. Bayan ta musulunta sai suka kara shakuwa da Khalid har soyayyarsu ta yi armashi sosai. Aka daura musu Aure.

Wata rana sun shiga kasuwa don yin sayayya kawai sai ta ga wata mata da hijabi da nikabi ba a ganin ko ina a jikinta. Sai ta tambaye yaya wannan mata ta yi irin wannan shigar. Khalid sai ya ce da ita ai irin shigar da ake son musulma ta yi. Daga nan kawai sai ta ce ai sai su tafi shagon sayar da kaya ita ma ta sayi irin wadannan. Yayi kokarin fahimtar da ita ba dole sai ta yi irin wannan shiga ba amma ta ki. Suka je ta saya kuma ta sanya su nan take.

Wata rana tana duba passort din ta sai ta ga wa'adinsa ya yi kusan karewa. Saboda haka yanzu dai tafiya ta kama ta komawa Rasha don ta sabinta passport din.

Suka shirya suka nufi filin jirgi sama. Bayan sun shiga jirgi an tashi sai wasu mutane suna ta yi musu dariya suna Rashanci da ita. Ya tambayeta me ke faruwa? Sai ta ce masa isgili suke mata. Haka nan dai ake ta yi har suka isa Rasha.

Da sukarsu tsammani yake za ta kai su gidansu amma sai ta ce su tafi Hotel. Suka kama daki suka huta. Kashe gari sai suka nufi ofis din katin shaidar tafiye-tafiye. Da suka je wajen da za a sauya mata sabo, sai suka nemi ta kawo hoton da za a sa a sabon passport din. Sai ta basu 'black and white'. Sai suka ce mata mai kala suke so kuma wanda gashinta ya fito. Taki yarda, haka nan suka yi ta shiga ofis zuwa ofis har suka je ofis din babba a wannan gari. Shi ma ya sanar da ita ba zai iya mata ba in ba abin da suka fada ta kawo musu ba. Amma kuma sai ya ce mata za ta iya tafiya hedikwatarsu a can babban birnin Moscow ko zata dace. Suka koma Hotel.

Kashe gari sai suka nufi babban birnin Moscow. Da suka je nan ma haka suka yi ta yawo ofis-ofis ba nasara Khalid kuma na kokarin shawo kanta ta yarda da dokarsu amma ta ki.

Daga nan sai aka tura su ofis din oga kwata-kwata na kasar. Da suka je tayi masa bayani ya ce ina hoton ta bashi, ta yaya zan tabbatar ke ce a wannan hoto? Sai ta ce ya kira daya daga cikin sakatarorinsa mace za su je ta nuna mata fuskarta sai yaki yarda. Khalid ya tambayeta me ke faruwa ne tun da Rashanci suka yi shi kuma ba ya ji. Ta sanar da shi abin da ke faruwa. Sai ya ce: Haba masoyiyata, ki yi hakuri mana ki yi duk abin da suka ce, taki yarda. Daga nan sai 'Passport Master General' ya koresu daga ofis din.

Bayan da suka koma Hotel suka ci abinci sai Khalid ya hau gado ya kwanta zai yi barci saboda gajiya. Sai ta tashe shi ta ce ai barci bai kama su ba. Suka fara sallar dare har ya gaij ya kwanta ya bar ta tana sallah. Duk lokacin da ya farka tsakar dare, ko dai ya ganta tana ruku'i, ko kuma sujuda. Da asuba ta yi sai ta tashe shi suka yi sallah. Ta dan yi barci kadan har gari ya waye ta farka suka yi wanka suka shirya, sai ta ce su kuma ofis din nan. Khalid ya ce me kuma za mu je mu yi bayan abin da ya faru jiya. Haka na dai ta rinjayesu suka koma. Da isarsu kawai sai suka ji ana kwalla musu kira sai aka bata passport din ta Sabo, Allahu Akbar! Ta juya ta kalle shi sai ta ce da shi: Duk wanda ya ji tsoron Allah, to zai sanya masa mafita cikin lamarinsa.

Suka koma garinsu suka nufi gidan iyayenta. Kash!

Bayan da suka kwankwasa kofa sai wani daga cikin yayunta ya bude kofar ta bude fuskarta, yayi farin ciki da ganinta amma kuma ga alama yana cike da mamakin shigar da ya ganta a ciki. Khalid ya zauna a falo su kuma suka shige can cikin gida.

Khalid na nan zaune falo shi kadai sai ya fara jin ana kace-nace, sai hayaniya, sai ya ji ana ta rudani yana zaune shi dai bai motsa ba. Da aka dan jima kadan sai ya ga wasu samari majiya karfi su hudu sun tafo wajensa, tsammani yake maraba suka zo yi masa, kawai sai ya ji sun fara bugunsa. Suka bashi kashi da kyar ya samu ya nemi kofar fita ya arce. Haka nan dai ya samu ya kutsa cikin mutane ya bace musu. Daga nan sai ya koma hotel ya shige dakinsu ya shiga bandaki ya duba jikinsa a madubi ya ga duk sun faffasa masa jiki ya samu ya wanke.

Khalid ya kwana wannan dare dai cikin tsoro don kuwa tsammani yake za a zo kashe shi. Yana ta tunani cikin zuciyarsa, wannan kasar da ba a dauki rai a komai ba, mutum na iya kisa a kan dala goma. Haka nan dai ya kwana cikin firgici da tsoro da tunanin ita kuma me ke faruwa da ita. Idan har shi namiji zai iya shanyewa naushi da mari, to ita kuma yaya kenan, haka nan ya kwana cikin zulumi. Anya kuwa ba za ta koma kiristanci ba?

Kashe-gari yayi safako ya je kusa da gidan yadda ba za a ganshi ba ya tsaya yana ganin me ke faruwa a kofar gidan. Can bayan wani lokaci sai ya ga wasu mutane uku sun fito daga gidan da alama wajen aiki za su tafi. Ya ci gaba da lura da gidan har suka dawo daga wajen aiki suka shiga. Sai da yayi kwana hudu yana haka. Rana ta hudun bayan fitarsu sai ya ga matarsa ta fito tana leken hagu da dama, ya matsa kusa da ita, yaga kayanta a yayyage, jikinta a farfashe jini yana zuba, an daure hannuwanta da kafafuwanta sarka, ya fashe da kuka. Ta dube shi ta ce: Khalid kar ka ji komai, zan rike alkawari ba zan canza addinina ba, Wallahi abin da ke faruwa da ni ba komai ba ne in an kwatanta da abin da ya faru da sahabbai da tabi'ai da ma annabawan Allah! Ka koma hotel ka zauna ka rabu da ni da iyayena kar ka shiga matsalarmu ta cikin gida zan zo in sameka.

Khalid ya koma hotel har dare yayi gari ya waye yana tsammanin zuwanta amma ba ta zo ba, kashe-gari ma haka sai can tsakar dare ya ji ana buga masa kofar daki. Ya tsorata, yana zancen zuci, kila ma sun sako ta a gaba ta zo ta nuna musu dakin za su kashe shi. Can dai sai Khalid yayi ta maza ya ce: Waye? Kawai sai ya ji sassanyar muryar matarsa: Ni ce ka bude min kofa, ya bude kofa ta shigo sai ta fara tattara kayayyakinsu ta zuba cikin jaka, ta sanya hijabinta da nikabi, ta ce maza-maza yai sauri su tafi. Suka shiga taxi sai ya ce a kai su airport ita kuma sai ta ce 'a'a, a kai su wani gari ta ambaci sunan garin. Daga wannan garin ma suka sake tafiya wani garin babba mai 'Intl airport'.

Bayan sun kama dakin hotel sun shiga sai ta cire kayanta. Khalid ya ce babu wani waje a jikin da babu rauni an yi mata jina-jina, gashin kan ta ma an tsige wani.

Daga nan sai ta fara bashi labarin abin da ya faru. Lokacin da suka shi ga gida da aka tambayeta waye shi ta fada musu yanzu ta mus lunta kuma shi ne mijinta. Daga nan sai suka ce sam basu yarda ba sai ta koma kiristanci, aka daureta da sarka sai shi kuma aka zo aka fara bugunsa har ya gudu. Dukan safe daban na yammaci ma daban, amma ta ki yarda. Idan sun tafi wajen aiki ana barinta tare da kanwarta wacce an bar mata makulin da za ta kunce ta taje bandaki sauran kuma yana wajen babban yayansu.

Haka nan dai suke zama har ta fara shawo kan kanwarta ta fada mata abin da ake nufi da musulunci, a bauta wa Allah shi kadai, sai kanwar ta ce nima ya dace na bi wannan addin don kuwa shi ne addinin gaskiya. Kanwar ma ta karbi musulunci, Allahu Akbar! Daga nan ne take hawa kan katanga har ta ke ganowa Khalid lokacin da yake zuwa gidan har ta fito suka yi magana.

Ranar da za ta gudu sai kanwarta ta dafa musu giya mai karfi sosai suka sha suka yi tatil, suka bugu sosai, bayan sun fita cikin hankalinsu sai ta sa hanu ta dauko makullin a aljihun yayansu ta since yayar ta gudu. Kafin ta bar kanwar ta ce mata kar ta nuna musu ta musulunta ta boye har su san yadda ita ma za su kubutar da ita.

Bayan ta gama bashi labari, gari ya waye suka nufi filin jirgi, da saukarsu a kasarsu Khalid ya wuce da ita Asibiti.

Karshen labarin kenan. Allah sa mu amfana.

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 06:39
In Hausa Article
Title : SOYAYYA TA SANYATA SAUYA ADDINI Part 1
Description : Wasu 'yan mata ne a can kasar Rasha wani mutum ya yaudaresu ya dauke su ya tafi da su wata kasar larabawa da sunan zai sama musu aiki. A...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Article

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "SOYAYYA TA SANYATA SAUYA ADDINI Part 1"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ►  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ▼  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ▼  April (187)
      • AWOYIN DA YAKAMATA ANA SAMU NAYIN BACCI
      • **Tunatarwa Guda 5 Ga Musulmi* *
      • Remain In PDP, We Don’t Need You-APC to WIKE
      • 64 Senators Endorse Bukola Saraki For Senate Presi...
      • Change Buhari promised will not happen overnight –...
      • MAI KIWON SHANU DA KARENSA
      • ME ZA'AYI YAU MAI GIDA? ''YACE KUNU''
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 6
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 5
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 4
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 3
      • DOMIN KE DA MIJINKI Part 2
      • DOMIN KEDA MIJINKI Part 1
      • KO KASAN KAKAN MUTU A RANA SAU (5) WANI LOKACIN?
      • INA MASU SAURIN KAWOWA A LOKACIN JIMA'I ???
      • Why Our Prayers Are Not Accepted
      • *** WAYYO NI NURUL AYN 003 ***
      • *** WAYYO NI NURUL AYN 002***
      • *** WAYYO NI NURUL AYN 001 ***
      • Fitsaranci Alokacin Bikin Aure
      • Jinnul Ashiq - Aljanin Soyayya
      • Daga Cikin Abubuwan Mamaki Wadanda Na Gani Akan Sh...
      • Mafi Qazantar Sihiri
      • I’m ready for probe, says FCT minister
      • I did not ask anyone to bar AIT from covering my a...
      • Chibok girls found? Nigerian troops find 200 girls...
      • DAUKEWAR RUWAN NONO
      • HANYOYIN RABUWA DA MASTURBATION
      • MATSALAR DA YA SHIGA SAKAMAKON SA'BA MA ALLAH TA H...
      • MAGANIN SHAFAR ALJANU DAGA ZAUREN FIQHU
      • GA WANI ALBISHIR
      • WANI LABARI MAI GIRGIZA ZUCIYA!
      • HALACCIN ZIYARTAR QABARI
      • MAGANIN QARIN KUZARIN NAMIJI.
      • MATSALAR KANKANCEWAR ALKALAMI
      • ABINCIN ZUCIYA
      • MATSALAR KANKANCEWAR ALKALAMI
      • QARIN BAYANI AKAN ALJANUN GADO
      • GORON JUMA'AH
      • FALALAR ALQUR'ANI
      • KU SAURARA KUJI
      • HUKUNCIN ALWALAR WANDA YA KALLI TSARAICI
      • YANA CIKIN BABBAR MATSALA
      • BA WAI MUTUWA CE ABIN TSORO BA.
      • YAWUN BAKIN MA'AIKINA (SAWW)
      • ALAMOMIN MASU TSORON ALLAH
      • HAMZA THE LION OF ALLAH
      • HALIMATUS SA'ADIYYAH (RA)
      • ALIYYU BN ABI TALIB (RTA)
      • Buhari bars AIT from covering his activities
      • 21 killed by Boko Haram in Yobe today
      • 21 killed by Boko Haram in Yobe today
      • FIQHU ASAUKAKE - DAGA ZAUREN FIQHU (DARASI NA 9).
      • This is daylight robbery.. Aisha Alhassan
      • Gen Buhari signifies interest to probe alleged mis...
      • Fulani Gunmen Kill 30 In Benue, Nasarawa
      • Okorocha, Ikpeazu win •PDP leads in Taraba
      • Bomb blast reported in Plateau
      • Marte Town Capture by 2000 Boko Haram Members
      • Boko Haram chase Nigerian troops from Sambisa
      • EFCC set to declare Ali Modu Sherrif a Wanted Man
      • GMB and GEJ Meet in Abuja today
      • GORON JUMA'AH
      • FALALAR ALQUR'ANI
      • Jonathan orders removal of campaign posters nation...
      • HUKUNCIN ALWALAR WANDA YA KALLI TSARAICI
      • WACECE MACE TAGARI? WAYE MIJI NAGARI?
      • Dalilin Da Yasa Matasa Suke Aure Yanzu
      • MATANSA SUN GALLABESHI
      • YADDA AKE TUBA DAGA LAIFIN ZUWA WAJEN BOKA
      • Rahma Sadau and Friend released new Pictures
      • Photos: Emir of Kano pays Gen. Buhari congratulato...
      • Gunmen kill El-Rufai’s campaign coordinator
      • Fire guts popular ​Kano shop
      • HUKUNCIN WANDA YA FIDDA MANIYYI DA AZUMI
      • MAGANIN SANYI NA YARA
      • DUNIYA TA RIGA TA AUREKA :
      • DAGA CIKIN ILLOLIN ZINA
      • IDAN AJALIN MUMINI YAYI
      • LABARIN ANNABI ISA (AS) DA WANI MUTUM MAI KWADAYIN...
      • KU DUBA WANNAN GIRMA
      • ALIYYU BN ABI TALIB (RTA)
      • Eight injured in failed suicide bomb attack in Pot...
      • LUQMAN AL-HAKEEM
      • LABARIN ANNABI ISA (AS) DA WANI MUTUM MAI KWADAYIN...
      • PDP’s sins will soon start coming out,’ President-...
      • Soldier, lawyer die in Bauchi roach crash
      • Jonathan demands N2tn Election funds return
      • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
      • MAZINACIYA MAI MUMMUNAN TARIHI
      • Boko Haram Slits The Throats Of 12 People In Gwoza...
      • SOYAYYA TA SANYATA SAUYA ADDINI Part 2
      • MATA 10 WAINDA ALLAH YATSINE MUSU
      • Kuskure Guda 50 Alokacin Bawa Yaro Tarbiyya
      • Makircin Iblees
      • APC rejects May 28 handover date
      • DUTSE YA SACE KAYAN ANNABI MUSA
      • YANA TAMBAYA AKAN ZAITUL LAWZ
      • MAI TSARKIN ASALI (SAWW).
      • Rahma Sadau released hot new Pictures
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Sadiya Gombe Ft Al'ameen Bauchi (Ra'ayin Ki Ne Nawa) Sabuwar Waka
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Fantyz Guy ft Mr SPYZY - ALKALERI GARINA (Official Hausa HipHop Music Video...
        Bauchi Base Popular HipHop musician FANTYZ GUY release hit track ALKALERI GARIN Featuring Mr SPYZY 

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger